Page 34

87 10 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 34 💦💦

Da yamma kamar yadda Sadeeq ya fad'a mata zai dawo hakan yyi,wayanta yah kira ya sanarda ita cewa yazo.Da kamar bazata fita ba sae kuma ta canza raayi ta tashi ta shirya ta fita.Koda ta fita tsayuwa tayi a gefen motar dan batada niyyar shiga,bbu yadda beyi da ita ba kan ta shiga suyi maganar a zaune amma taqi,hakan yasa ya rabu da ita.

Haquri ya fara bata daga farko kan tayi haquri da abunda yah faru,cikin b'acin rai tace mishi "dakata mallam,idan wannan ne ya kawo ka wajena,it's better u leave here because haqurinka bazae qara mun komai ba,dan haka ka kama gabanka yanzun nan kafin raina ya sake baci".

Ganin ranta yyi matuqa wajen b'aci yasa Sadeeq cewa "shikenan,zan tafi amma dan Allah inaso kiyi qoqari ki gafarta mun ko ba yanzu ba,na barki lafiya".Kafin ya motsa awajen taja tsaki ta shiga gida ta barshi tsaye a wajen.Ko kad'an Sadeeq beyi nadamar abunda yyi ba dan in akwae sabo to yanzu ya saba da yaudarar y'an mata,(saedae muce Allah ya karemu daga shiga tarkon irin wayannan samarin,ameen).

Ita koh tana komawa ta nufa d'akinta inda ta shiga rera sabon kuka,dan a gaskiya bata tab'a jin son wani d'a namiji ba irin Sadeeq,amma daga qarshe ya cuceta,yasa aka koreta a scul,yyi mata ciki daga qarshe ma yace ba zae aureta ba.Ta jima tana kukan kafin ta daina.Bacci ne me nauyi ya d'auketa bayan nan..

****
Washegari da yamma bayan su Mommy sun dawo daga office,Suhana tayi making up mind nata kan zata sanarda su cewa tayi aborting cikinta.

Hakan kuwa akayi,suna zaune a palourn Daddy ta shigo ta samesu.Bata tsaya wata-wata ba ta sanarda su abunda ke ranta.

Ba ga haka saita k'ara da cewa "ina son barin k'asar nan dan bazan iya yin karatu anan ba gaskiya,ina son zuwa koda Uganda neh nayi karatun acan",cikin fuskar tausayi take maganar wanda hakan yasa iyayen tausaya mata kuma basuyi k'asa a gwiwa ba wajen amincewa da buk'atar ta.

Daddy yace "it's ok mamana,Allah ya kare ki ya kuma baki sa'a",tace "ameen dad".

Mommy ma ta d'ora nata akai daga bisani ta tashi sd'af-sad'af ta barsu wajen duk sunyi juguum suna tunani.

Tana komawa d'aki ta kira Suby k'awarta ta zanarda ita yadda ake ciki,Suby tayi shewa tareda fad'in "gaskiya k'awata kinji dad'i,iyayenki na matuk'ar sonki da biye miki,kinga yanzu saiki ci karenki bbu babbaka tunda ba kya k'asar".

Suhana tace "ke dai bari kawae,ai zaman k'asar nan ta gagareni dan wllhi kunyar had'uwa da y'an school namu ma nakeyi,amma yanzu kinga inna tafi can,bbu ruwana da kowa kuma zanyi abunda nake so bbu me saka mun ido".

Bayan sun gama waya da Suby saita kunna data ta shiga youtube ta cigaba da kallon wani series film da take kalla.

Ina labarin Fahyim?
****
A halin yanzu har an fara maganar aurenshi da k'anwar Aasim wato Fa'izah,Fa'iza na matuk'ar sonshi daman saidai bbu wanda ya sani sai ita da yayanta Aasim,sai kuma Allah da ya fi kowa sanin abunda yake bayyane da wanda yake b'oye.

Sanin Fa'iza na sonshi kuma Fahyim baida wata matsala yasa Aasim ya had'asu cikin dabara,shima kuma yace yana son Abida.

Shirye-shiryen aurensu yanzu ake tayi,iyayensu sunyi farin cikin faruwan hakan,suna me musu addu'ar samun zaman lafiya.A yanzu Ammee ta daina fushi da Fahyim,saima k'ara gode ma ubangiji da takeyi dan yanzu ta gano cewa Suhana batada mutuncin dan jin irin abunda tayi,dan yanzu magana ta fara bazuwa a makarantar su cewa tayi cikin shege,saidai ba a san wa yyi mata shiba.

   hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now