page 44

63 7 3
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 44 💦💦

    Likitan neh ya na yi mishi bayani akan lafiyar shi tareda bashi wasu shawarwari akan yadda zai tafiyar da rayuwar shi cikin jin dad'i,in yaci sa'a ma kuma zai iya rabuwa da cutar kwata-kwata. Bayan nan ya rubuta mishi wasu qwayoyi tareda prescribing mishi yadda zai na sha tareda bashi shawarar ya ringa zuwa ana dubashi bayan kowane sati biyu.

   Godiya Farhan yayi mishi tareda bashi kud'in da shi kanshi bai san adadin su ba kafin nan ya fita,magungunan da ya bashi yaje ya saya sannan yayi tambayar inda aka kwantar da Suhana tareda zuwa dan ganin halinda take ciki.

   Idon ta na rufe lokacin da ya bud'e qofan ya shigo,still bata bud'e ido taga wanda ya shigo ba,sai dai a jikinta taji ba nurses d'in da ke dubata bane. Can dai ta bud'e idon nata dan ganin Wanda ya shigo dan taji anqi yin motsi balle magana. Ido biyu sukayi da Farhan wanda fuskar shi ke d'aure babu walwala yana kallonta.

   Tunda take dashi bata tab'a ganin shi a irin wannan yanayin ba,ita a zatonta ma bai iya fushi haka ba. Tsikan jikinta ne taji suna tashi dan ta tabbatar by now kan an fad'a mishi maganar abortion d'inda ta tab'a yi,sai dai har yanzu bata ma san tana d'auke da HIV ba.

    Shi kuma a ranshi ya tausaya mata ganin yadda ta wani yi baqi ta rame wuni d'aya tak. Can dai shiru babu wanda yace qala ma wani sai kallon juna da suke tunda ta bud'e ido sannan kowannen su da abinda yake rayawa a ranshi.

   Farhan ne ya katse shirun da fad'in "how are you feeling now?",tace "am feeling much better. Tana kaiwa nan ya d'aga idonta daga gareshi tana jiran jin abinda zai ce mata,shi kuma tun ganin ta da yayi ya canza mind d'inshi na rabuwa da ita sai dai dole zaman su ya sauya.

   Tana cikin jiran me zai ce sai taji yace "did you need something because the doctor said you'll be resealed by tomorrow, so you're going to spent your night here",ce mishi tayi "I don't need anything, they provides me with all I need,thank you",ta qarasa tareda d'ago kai ta kalle shi.

   Shi kuma kau da kai yayi kafin ya juya yace mata "good night",harya zo bakin qofa zai fita sai yaji ta kira sunan shi "Farhan",bai juyo ba ya amsa mata da "uhum". Tace "I need to talk to you please",yace mata "you shouldn't worry tomorrow is a day,let just call this a day".

   Ba tareda ya barta ta sake uttering wani word ba ya fice. Wani dogon ajiyan zuciya ta sauqe,sai dai ta d'an ji sassauci kad'an ganin yadda ya nuna mata kulawa. A tunanin ta ma wannan na d'an lokaci qalilan neh tunda tasan Farhan na mugun sonta kuma shi ba d'an Nigeria bane balle yace ba zai zauna da ita ba ko ya qaro mata kishiya dan bata haihuwa. Babu laifi ta d'an samu nutsuwa,dan tayi baccin ta mai dad'i ma bayan Likitan yazo ya duba ta.

    Bayan Farhan ya fita wajen Likitan yaje sukayi sallama kafin ya wuce gida. Gabad'aya ya karaya gani yake yi kamar ya kusa mutuwa yanzu haka. Sai dai inya tuno da zantuttukan Likitan na cewa zai iya warkewa gabad'aya saiya d'an ji danyi a ran shi. Da wannan tunanin yake tuqi har ya iso gida. Shi dai ranan bai yi bacci me dad'i ba.

    www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now