page 43

69 6 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 43 💦💦

    Nan ya bama Likitan duk wani kud'i da yake buqata har ma da extra incase dan ba yanzu zai dawo ba. Suka yi sallama sannan ya fice daga asibitin ya nufi gida. Baya son ganin kowa a wannan lokacin dan haka yayi gargad'i wa me gadin cewa duk wanda yazo ace bazai samu ganin shi ba dan koya zauna jira ba lallai neh ya ganshi don haka kawai mutum ya tafi.

    Da rawar jiki me gadin ya amsa mishi cikin ladabi. Daga nan ya shiga cikin gidan ya nufi side d'inshi tareda kulle k'ofofi. Kayan jikin shi ya cire tareda shiga toilet yayi wanka sannan ya fito ya shirya tsaf cikin farar t-shirt da wando three-quater. Bayan nan ya dawo kan gado ya kwanta,kan shi na kallon sama.

    Nan ya shiga tunani iri-iri, _*a ina suhana ta samu cutar HIV? Dama can tana dashi ko kuma a sama ta samu,amma in tunda tana dashi meyasa bata sani ba,ko da yake ko ta sani ai baza ta fad'a ba.Bama wannan ba yaya akayi har ta tab'a abortion amma bata tab'a fad'a mishi ba,duk da babu b'oye-b'oye a tsakanin su.*_

    _*Daman tayi yawace-yawace kafin suka had'u kenan,amma in dai hakane to ta cuce shi,dan duk da shima d'in ya sha yin mu'amala da mata amma ba har haka ba,kuma bai tab'a yi ma wata ciki ba balle yayi maganar zubarwa sannan a iya sanin shi bashida HIV tunda ya jima baya kula mata kafin ma su had'u da Suhana.Duk wannan tunanin shi kad'ai yake tayi.*_

   Tashi yayi yaje sitting room,wani glass naga ya bud'e tareda d'aukan kwalba. Kwalban nan na giya ne babu shakka,rabon shi daya sha harya manta. Cup ya d'auka kafin ya koma kan kujera ya zauna,nan ya bud'e kwalbar giyan nan ya zuba a cup sannan ya fara sha a hankali. Yana sha yana lumshe ido har ya gama da kwalbar nan tas.

    Bayan ya shawu ya bugu sai ya miqe akan zai tafi d'aki,ai anan ya zube sai bacci dan bema iya ya tashi ba. Bashi ya farka ba kuwa sai bayan sallahn magrib tun kafin azahar. Yana tashi ya sake yin wanka tareda yin dinner tunda already yanada masu aiki kuma sunyi girkin.

    Bayan nan saiya shirya be koyi sallah ba ya fita,rabon da yayi sallah shi kan shi ma ya manta dan bai isa qayyadewa ba sai dai yayi qarya. Kai tsaye asibitin ya nufa inda ya samu Likitan yace mishi yana so a duba shi duk da yasan cewa definitely yana dashi.

   Ba tareda wasting time ba Likita ya rubuta mishi test sannan ya bashi yaje a gwada shi. Zuwa yayi akayi mishi gwaji inda aka gano shima nada cutar,shi bai tab'a yin nadamar wani abu a rayuwar shi ba kamar sanin Suhana da yayi duk da yanzu ya yanke ma kanshi shawarar rabuwa da ita,sai dai kuma aikin gama ya riga da ya gama.

     Suhana kuwa an yi mata wankin cikin sannan an juya mata mahaifa inda bazata ma sake samun ciki ba dan rashin yin hakan yana nuna barazana ga rayuwar ta ne. Dana sani da nadamar zubar ciki kuwa yayi shi yafi a qirga,tsana da wasan Suby ne ya taru yayi mata yawa a halinda ake ciki tunda da bata bata shawarar zubarwa da bata zubar ba. Sai dai yanzu bakin alqalami ya riga da ya bushe dan babu wani hope na dake yin wani cikin ma balle ta haife shi. Dama hausawa sunce "qarshen alewa qasa,kuma duk abinda ka shuka dole shi zaka girba",Allah yasa mu gamada duniya lafiya kuma mu samu lahirar mu ma hakan,ameen...


     www.hghausanovelseries.blogspots.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now