Page 57

49 8 3
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 57 💦💦

    Yau kimanin sati guda kenan da fara jinyar Farhan amma babu wanda Suhana ta sanar ma a cikin 'yanuwan shi. Hatta mahaifiyar shi ma bata da masaniya akan rashin lafiyar,a tunanin Suhana rashin fad'in shine yafi mata alkhairi dan tasan lallai idan suka zo to zasu gano abinda ke faruwa a tsakaninsu,ita kuma bata son abinda zai iya raba ta da Farhan a yanzu,hakan yasa taja bakinta tayi shiru.

    Duk wani abinda ake buqata kuwa tana yi,dake atm cards d'in shi duk suna wajenta neh yanzu kuma tasan pin d'in so sai yadda tayi kawai. A cikin satin nan ba qaramin kashe kud'i sukayi wanda hakan yasa ta fara tunanin fad'a ma 'yanuwan shi dan a ganinta k'in zasu iya qarewa idan suka cigaba da amfani dashi kamar yadda suka faro.

     Wani abinda yake qara damunta kuwa shine ganin yadda jikin nashi kullum yake qara tsananta,a maimakon ta ringa ganin sauqi a kullum sai dad'a cigaba da tsananta yakeyi. Gashi a halin yanzu ma Farhan bai san inda yake ba,gashi sunce jinin shi yana ta shanyewa so koda yaushe cikin saka mishi jini akeyi dan zai iya qarewa at any moment. Yana gama shan wannan ledar za'a qara saka mishi wata,wani babban tashin hankalin ma shine duk Likitocin sun kasa gano matsalar balle kuma ayi tunanin shawo kanta.

      Farhan na kwance a kan gadon asibitin kamar kullum a yanzu. Suhana ceh ta shigo d'akin duk hankalin ta ya bar jikinta. Gefen shi tazo ta zauna tareda qura mishi ido,bata san lokacin hawaye ya soma zuba daga idonta ba. Surutu ta fara yi kamar tab'abb'iya "wayyo Allah nah! Yaushe zaka miqe my Farhan,you know that I always love you right,and nothing can change that. So please I beg of you for the sake of my love just get up,talk to me even once. Call my name,say Suhana I love you and will not leave you forever".

     Kuka mai qarfi ta shiga yi tana surutai. A take taji tsanan Michael yazo mata dan duk shiya janyo mata wannan abun. Ga matsalolin kanta da yawa yanzu kuma ga Farhan a kwance,ta rasa da wanne zata ji. Share hawayenta tayi sannan tace "ya zamo dole in sanar da iyayen Farhan inya so koma miye zasu yi suyi dan bazan iya handling d'in shi ni kad'ai na ba,gashi kullum abin qaruwa yakeyi instead of a samu sauqin shi".

    Tashi tayi ta koma gida dan dama ba ita ke kula da shi ba kasancewar tsarin asibitin dama su suke kula da marasa lafiya,hatta abinci su suke bayarwa dan komai na cikin kud'in jinyar. Tama rasa wanda zata kira da kuma ta inda zata fara fad'a musu,kuka ta fashe dashi kawai ganin ta rasa mafita.

     Can tayi tunanin kiran Mommy dan neman shawararta kan ta yadda zata sanar ma iyayen shi abinda ake ciki dan lamarin yafi qarfinta yanzu kam. Ringing na farko Mommy ta amsa da "hello,Suhana ya kuma aka yi?". Suhana tace "I can't hide it from them anymore, Mommy can you imagine how the sickness is getting worst now? I think it's better to let them know".

   Mommy tace "hakane but baki tunanin abu yaje ya dawo? Kin san cewa definitely idan suka zo zasu so susan menene matsalar,kuma dole za a ce musu yanada HIV kuma sun san cewa d'ansu bayi da wannan cutar". Suhana tace "that's it Mommy amma a halinda ake ciki yanzu ya zamo dole in sanar dasu because ba zan iya yi ni kad'ai ba,karfa ki manta yau kwanan shi biyar baya ko motsi kuma koda yaushe cikin shan jini yake,so I think they should just know".

    www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now