Page 41

61 7 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 41 💦💦

    Tarba me kyau yayi mata kafin ya gayyace ta zuwa can cikin d'akin shi,bata yi wata-wata ba ta amince dan tana son shi daman kuma itama d'in abinda ke ranta kenan. Yaji dad'i da bata bashi wata wahala ba ta amince da shi. Hakan ba k'aramin faranta mai ya yai ba. A haka sukayi sati guda da 'yan kwanaki,hakan ma da bazata tafi ba dan dai Farhan yace mata ya gama abinda yaje yi ne kuma yana dawowa in any moment of time.

    Michael yayi mata kyauta me tsoka tareda rakota har wajen mota,tayi mishi alk'awarin zuwa time to time. Bayan ta tafi saiya koma ciki jikin shi duk a mace,yana komawa ciki ya nemi guru ya kwanta yana kallon sama. Tunanin Suhana yayi tayi har yayi bacci a gurin.

    A wajen Suhana ma hakan neh,bata so tafiyar ta bar Michael d'inta ba,tana driving amma hankalinta gaba d'aya yana baya harta isa gida. Samu tayi har Farhan ya dawo gida,wai a dole zaiyi surprising d'inta. Ta mayar ma ko tun jiya ya dawo dan har gabanta ya fad'i,sai dai ta daure ta tambaye shi da yaushe ya iso. Yace mata yanzu shigowar shi,ya lura da damuwa a tattare da ita dan haka ya tambayeta me yake damunta,harya ce ko bata so ya dawo bane,tace mishi ba haka bane. Fakewa tayi da exams d'in yau beyi mata dad'i ba.

    Hak'uri ya shiga bata kamar shiya hana yayi mata dad'in. Haka suka cigaba da rayuwa har Suhana ta kammala exams d'inta na,babu yadda iyayenta basuyi da ita ba akan ta dawo gida tayi hutu amma sai tayi ta making excuses alhalin bata son dawowan ne.

    Bayan shekara guda..
Watanni k'alilan ya rage Suhana ta kammala karatun ta,a halin yanzu kuma sun rabu da Michael kasancewar ta kama shi da wata a gidan shi,ranan bai san zata zo ba kwatsam ya ganta. Babu irin hak'urin da bai bata ba amma ina fir tak'i,har yau kuwa bai rabu da ita ba dan duk chance d'in da ya samu sai ya bata hak'uri kamar wani maye.

    Farhan kuwa soyayyar tasu k'ara d'aukaka takeyi dan a yanzu tana ganin babu wanda zata so bayan shi. Hakan yasa suka yanke shawarar za suyi aure bayan ta kammala karatun ta,tare zasu koma gida inya so sai yayi ma iyayen shi magana suje su Nigerian tare.

    Bayan ta kammala kuwa Farhan ya sanarda iyayen shi suka je Nigeria neman aure. Ganin me hali ne gashi Suhanan ta kammala karatunta yasa iyayen suka amince,dad'i da k'ari ma ganin yadda take son shi dan koda sunga aibun shi in dai tace tana so to shikenan. Babu maganar da 'yan uwa basu yi ba kuwa akan meyasa za a yarda da shi bayan ba a san asalin shi ba,babu bincike babu komai kawai a d'au yarinya a bashi.

   Iyayen Suhana kuma a ganin su hassada ne kawai da k'yashi irin nasu,in ba haka ba baga iyayen shi yazo dasu ba kuma yarinya tace tana so,da ace baida hali me kyau da bazata yadda tace zata aure shi ba ai. Su dai basu ga aibun abin ba ko kad'an.

   Ba tareda b'ata lokaci ba aka fara shirye-shiryen bikin Farhan da Suhana. Shiri sosai akayi,'yan uwan Farhan kuwa tari sunzo dan ayi bikin dasu kasancewar dama tun tuni yak'i auren sai yanzu Allah yayi zai yi. An gama shiri tsaf za ayi hidima a nan sannan za a koma Uganda ayi wata hidimar. Sannan duk me son zuwa ya shirya dangin ango sun d'au nauyin zuwansu da dawowansu.

       www.hghausanovelseries.blogspots.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now