Page 36

95 7 0
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 36 💦💦

Kamar yadda yayi mata alqawari kuwa yana komawa gida ya kirata lokacin anyi sallahr magrib kenan,hiransu suka sha kafin yayi hanging.

*****
A halin yanzu saura kwana biyu a d'aura auren Fahyim da Fa'izah sai kuma Aasim da Abida,anata shirya amare dan yau za'ayi kamu.Kowaccen su tayi kyau sai faman d'aukan su hoto akeyi,bayan sun isa wajen yin kamun ne aka fara gudanar da event d'in,ga amare ga frnds d'insu ga kuma y'an uwa da abokan arzik'i,bayan an gama sai aka rufe taro da addu'a kamar yadda ake bud'eta sannan kowa yayi tafiyarshi.

Washegari kuma Walima sukayi,wanda ko wacce a gidansu tayi nata saboda haka babu wacce taje na watansu.Nanma komai ya tafi dai dai kuma duk amaren kaya iri d'aya suka sanya kaman na jiya,bayan an gama kowa ya watse.

*****
Washegari,
Ranan asabar kenan kuma wacce tayi dai dai da ranar d'aurin aure,ranar yaukam ta angwaye ceh dan su suke ta shirye shiryensu.Jiya aka kawo musu kayanda zasu saka a yau,iri d'aya neh har aikin dake jiki.Kowanne kuma harda babbar riga,hatta takalmansu da hula da iri d'aya neh.Wannan kuma ba aikin kowa bane illa na Abbansu Fahyim dan shine ya bada ordern kayan duka.

Around k'arfe 11 na safe aka d'aura auren Aasim da Abida,sannan aka zo akayi na Fahyim da Fa'izah,kowa Alhmdllh yake cewa barinma angwayen dan sunfi kowa farin ciki a yau,bayan su sai iyayensu sannan sai abokan arzik'in da suka samu halartar d'aurin aurensu.

Kowa sai taya su murna yakeyi tareda d'aukan hotuna dasu,bayan an kammala kuma sai aka wuce reception dan dad'a k'awata abun,abokansu ne suka shirya musu wannan a matsayin gudumawar su dan taya su farin ciki,sannan anjima da daddare akwai dinner kafin akai amare.Kowa yaci yasha kuma an tayasu murna sosai,ji suke kamar babu wata rana da ta kai musu wannan farin ciki a iya rayuwarsu,bayan an gama sai kowa ya watse saura angwaye da wasu daga cikin abokan nasu.Gidan wani abokin nasu suka tafi.

Su Abida kuwa sai kuka suke na jimamin rabuwa da gida,dukda irin sonda sukeyi wa mazajen amma wannan jimamin dolene dan haka k'awayenda ke kusa dasu sai hak'uri suke basu,basu tare amma ko yaushe suna waya.

Da dare yayi around 9pm amare da angwayensu suka halatta cikin wani babban hall wanda ya k'awatu kuma ya amsa sunanshi na hall,ko wannensu na tareda da amaryarshi,kayansu nanma iri d'aya sai faman haska waje sukeyi.Kayan amaren Blue da fari neh,su kuma angwayen fararen shadda bugaggiya suka sha sai akayi aikin jiki blue,hula blue me ratsin fari sai takalma blue.Ba k'aramin kyau sukayi ba,shi kanshi wajen blue and white decoration akayi sai d'an red kad'an.

K'awayen amare ne suka sanya red d'in kaya da silver head,sauran mutane kuma colour of the day d'insu silver neh.Daga jin wannnan tsari kaima me karatu kasan cewa ba k'aramin haskawa wajennan yayi ba,dinner yayi kyau anci ansha anyi rawa,an watsa kud'i.Wajen sha biyun dare aka gama aka kai amare gidajen iyayen mijinsu dan sai anyi wuni gobe za'a kaisu ainihin gidajen nasu.

Kowannensu yayi baccin farin ciki yau.Washegari akayi wuni sannan aka kaisu da daddare,bayan an kaisu anga gida sai kowa yayi misu fatan zaman lafiya sannan aka watse,abokai da k'awaye ma sukayi nasu nasihar sannan suka tafi suka bar ko wane ango da amaryarshi.Allah sarki Fa'iza yau burinta na zama matar Fahyim ya cika,batareda ta zubar ma kanta da mutunci ba sannan cikin sauk'i gashi yau itace matarshi,hawayen farin ciki takeyi.

Bayan sunyi salloli da duk yadda ma'aurata keyi a ranar farkonsu sai sukayi bacci dan huta gajiyar bikin.Washegari kuwa basu tashi da wuri ba dan sallah ma late sukayi ta,bayan sunyi wanka kowannensu aka kawo musu abinci daga gidajen mijin kamar yadda akeyi na sati guda a al'adar bahaushe.

Haka rayuwar su ta cigaba cikin jin dad'i da kwanciyar hankali,ga nuna so da kulawa ma junansu.

*********
Uganda,
Koda Suhana taji labarin Fahyim yayi aure bata damu ba dama ba sonshi takeyi ba,sannan ita yanzu sabon shafi ta bud'e na rayuwarta.Irin rayuwar da Suby ta fara d'orata akai shita cigaba harma ta bunk'asa shi dan a halinda take ciki yanzu ma bata fasa kula maza ba,yanzu haka ma a gidan wani saurayinta take wanda ya d'auketa tamkar matarshi,yana da kud'i sosae hakan yasa basu samun matsala na expenses.Saidai kuma duk nisan jifa k'asa yake dawowa,sannan duk barinka akawai wanda suka riga ka,Allah ya kyauta.

    hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now