Page 59

40 8 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 59 💦💦

    Komawa wajen mijin ta tayi ta sanarda shi abinda ake ciki. Shima baiji dad'in faruwar hakan ba,ba tareda wasting time ba ta kira gida ta sanar dasu dukkanin abinda ke faruwa. Ai a ranan suka nemi visa akan anjima da daddare zasu iso,maman tace ma Farheen ta zauna a jikin shi sannan koda Suhana tazo karta yadda ta barta taje mata jikin d'a daman inda abinda tafi so a rayuwarta to Farhan ne shiyasa ma yake abinda ranshi yaso tun yana qarami.

★★★
   Sai wajen qarfe tara na dare Suhana ta tashi,wanka ta shiga tayi sannan ta shirya ta fita zuwa asibitin. Koda ta isa kai tsaye cikin d'akin da yake ta shiga,ganin iyayen shi da 'yanuwan shi ba qaramin bata mamaki yayi ba. Tama rasa me zata ce musu, gashi kowa hararanta kawai yakeyi,da qyar ta daure ta iya gaida Maman da Baban. Cikin su babu wanda ya amsa mata gaisuwar,hakan ba qaramin d'aga mata hankali yayi ba.

     Maman dake gefen shi ne taga kamar yayi motsi dan haka ta maida hankalin ta kanshi,ai kuwa da gaske motsin yayi after so many days bai san inda yake ba. Numfashi ya fara yi sama-sama,Maman ce tace ma Farheen maza taje ta kira Doctor. Ba tareda b'ata lokaci ba Farheen ta fita,within some times ta dawo da Likita cikin gaggawa.

     Nan ya umarce su da su fita inya so parent nashi zai su zauna a jikin shi,bayan fitarsu ya shiga duba lafiyar shi,da qyar numfashin ya daidaita. A waje kuwa Farheen da Farhana sai kallon banza sukeyi wa Suhana,ga habaice-habaice wai tana son kashe musu d'anuwa.

    A day after,
Farhan ya d'an samu sauqi dan har ana cewa nan da two days za a sallame su dan har magana ya fara yi. Ana zaune a d'akin ana hira saidai Suhana bata cikin su dan da tazo jikinsu sai su soma hararta suna mata habaici,hakan yasa bata ma zuwa inda suke.

     Maman da Baban ne suka fita,Farheen kuma tana wajen mijinta suma gobe za a sallamesu,yaran kuma suna wajen Farhana dake jikin Farhan. Ganin Farhan yayi bacci yasa Farhana ta fita akan zata siyo abu a nan kusa ta dawo. Suhana na zaune tana kallon fitowar Farhana,kamar wacce aka mintsina tayi sauri ta miqe daga inda take.

     D'akin ta nufa dan ganin jikin Farhan dan tun jiya rabon da ta saka shi a idonta. Koda ta shiga kuwa bacci taga yanayi,tsayawa tayi tana qare ma fuskar shi kallo. Bata san lokacin da qwalla ya soma zuba daga idonta ba,ta jima tana kallon shi kafin ta shafa kanshi tareda goge hawayen dake idonta sannan ta fice,gida ta nufa kai tsaye.

    Koda ta koma Mommy ta kira tana mata kuka,da qyar Mommy ta rarrasheta tareda ce mata tayi haquri watarana zai zamto labari tunda Farhan d'in bazai dawwama a haka ba. Haka dai tayi ta rarrashin ta har tayi shiru kafin tayi hanging call d'in. Bayan nan wanka ta shiga tayi dan rabonta da wanka dan jiya da zata je asibitin.

    Wajen qarfe hud'u na yamma Mommy ta kira ta,inda ta umarce ta data tura mata kud'i zatayi amfani dasu. Ba tareda wani b'ata lokaci ba Suhana tayi sending 5m wa Mommy,Mommy ta kirata nanma tayi ta mata godiya tareda saka mata albarka. Bayan sun gama wayan be wuce da minti talatin ba Suhana taji an danna qararrawa na main door d'in gidan. Tana shirin fita ma kenan zuwa asibiti sai taji qararrawar.

      www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now