page 46

57 11 5
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*This page is devoted in special honour to Oumyasmin,tnks for following my write-ups. This indeed is something to be appreciated, tnks alot dear,keep following, voting and share if possible and yes I like commenting...*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 46 💦💦

    Dukan ta ya shiga yi kamar Allah neh ya aiko shi,tun cikin tana tsiwa har ta dawo tana bada haquri,daga qarshe haqurin ma kasa bayarwa tayi. Sai da ya gaji kafin ya rabu da ita. Kuka Suhana ta shiga yi ba qaqqautawa,jikin ta duk ciwo yake yi mata dan ta bugu sosai. A tarihin rayuwar ta bata tab'a shan duka kamar na yau ba,hasalima bai fi ta qirga dukan da akayi mata ba dan dalilin duka nema ya sanya bata zuwa islamiya tun da d'inta.

  
      Tayi kukan har ta gode ma Allah,daga qarshe tashi tayi ta koma sashen ta dan Farhan kanma fita yayi ya bar gidan. Wanka taje tayi da ruwan zafi ta d'an gasa jikin ta dai,sa'annan ta fito ta shafa mai ta sanya kaya mara nauyi a jikinta sai ta kwanta.

   Harta kwanta sai wayan ta ta fad'o mata a rai,nan ta miqe ta fara dubawa. Can kuma ta tuno da ta barta a palour ranan da aka kaita asibiti. D'auko wayar ta tayi a palourn sannan ta dawo d'akin ta kwanta. Tunani iri-iri ta shiga yi aranta,tana ta tunanin wanda zata kira ta kaima kukanta. Can dai ta yanke shawarar kiran Mommyn ta..

★★
    Tun bayan bikin Suhana da sati biyu Daddy ya fara fama da rashin lafiya. Na yau daban na gobe daban,koda suka je asibiti anyi gwaje-gwaje daban-daban amma ba a gano komai ba. Wannan abu ba qaramin damun Mommy yake yi ba dan a rayuwa batada farin cikin daya wuce 'yarta da Daddy,ta shiga cikin damuwa matuqa dan har rama ta d'an fara.

   

    Sau da dama tana so ta sanar da Suhana kan lamarin amma bata son hankalin ta ya tashi shiyasa tayi shiru. Ba qaramin kud'i suke kashewa ba a jinyar shin nan gashi jiki yaqi yin dad'i,bama wannan ne yafi d'aga ma Mummy hankali ba illa kasa gano taqamamman abinda yake damun shi da akayi.


    D'an savings d'insu duk ya tafi gashi ita bata aiki,shi kuma abokan kasuwancin nashi kowa sai gudu yake yi kada asara ta hau shi tunda ya jima a kwance. Abin ya kaima har an fara saida qaddarori da suke dasu saboda lafiyar shi. Ganin abin yaqi ci yaqi cinyewa yasa Mommy ta kawo shawarar zuwa India ko Allah zaisa suyi dace.


    Hakan akayi kuwa,tareda wani qaninshi suka je. Nan ma babu yadda basuyi ba dan gano abinda ke damun shi ba amma ina,sun kasa gano komai,qarshe sai suka tura su United Kingdom inda aka had'a su da wani babba kuma qwararren Likita ya duba shi.

   Bayan yayi iya dube-duben shi sai aka gano yanada blood cancer da kuma kidney cancer wanda a halin yanzu ta cinye kidney d'in,ya zamo dole a cire a canza mishi wasu inba haka ba kuma yana dab da mutuwa neh. Ba qaramin shiga tashin hankali Mommy tayi da al'amarin ba.


   Babban damuwanta shine inda zasu samu kud'in da za ayi mishi wannan aikin,qarshe suka yanke shawarar saida gidan su da suke ciki tareda had'a sauran kud'ad'an da suka rage musu. Sannan sai su koma wani gidan hayan da Daddyn yake dashi yasa 'yan haya. Da qyar suka had'a kan kud'ad'an nan aka samu aka yi mishi aikin....



        www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now