Page 61

53 6 1
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 61 💦💦

'Yanuwan su na can Cairo dana nan Uganda suka shiga kira suna sanarda su gameda rasuwar,kowa yaji mutuwar a ranshi ba kad'an ba. Nan suka d'auki gawar akan zasu kaishi gida ayi mishi wanka kafinnan an taru ma. Suna isa Maman ta ba wa me gadi kud'i ya siyo likkafani da dai sauran abubuwan da za'a yi amfani dashi. Shima ba qaramin jin mutuwar yayi ba da aka sanarda shi.

★★★
Suhana na bud'e qofar taci karo da harara gurin Mamansu Farhan,ai tuni taji hanjin cikinta ya kad'a. Shigowa sukayi sannan Maman ta umarce ta da ta fita ta bar mata gidan d'a tunda ta kashe shi ta huta. Haquri Suhana ta shiga bayarwa tana kuka amma fir suka qi,kai qarshe ma korar kare sukayi mata. Ba a jima ba 'yanuwa da sauran mutane suka baibaye gidan,bayan anyi mishi wanka da sallah aka kaishi,sauran kuma ya rage wa masu mishi addu'a.

Koda fitar Suhana bata san taqamammen inda zata je ba,gashi basu barta ta fita da komai ba illa wayarta dake hannunta sai kuma ATM card d'inta,shi d'inma dan na aljihun wanda dake jikinta ne wanda ta sanya after dress a kai. Tafiya kawai takeyi amma bata san inda ta nufa ba,Suhana ta zama abin tausayi gashi ta rame da dishe.

Can wani tunani ya fad'o mata na zuwa gidan Michael, tasan zai taimake ta tunda shiya ja mata koma miye yanzu take ciki. Nan ta shiga wani ATM dake kusa da wajen ta cira kud'i sannan ta nemi me taxi tareda fad'a mishi inda zata je. Ana tafiya tana kallon gefen hanya amma san bata ma san me take kallo ba tsanani hankalinta baya jikin ta. Ta rasa da wanda zata ji,da rasuwar Farhan d'inta neh koda korar wulaqancin da 'yanuwan shi sukayi mata,ko kuma da halinda zata koma gidansu ta tarar.

Bata gama wasiqar jakinta ba taji an tsaya,a ranta tace har an iso. Kud'in shi ta bashi sannan ta fita,knocking na farko aka bud'e mata qofar. Ta dubi me gadin sannan tace dashi tazo wajen me gidan nan neh,me gadin yace mata ai baya nan sunyi tafiya da matarshi wai basu cika zama ba a gidan dama ba 'yan nan bane hutu suke zuwa yi. Suhana ta shiga duhu,ya za ace shida matarshi,dama yanada matane,kuma ma daman ba d'an gari bane,tace kai saidai in wrong information ta samu daga gurin.

Ta dubi mutumin sannan ta tambaye shi "can I please ask you something?",yace "sure!". Tace "when did the owner of this house get married?". Mutumin yace "I think he's married since the past seven years". Hakan ya tabbatar mata da cewa ba Michael yake nufi ba dan a iya saninta bayi da wata mata,idan ma yayi aure to daga baya neh.

Nan ta tambaye shi cewa Michael take nema koya san inda yake,koda jin tambayar sai me gadin ya d'an jirkinta kafin yace mata ai ya rasu,wani fad'uwar gaba Suhana taji. Nan yayi mata bayani kan abinda ya faru,ashe Michael ya kai watanni da mutuwa,bayan mutuwar shinne 'yanuwan shi suka saida ma me gidan a yanzu gidan. Yana gama mata bayani kuwa ya koma ciki ya rufe qofar,ya barta anan da hannu a kai tana kuka.

Shikenan kashinta ya bushe dan yanzu dolenta ta koma gida,wanda take sa ran samun taimakon shi ya riga da ya mutu. Tayi kuka kamar ba gobe,daga qarshe ta shirya komawa gida 9ja...

www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now