Page 33

118 8 3
                                    


💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

I'm wishing all the entire muslims a happy eid fitr,may Allah bless us with all the blessings of the day,may he answers all our prayers,may he forgive our sins and shower us with the khair upon the new year that is arriving,eid mubarak and juma@ mufeeda🙏🏼

Wattpad @
Hama_gee

Page 33 💦💦

Mommy da Daddy na zaune a palour duk sunyi tagumi,kowa da irin tunaninda yakeyi a ranshi.Suhana ceh ta bud'e qofar d'akinta kai tsaye ta fito,nan ta shiga qwalama Hadiza kira,bayan Hadiza ta fito sae take ce mata tana son shan tea neh,so taje ta dafa mata da kayan yaji saeta yi mata warming koma wane snack ta samu a fridge dan tasan fridge d'in dama baya rasa wani abin ci.

Bayan ta gama da ita sea ta koma cikin palourn inda tayi sallama su Mommy suka answer sannan ta shiga,ta dubesu bbu koh kunya kafin ta kira sunayensu "Mommy,Daddy!",dukansu suka kalleta tareda answer mata,tace "daman zan fad'a muku neh gobe ina so inje school dan na dubo result naji anyi placing".Mommy ta maida idonta kan Daddy taga shima itan yah juyo yake kallo,ta juyo tana fuskantar Suhana kafin tace "my dear be kamata a wannan situation d'innaki ki ringa fita ba,why not muje nida Daddynki mu dubo miki".

Wani irin b'ata rai Suhana tayi kafin tace "I want to check it my self and besides miye don na fita a haka?",Daddy neh yace mata "kin manta a irin halinda kke ciki neh?",Suhana tace "nidae gobe zanje na dubo result",ta tashi tabar palourn,duk tasu bbu wanda yah tanka mata kamar sune y'ay'an ita kuma iyayen.

*****
Washegari kuwa da safe ta shirya tsaf ta fito taje tayi musu sallama kafin ta tafi,bbu yadda suka iya kuwa dan koh musu bbu wanda ya gwada yimata a cikinsu.

Suhana na isa tayi parking mota tareda kiran Suby dan jin inda take,Suby tace ta sameta a qofar wani lecture hall.Bayan tayi hanging sae ta d'au jakarta tareda fitowa ta kulle motar sannan ta nufa inda Suby tace ta sameta,a sannu a hankali take tafiya kamar ko yaushe.

Tana daga nesa ta hango Suby tsaye daga gani jiran isowarta takeyi,ae kuwa nan da nan Suby ta fara yi mata murmushi daga hangenta,itama ta mayar mata da murmushin.Tana isowa suka gaisa sannan Suhana take tambayarta yadda zasuyi.Qarshe dai suka tsaida magana akan zasu je su samu Mal.Sadeeq kafin nan sae suje a zubar da cikin kowa ya huta.

Bayan sun gama shawarwarinsu kai tsaye suka nufa office d'in Sadeeq,sunyi sa'ar samunshi kuwa yana nan.A waje Suby ta tsaya Suhana ceh ta shiga ta sameshi,sallama tayi yah answer kafin ta qarasa har inda yake zaune,d'agowan da zaiyi sukayi ido biyu da Suhana,ya d'anji wani iri saedae ba har can,amma shi kanshi yasan be kyauta mata ba.

Ganin bashida niyyar yin magana yasa tace "ba wani abu bane yah kawoni wajenka illa nayi maka godiya kan kulada result d'ina da kai,kuma ina so ka sani wannan ba shine qarshena ba.Barina makarantannan does'nt mean I lost everything,not that,I'm here to inform u about the abortion am going to do,kuma kai nake so ka kaini ayi komai a gabanka becoz u r responsible for it".

Sai yanzu Sadeeq ya yi magana "it's ok,amma ina so ki san wani abun bbu irin qoqarinda banyi ba kan result d'inki ba amma be yiwu ba,am sorry for that",ba tareda tace mishi komai ba ta bar office d'in,shima tashi yyi ya bi bayanta,bayan sunje asibitin be kai one hour ba aka gama komai aka sallamesu,ba qaramin wuya Suhana tasha ba dan har yanzu cikin ta ciwo yake mata.

Sadeeq da kanshi ya maidasu gida kafin ya wuce akan anjima zaizo gidansu,Suhana dae bata answer mishi ba sannan kuma bata ce karya zo ba.Da qyar ta shiga gida,koda ta shiga kuwa bata tsaya ko ina ba sae a d'akinta inda ta kunna air condition kafin ta kwanta,saedae a ranta taji dad'in cire cikinnan da akayi dan ya fara damunta kuma yanzu tasan inta warke komai zai wuce mata da iyayenta dukda tasan in suka gano abunda tayi bazasu soba,amma tasan bbu yadda suka iya da ita.

hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now