Page 62

47 6 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 62 💦💦

   Hotel ta kama sannan ta fara shirye-shiryen komawa gida,nan da jibi take son ta koma. Tana kwance a d'akin da ta kama ta d'au wayarta ta shiga kiran Mommy,bata b'oye mata komai ba harta zuwa gurin Michael da tayi da irin labarin da ta jiyo har zuwa kama d'akin da tayi,daga qarshe ta qara mata da cewa jibi tana nan dawowa. Babu yadda Mommy ta iya sai haquri tunda koma miye ya faru a yau tanada LAIFI itama.

    2days after,
Qarfe shabiyi yayi ma Suhana a Nigeria dan morning flight tabi,wajen qarfe d'aya kuwa ta isa gida da d'an jakar kayanta qarama kasancewar duk kayayyakin ta na Uganda dan basu barta ta fita da ko d'aya ba sai na jikinta kawai. Sun sha kukan su itada Mommy har sun gaji,saidai kukan nasu ba abinda zai qare su dashi.

    Suhana na zaune a palour ta had'a uban tagumi in banda tunani babu abinda takeyi. Mommy ce ta fito daga d'akin su a hanzarce,"Suhana!",amma shiru dan Suhana bata ma san inda take ba balle tasan ana mata magana. Qarasowa Mommy tayi ta d'an bugeta "keh Suhana",sai a lokacin tasan da Mommy na wajen.

   Cikin hanzari Mommy tace "kizo mu kai Daddyn ki asibiti jikin shi ya tashi,yanzu kije d'aki ki zauna a jikin shi inyaso ni kuma saina fita na nema mana koda me adaidaita ne",wani irin juyowa Suhana tayi ta kalli Mommy kafin tace "me adaidaita fa naji kince?",Mommy tace "eh mana,to Suhana in bamu nema ba munada mota ne?". Suhana tace "au yanzu daman ko motar hawa guda d'aya babu a gidan? To garage d'in can miye amfanin shi?".

    Mommy tace "haba Suhana,ina muka ga ta ajiye mota a gida bayan irin wahalan da muka sha a jinyar Daddyn ki,kina gani fa gidan da muke ciki ma saida muka saida,ga qaddarorin shi dama nawa da muka saida still jikin babu dad'i",Suhana ta tab'e baki kafin tace "je ki nemo amma taxi ba adaidaita sahunnan ba". Mommy tace "shikenan" sannan ta fita neman d'an taxi a waje.

      Nan Suhana ta nufi d'in inda ta taradda jikin Daddynta babu dad'i,sannu ta shiga yi mishi kafin Mommy ta dawo da me taxi har cikin gidan. Fito da Daddy sukayi suka sa shi a motar sannan suma suka shiga suka tafi. Suna isa kuwa aka karb'e shi sai emergency, allura sukayi mishi sannan ya d'an samu yayi bacci dan lokacin da suka kawo shi buge-buge yake tayi.

    An caje su kud'i kam ba na wasa ba dan a cewar Likitan aikin dashen qodar da akayi mishi bai zauna daidai ba so dole a daidaita mishi inba haka ba yana gama gocewa daga gurbinshi zai iya rasa ranshi,gashi aikin na gaggawa neh. Haka suka harhad'a kan kud'aden da suke dashi kama daga kan na Mommy wanda Suhana tayi ta turo mata harna Suhanan ita kanta. A yanzu basu da ajiyan kud'i daya wuce dubu d'ari,shima kuma dole zasu ringa saya mishi magunguna akai akai.

    A ranan da yamma akayi mishi aikin dan na gaggawa neh. Bayan aikin sai aka kaishi wani d'aki inda zai huta shi kad'ai dan ba a son ayi disturbing d'inshi daga nan zuwa gobe da safe aga yadda Allah zaiyi abin shi. Koda jin hakan sai su Mommy suka koma gida dan ko sun zauna ba shiga za'a barsu suyi ba,iyakaci Likitocin dake kula dashi neh suke leqawa time to time.

     www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now