Page 53

47 10 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 53 💦💦

    Bayan sun gama wayar sai Mommy ta tashi,kitchen ta nufa inda tayi ma Daddy kudun gyad'a. A baki ta bashi ya sha kafin ta kwantar dashi,itama shan kunun tayi kafin nan ta nemi guri ta d'an kwanta. A daren kuwa taji shigowar alert,tana dubawa taga million biyu neh suka shigo da text d'in Suhana kamar haka:

     "Hi Mom,ga wannan ki lallab'a kafin ku isa Germany d'in,insha Allahu zan tura miki koda three millions neh yanzun bana so na dame shi da yawa amma nasan shida kanshi ma zai ringa bani kud'in. Take care of yourself and my Dad for me,bye". Mumushi Mommy tayi bayan ta karanta text d'in,a ranta take tunanin sauqi yazo musu indai Suhana na tare da Farhan. A fili kuma tace "Allah ya yi miki albarka 'yata,shiyasa akace da haifar gwamna gwara haifan matar gwamna",tayi murmushi kawai.

    Washegari ta fara shirye-shiryen zuwan su Germany d'in,visa taje ta nema musu akan da sauran shirye-shiryen,sannan nan da kwana uku ne zasu tafi. Haka taita hidimar har zuwa randa zasu tafi,da wuri suka shirya suka sai Germany.

    Sunyi sa'ar samun Likitan kuwa dan a ranan yana duba mutane,kasancewar ba kullum yake duba mutanen ba. Yayi iya ka bakin qoqarin shi akan Daddy,satin su biyu suka koma gida. Kamar yadda Suhana tayi alqawari tayi sending ma Mommy three millions na jinyar Daddy. Ba laifi ya d'an samu sauqi,dan har magana yana d'an iyawa yanzu sab'anin kwanaki da baya iya cewa komai.

★★★
   Farhan na zaune kan three seater dake palourn Suhana,ita kuma tana kwance kanta na kan cinyar shi yana d'an wasa da gashin kanta. Kallon wani American film sukeyi wanda da gani suna jin dad'in shi. Hankalin su kwance kamar basu ba,Suhana ce ta d'ago kanta ta kalle shi kafin ta kira sunan shi "Farhan",ba tareda ya amsa ba ya sauqar da idon shi kan nata yana kallo.

   Nan taci gaba "I think we should go and check how my Dad is feeling now right?". Farhan yace "sure! I think that's a good suggestion,so when do you think we should go?". Suhana tace "maybe in two to three days time,is it ok for you?". Yace "yeah". Tace "thank you then",yace "anytime my wife",tareda manna mata kiss a goshi. Kallon su suka cigaba dayi hankali kwance.

     Suhana taji dad'in hakan dan akwai abinda Mommy ke son ta bata ne shiyasa take son zuwan nasu bawai dan duba jikin Daddy bane,tunda tasan yanayin jikin nashi yanzu. Da yamma bayan ya fita ta koma d'akinta inda ta fara shirin tafiya dan zuwa jibi take son su je.

    Da daddare bayan ya dawo kuwa fita sukayi inda sukayi dinner d'insu a wake,kafin su dawo kuwa saida sukayi sayayya na abubuwan ci. Straight side d'in shi suka nufa suna dawowa,film d'in da suke kallo d'azun nan shi suka koma suka cigaba da kalla bayan sunyi wanka.

   
     Washegari ya sama musu ticket na tafiyar dan ta fad'a mishi cewa gobe take son suje su gidan. Bayan ya dawo kuwa da yamma suka fita shopping inda suka yo siyayya me yawan gaske,wasu na Mommy neh,wasu kuma da Daddy. Sannan Suhana ta siya wa qawa d'aya tilo a wajenta kayayyaki wato Suby.

     Bayan sun kammala da shopping d'in wani wajen gyaran jiki da gashi ya kaita,saida ya jira akayi mata sannan suka koma gida. Tun qarfe 8 suka kwanta bacci duk da flight d'in nasu na rana neh bana safe ba dan sai 12 noon zasu tashi.

    
     www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now