Page 69

58 6 1
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 69 💦💦

Ba qaramin mamaki maganganun ta suka bashi ba,maybe wani yayi breaking heart d'inda ne shiyasa take gudun soyayya,a ranshi ya fad'a. Komawa cikin mota yayi ya kunna ya tafi da niyyar zai dawo dan shikam yaga abinda yake so kuma baya tunanin akwai abinda zai hana shi aurenta saidai wani ikon Allahn. Yana komawa gida ya sanar wa iyayen shi abinda yake ciki,nan mahaifin shi yayi mishi alqawarin shige mishi gaba indai sun bincika sun ga asalinta nada kyau,hakan ba qaramin dad'i yayi mishi ba.


Suhana kuwa bata shiga cikin gidan ba saita tsaya a soron gidan tana kuka. Saida ta gama kukanta sannan ta shiga,tana shiga kuwa idon kowa ya dawo kanta cikeda tambaya. Baffanta yace "wanene?",tace "wani d'an makarantar mune tun ina university na nan garin",baffan yace "haka zaki qare ai,saidai d'an makaranta ba dai miji ba,toni wallahi na gaji da ciyar dake idan kika kasa auruwa duk wanda naga yamun dashi zan had'aki kinji na gaya miki,daman akwai wanda yamun maganarki ma".


Matar shice tace "sosai ma kuwa,kina gani qannan kin nanma auren su za ayi nan da wata biyar,gara ma ki samu ki fidda miji in kuma ba haka ba had'aki zamuyi da wanda Babbanfi yake so dan tare zamu aurar daku ehe,bazamu rabuda namu yaran sannan ke mu zauna dake ba",duk maganganun nan da sukeyi idon Suhana na qasa tana kuka.


Washegari da rana wajen qarfe biyu saiga mahaifin mutumin jiyan nan da wasu maza su uku. Sallama suka sa akayi musu da Baffa,sunci sa'a kuwa bai fita ba yana nan. Ba tareda b'ata lokaci ba kuwa ya fita,koda suka sanar dashi dalilin zuwansu yayi maraba da hakan sannan yayi musu alqawarin babu wata matsala,sannan yana son ganin yaron koda anjima neh. Sunyi farin ciki da jin hakan sannan sukayi godiya suka tafi ko ruwa basu yadda sun sha ba,a cewar su suna sauri neh.


Da daddare kuwa saiga mutumin nan,koda Baffa ya fito gaishe shi yayi shi kuma ya amsa cikin mutuntawa,ya tambayeshi "kaine Fadeel koh?",yace "nine Baba",Baffa yace "to madallah,daman nasa a turo mun kaine dan naji daga bakinka,shin kanason Suhana?",wani farin ciki Fadeel yaji kasancewar bai tab'a jin sunanta ba sai yanzu,a ranshi yace suna mai dad'i. A fili kuma ya amsa ma Baffa tambayar shi "eh ina sonta hasalima nina tura azo a nema mun izinin nemanta",Baffa yace "to babu matsala,mun riga da munyi magana da magabatanka akan nan da watanni biyar dama nake so na aurar dasu itada qannenta guda biyu".


Fadeel yace "babu komai duk an min bayani",Baffa yace "to madalla,barin shiga saina aiko maka da ita",Fadeel yace "to na gode Baba,a huta lafiya",baffa yace "yauwa",tareda komawa ciki. Befi shigarshi da minti uku ba saiga Suhana,tana tafe kamar wacce qwai ya fashe ma a ciki. Da sallama ta isa wajen shi,shi kuma ya amsa tareda sakar mata da murmushi kamar koda yaushe in sun had'u.


Cikin zolaya yace "amaryata ta kaina!",bata ce mishi komai ba,shima kuma hakan bai dame shiba. Bayan d'an wani lokaci jin shirun yayi yawa yasa Fadeel ya kira sunanta "Suhana!",ba tareda ta amsa ba ta juyo ta kalleshi,cigaba yayi "meyasa baki sona?". Sam ita har a ranta ba wai bata sonshi bane saidai cutar da take d'auke da ita ne tasan in har yaji to babu makawa fasa aurenta zaiyi,itama kuma bata son ta cutar dashi dan haka ta d'au aniyar dakatar dashi koda kuwa ta halin qaqa ne.


www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now