page 47

55 10 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 47 💦💦

    Bayan sati biyu aka sallamo su da magungunan da zai ringa sha. Yayi baqi ya rame,haka ma Mommy duk ta dishe. Wani d'an qaramin gida suka koma wanda befi rabin gidan su nada ba,d'akuna biyu ne a gidan sai kowanne da toilet a ciki,sai palour d'an qarami a tsakiya sai kitchen. Filin tsakar gidan kuwa d'an mitsitsi dan kana fitowa daga palourn sai gate.

   Kwanaki suna ta ja amma shiru babu wani improvement gameda jikin Daddy gashi ba kud'i suke da shi ba,na aminci ma yanzu kam da qyar suke samu. Daga qarshe dai Mommy ta yanke shawarar fad'a ma Suhana halinda suke ciki ko zasu samu wani abin daga hannun mijin ta. Sai dai tun jiya take kiranta amma shiru bata amsa ba kuma bata sake kiranta ba,zuba ma sarautar Allah ido kawai tayi.


    Mommy na zaune a jikin Daddy damuwar duniya ta gama isarta,ta wani yi uban tagumi ta tsumduma cikin duniyar tunani. Ringing d'in wayarta neh ya maido ta cikin hankalin ta,da ganin me kiran wayan kuwa tayi sauri ta amsa tare da fad'in "hello,'yata!",cikin shauqi da keyan jin muryar Suhana tayi maganar.


  Ita kuma Suhana jin muryar Mommyn yasa ta fashewa da kuka,hakan kuwa yayi matuqar tada ma Mommy hankali dan bata zaci hakan daga gareta ba. Da qyar Mommy ta saita kanta kafin ta shiga rarrashin ta tareda tambayar abinda yasa ta kuka. Suhana tayi-tayi ta daina kukan amma ta kasa,qarshe kashe wayar tayi ta cigaba da yin kukan.

   Hankalin Mommy ya qara tashi gashi Daddy bai ma san inda kanshi yake ba ballentana yayi consoling d'inta,idon shi biyu amma babu uhm babu uhmuhm. Yana dai nan ne kawai,duk ya bi ya qwanjame a gurin gashi babu kud'in magani. 'Yan uwan shima da zasu taimaka musu kowa cewa yake yi baida shi,abin dai ba'a cewa komai. Ita ma Mommyn nata 'yan uwan qin taimaka musu suka yi,a cewar su ta rabu dashi kawai tunda wahala take sha ita kuma tace bazata iya ba,hakan yasa duk suka fita daga harqarta.


     Babu irin tunanin da Mommy ba tayi ba,tayi tunanin ko an sanar da Suhana halin da suka koma ne? Allah ne dai yasan dalilin kukan nan nata. Hankalin Mommy ya kasa kwantawa dan haka ta shiga kiran Suhana a waya. Ringing na farko ta amsa sannan ta Mommyn ta shiga rarrashin ta,daga qarshe tace ta fad'a mata abinda yasa ta kuka. Suhana ta bud'i baki zata yi magana kenan zai kaji matar MTN na fad'in "your account balance is exhausted,please recharge your account to continue your call or dail *606# to borrow airtime,tank you",d'in d'in d'in ya mutu.


     Suhana taji mamakin d'aukewar wayar saboda bata tab'a suna waya da Mommy ko Daddy taji wayar ta katse da sunan qarewar credit ba sai yau,sai dai tayi tunanin ko network ne. Nan ta shiga kiran ta,yana fara ringing ta amsa da "hello,ina jinki Suhana kud'in nawa ne ya qare". Cikeda jin mamaki ta tambaya "kud'in ki ya qare kuma?",Mommy tace "uhmmm,Suhana kenan da ba kamar yanzu bane fa,in dai fad'a min damuwar kin tukunna daga baya kyaji duk abinda me gudana.


   Suhana dai abin ya bata mamaki matuqa,sannan ta matsa taji dalilin da yasa Mommy tace da ba yanzu bane. Nan dai ta shiga koro mata duk abinda ya faru kama daga jiya zuwa har yau,sannan ta qara da cewa Farhan na neman d'ora mata LAIFIN da ba nata ba. Ya cuce ta ya sanya mata cuta kuma yana neman qala mata,da wanne zata ji? Matsalar rashin haihuwa ko ta qanjamau? Allah yasa mu zamanto masu shuka abin arziqi,ameen..



      www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now