Page 51

53 8 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 51 💦💦

    Hankali kwance Mommy ta koma gida,ko irin taji abun ya d'an dametan nan bata yi ba. Bata fad'a ma kowa abunda ta aikata ba sai Suhana dan a cewar ta tayi hakan neh saboda farin cikin ta ya samu,ta manta cewa Allah ne ke samar da farin ciki me d'orewa ma.

****
   Bayan Farhan ya bar gidan ba ko ina yaje ba illa wani gidan shi dake wata anguwar,wanda Suhana ma bata san da shi ba. Nan ya koma dan baya qaunar ganin Suhana ko kad'an,yana ganin idan suna zaune waje d'aya duk sanda ya kalleta qara takaici yake ji shiyasa ya tafi. Sai dai komawar shi gidan baida wata sana'ar yi illa ta shan giya dan yanzu ya koma shan giya papa abin shi.

     Ko wanka baya yi balle maganar sallah,infact rabon shi da yin sallah har ya mance shekarar. Itama kuma Suhanan bayi take ba balle ta sa shi ya ringa yi,zaman su banda aikata aikin b'arna babu abin da suke yi. Dama dance duk alaqar da ba a d'orata kan gaskiya ba bata d'orewa.


    Some days ltr,
Farhan na kwance yana shan bacci dan ya sha giya har taso tayi mishi yawa ma,mafarki yayi wai Suhana na kiran shi akan ya koma gida. Bai jima ba cikin mafarkin ya tashi da hanzari yana kiran sunan ta,shikenan aikin da boka yayi Allah ya bashi nasara a kai tunda Allah ne ke barin komai ya faru. Dad'in qarawa ma Farhan ko sallah bayayi balle azkar,wanda yin azkar ba qaramar kariya take bamu ba a koyarwar Annabi mafi girma Muhammad S.A.W,Allah yasa mu tashi cikin zab'bb'un ka ameen.


    Babu shiri ya d'au keyn motar shi da waya ya fice,kayan jikin shi kuwa tun wanda ya saka ran da ya bar gidan. Bai tsaya ko ina sai qofar gida inda ya danna horn me gadi ya bud'e mishi ya shiga. Kai tsaye side d'in Suhana ya nufa dan ya qagu daya ganta,shi dai burin shi tayi accepting d'in shi kawai.

  Suhana kuwa tana jin bud'e gate tayi sauri ta shiga d'akin ta ta kulle ta ciki sannan ta cire kaya ta saka towel kafin nan ta shiga wanka. Murna kuwa baya misaltuwa a ranta,tana jin lokacin da yazo yana knocking amma tayi shiru tana murmushi kawai. Bayan d'an wani lokaci ta gama wankan ta fito,goge jikin ta tayi sannan ta d'aura wani towel d'in mara jiqa. Dai-dai lokacin tazo ta bud'e qofa tana tambayar "who's it?",kamar bata san Farhan d'in bane.


   Tana bud'ewa sukayi ido hud'u dashi,zuba mata ido yayi itama hakan tayi sai dai karya raina ta abinka da mata sarakan jan aji sai ta kauda idonta daga ganin shi. Tace "and what brought you here?",be ma ji abinda tace ba dan gaba d'aya qwaqwalwar shi kamar ta juya yake ji. Tambayar ta sake yi "I asked you,what brought you here?".


    Be ce komai ba sai yunqurowa da yayi kanta,da sauri ta koma ciki ta rufe qofar dan bata shirya mishi a yanzu ba tasan kuma halin Farhan,haka kawai ma baida sauqi balle yadda yake jin shi a yanzu. Knocking qofar ya shiga yi yana fad'in "I'm so sorry my love,you know it I can't do without you so please accept my apology since I am back for you and only you",haka yayi ta surutan shi amma tana ji tayi shiru kuma bata bud'e qofar ba either.



     www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now