Page 50

48 12 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*This page goes to Pretty queen,Allah ya bar min ke*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 50 💦💦

    Michael ne ya fad'o mata a rai,tana tunanin ko shine ya sanya mata cutar nan. Tabbas biri yayi kama da mutum dan akwai wasu qwayoyi da taga yana sha,koda ta tambaye shi sai yace mata yana da asthma neh. Gashi maganin sunyi kama dana HIV amma saboda son shi da take idon ya rufe ta amince da abunda ya fad'a mata.


     To lallai indai har shi ne ya saka mata to ta cuce Farhan kuma dole ta nemi afuwar shi. Shiryawa ta shiga yi akan zata je gidan Michael dan warware zare da ababa. Bayan ta shirya saita d'au tsohon layinta sannan ta sanya shi a wayar. Messages tagani rututu suna ta shigowa,mafiya yawancin su na Michael neh dan a rana ya kan mata messages hud'u zuwa biyar duk na bada haquri.


    Zama tayi ta shiga karanto su cikin hanzari. D'aya bayan d'aya take bi tana karantawa,daga farko dai duk na haquri ne akan ta haqura ta dawo gare shi dan babu wacce yake so sama da ita. Haka tayi ta bisu tana karantawa kafin ta iso kan wani wanda ya mugun girgiza ta,ba qaramin razana ta yayi ba,message d'in an rubuto shine kamar haka:

   *"Ever since we met, I've never loved anyone else apart from you. Because of the love I've for you,I think I shouldn't hide this secret from you anymore, I'm HIV position Suhana,that means you have it also,ever since I got it I promised myself to spread it among many girls because it was a girl I loved that give it to me. But unfortunately the love I have for you tells me that I shouldn't do this to you,so am very sorry and I wish you'll come back to me later or sooner"*..


    Tana gama karantawa zufa ya keto mata,duk da kasancewar d'akin akwai air condition. Bayan d'an wani lokaci saita dubi wayar ta cigaba da karantawa,message na qarshe kuwa shine "I'll be glad if you come back to me because I'll take good care of you because you are the only one I love".


    Bayan ta gama karantawa saita kira numbern Suby ta sanarda ita komai,har rayuwar da sukayi da shi Michael d'in. Suby tace "yanzu abin yi shine,idan har shi Farhan d'in kika kasa gane mishi kawai mu juya mu koma ga shi Michael d'in dan ina ga za a fi samun abinda ake so tunda king a shi ya saka miki cutar dama,so ba zai guje ki ba. Suhana tace "amma kina ganin hakan yayi dai-dai Suby?",Suby tace "hakane dai-dai baby". Suhana tace "to shikenan,mu jira dawowar shi inyaso idan naga reactions d'in shi zaki ji feedback, sannan nagode da so da kulawar da kike nunawa a gareni",Suby tace "that's the friendship, don't worry". Sukayi sallama kafin Suhana tayi hanging call d'in.


    Bayan sun gama wayan Suhana ta koma ta kwanta,tunani kala-kala ta shiga yi. Kamar zata kira Fardan sai kuma ta fasa. Mommy ta kira taji bata amsa ba dan haka ta ajiye wayar,bata jima ba tayi bacci.

★★★
   Ba wani abu Mommy ta tuno ba illa kayan daya kawo musu lokacin da zasu zo da Suhana. Daga cikin kayan akwai takalmi so shi ta d'uka ta koma wajen bokan nan,take ya tabbatar mata da aikinta ya gamu,ta koma gida ta jira ganin aiki.



      www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now