Page 48

59 7 4
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 48 💦💦

    Dukan uku-uku qirjin Mommy ya fara,tama rasa da wanda zata ji. Da rashin lafiyar Daddy ne ko kuma da abinda ke shirin faruwa da Suhana? Jikin ta a sanyaye tace "ina shi Farhan d'in yanzu?" Suhana tace "tunda ya gama duka na ya fice,ban san inda yaje ba". Mommy tace "barni dashi,na san maganin shi,ke dai abinda zaki daure kiyi shine in kinada d'an kud'i a hannunki ki turo min ni nasan yadda zan bima lamarin".

   Cikin rashin fahimtar abinda Mommy ke nufi Suhana tace "ban gane ba Mommy",Mommy tace "kina da kud'i ko baki dasu?". Suhana tace "akwai", Mommy tace "an wuce gurin! Ki turo min kawai". Ita dai Suhana har yanzu bata fahimci abinda Mommy ke nufi ba,me zatayi da kud'i.


   "Shikenan zan turo amma baki fad'a min abinda yake faruwan ba". Suhana ceh ta tambayi Mommy,Nan Mommyn ta zayyana mata halinda suke ciki. Daga farko Suhana na tunanin kashe auren ta dan ta dawo gida amma yanzu ta shirya ma duk wani wulaqancin da zata fuskanta daga gurin Farhan in dai ba zai sake ta ba.

   Bayan sun gama wayan Suhana ta tura ma Mommy 100k dan account d'inta baya rabuwa da kud'i dama,koda yaushe cikin sa mata Farhan yake. Tayi mamaki qwarai da jin halinda su Mommy ke ciki,sannan ta d'au niyyar bama Farhan haquri in ya dawo dan she can't be without him a yanzun nan.

   Bacci b'aro ne ya sace ta tana zaman jiran dawowar Farhan. Ba ita ta tashi ba sai can tsakar dare dan karfe biyu saura neh lokacin. Gyara jikin ta tayi ta sanya attractive night wears d'inta da tasan na d'aukan hankalin Farhan duk sanda ya ganta a cikin su. Ta bi duk jikin ta ta feshe da turare kafin ta fito ta nufi side d'in shi.


    Daga farko knocking ta shiga yi amma jin shiru yasa ta bud'e qofar a hankali sannan ta shiga. Gani tayi babu Farhan babu alamar shi,toilet ta leqa ko ya tashi ya shiga ne,nan ma taga baya nan. Babu inda bata shiga ba a ranan amma ina babu ko alamun Farhan a gidan. That means a waje zai kwana kenan.


   Da qyar ta iya yin bacci bayan tayi ta trying line d'in shi ya qi shiga. Washegari da safe ta kira Mommy ta sanar mata duk abinda ya faru tana yi tana kuka. Mommy tace ta share hawayem tasan abinda zata yi,ita dai ta zauna kawai ta jira ganin abinda zai faru dan da qafar shi zai dawo kuma yazo ya nemi gafarar ta.

   Ita dai Suhana abin ya bata mamaki,ta rasa gane abinda Mommy ke shirin yi. Ita dai koma miye indai zai shawo mata kan Farhan d'inta shikenan bata da matsalar komai. Jin yadda Mommy ta tabbatar mata da cewa Farhan zai dawo gareta ya saka ta farin ciki matuqa.

★*★*★
    Bayan gama wayar su da Suhana Mommy ta shirya ta fice ta bar gidan. Abin da zai bama karatu mamaki shine bata tsaya ko ina ba sai wajen boka bayan ta ciro 30k daga account d'inta a cikin wanda Suhana ta turo mata. Kafin ma tayi mishi bayanin abinda ke tafe da ita bokan nan ya shiga qirgo mata.


   "Nasan dukkanin abinda ke tafe dake,ba so kike mijin 'yar ki ya koma gareta ba? Sannan kina so ku more shi", Mommy tace "tabbas abinda ke tafe dani kenan,kuma ina buqatar aikin cikin gaggawa dan muna cikin wani irin hali a yanzu. Bokan yace "kada ki damu,ai kin kawo inda za a share miki hawaye neh indai kin zo da idon garin wato kud'i".



    www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now