Page 72

71 8 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @Hama_gee

Page 72 💦💦

   Bayan Baffa yasha ruwan ne yake sanarda Alhj.Suhan abinda ke tafe shi,yace "wallahi bansan yarinyar nan na d'auke da wata cuta ba,shiyasa ma tun farko na amince maka akan ta",Alhj yace "to indai kuwa hakane fad'uwa tazo dai-dai da zama,baka da masaniya kan cewa cutar da ta kashe matata kenan? Ai ni tun farkon ma da nayi maka maganar yarinyar ba da gaske nayi maka ba saboda nasan ina d'uke da wannan cutar. To amma yanzu kaga na huta,Allah ya hore min mata".

   Ganin Baffa bai fahimci inda maganganun sa suka dosa ba yasa yayi mishi bayani dalla-dalla kan yadda akayi yake da cutar,Baffa yasha mamaki qwarai dan bai tab'a sanin cewar abokin nashi nada wannan cutar ba,saidai koma miye yayi godiya wa Allah tunda ya samu me auren Suhana. Bai bar gidan ba saida suka tsaida magana kan za'a had'a auren dana sauran yaran shi. A take ya bada sadakin Suhana tareda alqawarin nanda kwana biyu za'a kawo kayan auren Suhana dan already Alhj ya shirya ma yin aure,Matar ne da bai samu ba.

    Bayan Baffa ya sanar dashi date d'in da aka tsayar sai ya tafi bayan sunyi sallama,gameda Suhana ta tab'a yin aure kuma daman already Alhj ya sani,so ba wani abin b'oyewa bane. Ba qaramin farin ciki yayi ba,take ya fara sanarda 'yanuwa da abokan arziqi kan yayi mata,kowa murna yake taya shi barinma 'yanuwanshi. Ranan yayi bacci mai dad'in gaske.

    Washegari ya sayi waya tareda registering M.T.N line yasa a ciki da credit na dubu d'aya sannan yaje ma Suhana dashi dan Baffa yace batada waya kasancewar tun zuwanta gidan suka qwace. Koda suka gana da Suhana baiyi mata ba amma babu yadda ta iya hakan ta haqura dashi dan dole,kai kace an canza Suhana neh. Yarinyar da ada duk kud'in ka duk had'uwarka saita kusheka amma yau itace take zantawa da wannan tsofai-tsofai d'in a matsayin mijin da zata aura,duniya kenan.

     Biki sai matsowa yakeyi dan a yanzu sati guda ya rage a d'aura musu aure. Babu irin shirin da uwa keyi wa yaranta wanda Matar Baffa batayi wasu Ummu ba amma koda sau d'aya bata tab'a kwatanta gyara Suhana ba,a cewarta su sabin shiga neh ita kuwa babu abinda bata sani ba gameda aure dan haka bazata b'ata kud'inta da lokacinta wajen yi mata gyara ba. Saidai ko kad'an hakan bai damu Suhana ba kasancewar wanda zata auran ba wai son shi take ba balle tayi tunanin sashi farin ciki,kuma kamar yadda maman ke fad'in ita ba auren fari zatayi ba hakan ne.

    Kowacce daga cikinsu an kawo kayan aure da sadakin ta,sadakin su Ummu yafi na Suhana dan na Ummu 50k neh,saina Khadija wato Hadiza 40k,ita kuma Suhana 35k aka bada. Wajen kayan akwati kuwa na Suhana yafi nasu duka,kama daga kan akwatuna har kayan dake cikin akwatunan.

    Koda aka zo bikin komai tare akayi musu,'yanuwa da abokan arziqi kowa ya halarta. Kwana uku akayi ana shagali kafin aka kammala,kowaccen su aka kaita gidanta. Kayan garan da akayi ma su Ummu duk yafi na Suhana,hakan kuwa ko a gyalenta dan bata ma sani ba. Masu ganin gida kuwa kowa saida fad'i cewa gidan Suhana yafi kyau da girma,dan kafin auren saida Alhj ya sa aka gyara gidan. Side d'in yaran shi maza kuwa daban dake duk manya neh,d'ayan kanma ya kusa aure,d'aya kuma yana service dan ya kammala degree d'inshi. Yara matan kuwa anyi auren babbar,saura su biyu,d'aya na ss2 yanzu d'ayar kuma primary one ta shiga yanzu. Anyi aure dai hankalin kowa ya kwanta.

     hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now