Page 66

52 7 3
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 66 💦💦

    Waje suka samu suka zauna sannan Mommy ta dubi Suhana tace "Allah yayi wa mahaifin ki rasuwa Suhana",wani irin jiri ne ya kusa yarda Suhana danma a zaune take,abinka da tsakanin d'a da mahaifi sai Allah. Kukan nema ya gagareta sai kawai ta koma ta d'an kishingid'a a kan kujerar. Suby kuwa salati ta shiga yi tana fad'in "Allah ya gafarta mishi yasa ya huta,sannan Allah yayi mishi rahama mu kuma in tamu tazo yasa mu cika da imani",Mommy ce ta amsa mata da "ameen" dan Suhana kam tana ta kanta neh.

   Ganin yadda a lokaci guda duk Suhana ta kid'ime yasa Suby ta shiga bata baki "haba Suhana mutuwa fa tana kan kowa,daurewa zakiyi,kuma ma insha Allahu ya tafi a sa'a sakamakon irin wahalhalu na jinya da yayi ta sha d'innan". Suhana bata ko amsa mata ba,can ta fashe da kuka mai tsanani abinka da dama ba islamiya taje ba ballantana tasan cewa haramun neh kuka me had'e da ihu ko hayaniya ga mamaci. Tana yi Suby na bata haquri,harta d'an sassauta muryarta dan muryar ta riga da ta dishe.

    Can aka fara shigo musu ta'aziyya,kama daga 'yan anguwa zuwa 'yanuwan Daddyn. A cikin su kuwa akwai masu yima Mommy habaici dama ba sonta suke yi ba asali,kasancewar Daddy nada kud'i suna cin arziqi a wajen shi yasa basuyi mata ido da ido. Daga cikinsu kuwa akwai masu fad'in ai itace ta kashe shi dan taci dukiya.

    Wasu na fad'in ita ce ta nakasa shi tun farko dan taci arziqi sai kuma yazo ya talauce,babu abinda basu fad'a mata ba na b'atanci amma shiru kake ji dan ko Suhana bata tanka musu ba balle Mommyn. Kaf abincin gidan saida aka dafe su wa 'yan zaman makoki,a cikin qannen Daddy kuwa akwai wa'yinda musamman suka baro gidajen su suka dawo gidan suna kwana tsabagen neman ayi.

   Banda hantara kuwa babu abinda sukeyi wa Mommy da Suhana,ana haka har anyi sadakar bakwai. Maimakon su tafi saima canjen rana da sukeyi a tsakanin su,idan guda biyu suka kwana biyu sai su koma gida wasu biyun su dawo suma su kwana biyu,sunyi matuqar saka Mommy a gaba hakan yasa rana a tsaka ta yanki jiki ta fad'i,daga dukkanin alamu ciwon tane ya tashi.

    Suhana da taimakon Suby neh suka kaita asibiti dan in don ta qannen Daddy neh sai dai ta mutu a wajen dan ko d'aga ta baza suyi ba balle su kaita asibiti. Koda suka isa asibitin taimakon gaggawa aka yi mata dan direct to imagency aka tura ta,Suhana kuwa banda kuka babu abinda take yi. Suby ceh me d'an rarrashinta,itama d'in gabad'aya tausayin Suhana take yi.

    Bayan kaman twenty minutes da karb'an Mommy sai ga wata nurse da hanzarinta,ganin su Suhana a tsaye yasa ta tambayesu ko sune suka kawo mara lafiya yanzu,sukace sune. Nurse d'in saita ce "ok,who's the woman's daughter amongs you? Her attention is needed by the patient please",tana kaiwa ta juya ta fara tafiya.

    Nan Suhana tabi bayanta da sauri,cikin qanqanin lokaci sai gasu nan a d'akin da Mommy take,da sauri Suhana ta qaraso inda Mommyn take ganin idonta biyu neh lokacin. Kuka mai tsanani ta shiga yi tana fad'in "get well soon Mom please,I don't want to miss you even for a second from now on I promise, don't leave me the way Dad passed away",kuka take kamar yarinya tana maganganu. Mommy ta tausaya ma Suhana sosai,dafa ta tayi sannan Suhanan ta d'ago kanta tana kallon Mommyn.

    www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now