Page 52

61 8 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 52 💦💦

    Zama Farhan yayi a wajen yana kan surutan kuma bai fasa ba. Suhana kuwa wayarta ta d'auka ta shiga kiran Mommy,ringing na farko bata amsa ba sai ana biyu. "Yauwa Mommy,na kira ne in baki good news!"ta fad'a cike da zumud'i. Mommy tayi farin ciki da jin hakan dan haka babu b'ata lokaci ta tambaye ta "yaya akayi?". Nan Suhana ta shaida mata cewa Farhan ya dawo gidan kuma a yanzu haquri ma yake bata,sai dai tana ganin gara ta d'an ja ajinta kad'an tukunna.


   Ai da gaggawa Mommy ta tare ta "haba Suhana,ware irin aji kuma? A yanzu har wani aji ne gareki ko kuma neman damar ta kubce mana?". Maganar Mommy ba kad'an ba ta sosa ma Suhana rai,ita Mommy ke kira mara class? Lallai Mommy na nema ta jiqa ma kanta aiki kenan dan yadda take jinta a yanzun nan zata iya fita sha'anin ta ma gabaki d'aya in yaso tasan yadda zata kula da kanta da kuma Daddy da bashi da lafiya.


    Suhana na cikin wannan tunanin Mommy ta katseta da "look my daughter! I don't said it to hurt you ohk? Please try to understand me,idan mukayi missing wannan damar wallahi muna cikin uquba babba". Suhana ta d'an sassauta murya da jin hakan tace "amma miyasa zaki zageni da banda class to?",Mommy tayi murmushi dan tasan halin 'yartan da shegen rigima,tace "look I don't mean it that way,but if you feel obsessed, I'm sorry".


    Suhana tayi smiling kafin tace "it's ok then". Mommy tace "that's my girl,yanzu abinda make son kiyi shine ki tashi kije ki karb'e shi hannu bibbiyu kamar ma babu abunda ya had'a ku sannan kiyi mishi duk abunda kika san yana son kiyi". Suhana tace "toh shikenan Mom,ya jikin Daddyn?",Mommy tace "gashi nan dai,har yanzu jikin yaqi dad'i yanzu so nake in kika karb'a mana wasu kud'ad'en daga wajen Farhan d'in sai mu je Germany dan naji akwai wani qwararren Likita daya qware ta wannan fannin,kin ga idan muka yi sa'a aka dace shikenan mun huta da wannan wahalar".


   Suhana tace "gaskiya kam Mommy,barin sa kaya dan yanzu fitowata daga toilet nayi wanka",Mommy tace "ohk,kar dai ki manta da batu na kinji",Suhana tace "tana sane,ki gaida min Daddy nah". Mommy tace "zaiji,sai zuwa anjima,kuma kada ki manta as soon as kukayi settling ki samu ki karb'i kud'i ki aiko mana dan ina so nan da baifi sati ba mu samu muyi tafiyar nan". Suhana tace "don't worry daman wuyanta ya karkato kaina neh". Bayan nan dai sukayi sallama tayi hanging call d'in.


    Nan da nan ta shafa mai da tararurruka kamar yadda ta saba yi sannan ta saka kayanta ta fito. Kamar yadda Mommy tace tayi hakan tayi,taimaka mishi tayi ya tashi tsaye sannan ta rungume shi tana kuka tareda fad'in "promise me that you'll never leave me",yace "that's my promise to you my love. I so much miss you",tace "I miss you even more".


    Bayan sun gama sasanta wa side d'in shi suka koma inda ta qara nuna mishi cewa lallai ta haqura. Kamar yadda Mommy ta umurta kuwa cikin dabara tasa yayi mata transfer d'in kud'i na 3m to account d'inta,dama yaya shikam wajen bata duk abinda take buqata balle yanzu an shanye shi bashi da ikon qi. 2m ta tura wa Mommy washegari kenan.


      www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now