page 42

65 8 3
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 42 💦💦

   Biki aka yi na gani na fad'a dan an kashe kud'i sosai,kama daga kan dangin ango har na amarya. Anyi sati biyu ana abu guda,bayan an kammala biki kowa ya koma gidan shi tareda fatan zaman lafiya wa amarya da ango. Mommy kuwa har kuwa saida tayi na rabuwar su da suhana,itama Suhanan tasha kuka. Su Suby kuwa tare aka tare da amarya dan koda aka gama biki cewa tayi bazata dawo ba saita d'anga gari tukun.

   Wajen qarfe biyu na rana kowa yayi tafiyar shi,aka bar Suhana da Farhan sai kuma Suby wacce suka ware wa makeken d'aki guda ita kad'an ta. Hakan ba qaramin dad'i yayi mata ba,tare suke fita in zasu zaga gari.

    Saida tayi sati biyu masu kyau kafin ta tattara ta koma gida,Farhan ne ya biya kud'in flight sannan sun mata goma na arziqi kafin ta tafi. Shikenan Suhana ta koma Uganda da zama,ta qara fresh abinta akan na da. Hankalin ta ya kwanta kuma,sai dai kwana biyun nan ta kan ji sauyin yanayi. Yau taji jiri gobe taji zazzab'i sama-sama,sai jibi taji ciwon ciki.

   Kamar koda yaushe tana kwance kan three seater tana latsa wayarta kawai taji wani irin murd'an ciki. Babu shiri ta qwalla ihu,Allah yaso ba ita kad'ai bace a gidan akwai masu yi musu hidima dan ko tsinke Suhana bata d'agawa a gidan,rayuwar hutu kawai suke yi abinsu.

    Da sauri ta qaraso kanta tana tambayar lafiya kuwa,ganin yanayin da take ciki yasa tayi maza ta kira wani daga cikin masu aikin dan yazo ya taimaka mata. Yana zuwa bai yi wata wata ba ya kira Farhan dake office,ba tareda b'ata lokaci ba kuwa sai ga shi ya iso.

    Bai tsaya jin komai ma ya d'auke ta ya sanya ta cikin mota sannan ya ja suka tafi. Asibiti ya kaita straight, da gaggawa aka karb'e ta saboda yanayin ta a lokacin is critical dan bata cikin hayyacin ta ma. Bayan nurses sun kaita emergency sai ga likitan da zai duba ta,ba tareda b'ata likaci ba ya shiga.

     Shi kuma Farhan na waje yana ta saqa da warwara akan miye ya sameta haka,shi dai yasan ya fita ya barta lafiya lau sai kuma wannan abin yazo ya faru. Shi dai fatan shi Allah yasa abin yazo musu da sauqi dan gaskiya ya tsorata ganin yanayin da take ciki lokacin da suka zo asibitin.

     Bayan wani lokaci Likitan ya fito tareda yi mishi magana akan ya biyo shi zasu tattauna,nan da nan ya bi bayan shi dan jin feedback. A nan ya yi mishi bayanin komai gameda matsalar da aka samu,abinda yake faruwa shine Suhana ta samu ciki wanda a halin yanzu ya kai wata biyu a jikinta sai dai dole a cire shi dan bazata iya haifa saboda lalacewa zaiyi mata a ciki in aka bari.

   Ba wani abune ya sanya hakan ba illa mummunan abortion da ta tab'a yi a baya,sannan ya qara tabbatar mishi da cewa ciki ba zai tab'a iya zama a jikin ta ya wuce wata uku ba. Sannan ya zamo dole ayi mata wanki ciki nan da awanni inba haka ba kuma rashin yin sa zai iya haifar mata da gagarumin matsala.

    Sannan a binciken da yayi ya gano tanada HIV wanda shima ya kusa yin chronic idan ba a d'au wani mataki da wuri. Wani irin jiri neh ya d'ebi Farhan Wanda yasa ya kusan fad'uwa ta baya,yama rasa abinda zaiyi ko zai ceh. Qwalla ne suka soma zubo mishi dan yasan definitely shima ba za'a rasa cutar nan a jikin shi ba.

    Ana wata ga wata....

      www.hghausanovelseries.blogspots.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now