Page 40

66 7 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 40 💦💦

    Washegari Suhana taje hotel d'in da suka dauk'a ta gaidasu,bayannan ta dawo gida a kan zata koma anjima dan suma fitar suke son yi yanzu. Bayan tafiyar ta suka fita zuwa kasuwanni inda suka yi 'yan siyayyar su sai dai kallon kayan yafi siyen kayan da suka yi yawa. Sun d'an zazzaga babu laifi kafin suka dawo lokacin ana kiran sallahn la'asar dan tun d'azu sukayi azahar,suna wucewa sukaji ana kira sai suka tsaya a wani masallaci sukayi sallahn.

   Da yamma kuwa bayan sun koma suka sanarma Suhana  dan haka ta dawo ta samesu,nan suka fara zantuttukan bayan bata nan,itama tayi ta basu labari kan yadda ta sha gwagwarmaya kamar da gaske. Su kuma tausayinta neh ya kamasu daman yaya balle sunji irin wahalhalun data sha,sai dai yanzu tace musu ba kamar da bane dan yanzu ta k'ara sabawa da gurin da kuma mutanen gurin so dole abin yazo mata da sauk'i.

   Sun kai har dare kafin ta tafi bayan sunyi dinner kenan,tana komawa gida ta kira Farhan ta sanar dashi cewa zai iya dawowa gida dan yanzu bata expecting d'insu. Infact ma gobe taji sunce zasu tafi dan akwai wasu k'asashen da suka ce zasu bi kafin su koma gida,kuma ita zata je tayi musu sallama.

★★★
Washegari da safe,
   Tun k'arfe 7 ta shirya ta fice daga gidan,wajen su Mommy taje dan da wuri suka ce mata zasu tafi daman. Koda suka zo rabuwa ta d'an damu abinka da iyaye sai dai damuwar ba har can dan sunma fita damuwa. Su dai sun rattashe ta dan a zaton su tafi su jin rabuwar da zasu yi yanzun,basu san alla alla ma take su tafi ba ita kam.

    Bayan tafiyar su da kwana biyar Suhana suka shirya inda zasu had'u da sabon saurayin ta me suna Michael dan bama musulmi bane shi. Sun yi akan zasu had'u a gidan shi dake nan garin da take kuma ta amince kasancewar yau Farhan zaiyi tafiya wai zashi America akwai wani contract da yake dashi da wasu company.

    Tun safe ya bar k'asar akan cewa zaiyi sati biyu a can,yayi kewar ta sosai dan kafin ya tafi ma yayi ta jimami dan dai kawai babu yadda ya iya ne shiyasa bai fasa tafiyar ba. Ita ma d'in ta haka ta nuna mishi ta damu amma bazata iya binshi ba saboda exams zasu fara week d'in da za'a shiga.

    Kafin ya tafi sai da ya tabbatar bai barta da wata buk'ata ba dan saida ya saka mata enough kud'i a account d'inta wanda zai isheta duk wani biyan buk'atar ta. Bayan tafiyar shine ta kira Michael akan ya shirya tana nan zuwa nan da 2 to 3 a hours hakan nan. Yayi maraba da zuwan ta.

   Bayan ta gama shirin ta ne ta fita zuwa gidan Michael,sanye take da riga da wando kanta babu ko mayafi,ta wani tufke gashinta da ribbon colourn kayan jikin ta dama gata da gashin. Sai ta fito sak irin fararen fatar,basu wuci mintuna 30 ba sai gata a cikin gidan Michael.

    Kiran shi ta shiga yi ta fad'a mishi cewa gata nan ta iso,shine ya fito yazo ya shiga da ita har cikin gidan. A sitting room ya barta sannan yaje da kanshi ya kawo mata drinks,ga ma'aikata kaca-kaca a gidan amma shi da kanshi yaje ya kawo mata saboda karramawa. Godiya tayi mishi lokacin daya zuba yoghurt a cup ya mik'a mata,ta karb'a tareda yin smiling kafin tayi sipping d'aya.

      www.hghausanovelseries.blogspots.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now