Page 68

58 9 3
                                    

💦 💦💦💦 💦
*LAIFIN WAYE??*
💦💦💦 💦💦💦

_Written by the Aplomb writer: *Hamagee*_

*In devotion to Maman Saif*
💦

Wattpad @ Hama_gee

Page 68 💦💦

    Sai a yanzu ta fahimci cewa Suby ba qawar arziqi bace,tunda a da bata guje taba sai yanzu da taga rayuwarta ta zamo miserable. Amma hakan ya qara koya mata hankali neh,a yanzu tasan irin mutanen da zata ringa huld'a dasu kuma tasan yadda zata bi dasu. Har yau a kullum cikin yima iyayenta addu'a takeyi dan samun rahamar ubangiji. Abinda zai bama mai karatu mamaki kuma islamiya Suhana ta koma a yanzu,dan baffanta yace shi ba ayi mishi zaman banza a gida,indai yarinya ba aure tayi ba to dolenta ta ringa zuwa islamiya,zuwanta islamiyar ba qaramin taimaka mata yake yi ba ta fanni daban-daban.

   Na farko tana samun ilimi ga abinda ya kamata ta sansu da bata sani na,na biyu yana d'ebe mata kewa dan idan tana makarantar ji take kamar kada a tashi ma ta dawo gidan,gashi yanzu Alhamdulillah tana yin sallah. Watarana da safe ta fito zata makarantar tanata sauri kasancewar tayi latti dan saida ta tsaya yin aikin gida kafin ta fita. Tana tafe tana tuntub'e dan bata son tayi latti sosai.

   Horn d'in mota ta jiyo daga bayanta amma bata ko juya ba,saima saurin da ta qara. Shi kuma me motar sai sake horn d'in yakeyi,ganin bazata tsaya ba yasa ya qara gudu yazo gabanta ya tsaya da motar,kafin ta canza hanya ta tafi harya fito daga cikin motar da saurin shi. Kafin ma yayi mata magana tace "lafiya mallam,baka ganin already nayi late neh?". Murmushi yayi kafin yace "haba baiwar Allah,tambayar ki fa kawai zanyi. Gidanku nake son in sani so that anjima in kin dawo saina zo muyi magana dan bai kamata muyi ta anan ba kinga ma kina sauri",da qyar ta yadda tayi mishi kwatancen gidan hakan ma dan taga zai b'ata mata lokaci neh.

     Around 5 na yamma saiga mutumin nan yazo gidansu Suhana,yaro ya aika cikin gidan akan yayi mishi kiranta,kwatance yayi ma yaron dan baima san sunanta kasancewar a hanya suka gamu. Yaron kuwa ya gane wacce aka aike shi ya kira d'in,dama 'yanmata uku ne a gidan,Hadiza da Ummu-khulsum su yaran baffan Suhana neh,sai kuma Suhana da ta cika ta ukun,dukkan su chocolate complexion ne dasu so Suhana ce kad'ai fara shiyasa yaron yasan wacce ake kiran.

    Suhana na zaune ta kammala sharan tsakar gida kenan saiga yaron nan da aka aiko,ita kanma ta manta cewa sunyi wata magana da wani d'azu. Yaron yace "wai ana magana da baquwar gidannan",daga ji sun san da Suhana akeyi. Baffan ne ya daka mata tsawa "baki ji bane ko so kike sai an roqe ki da ki fita?",matarshi tace "inaga". Tashi Suhana tayi da sanyin jiki ta shiga d'aki inda ta d'auko hijabinta ta nufi hanyar fita wajen bada sonta ba.

    A jingine jikin motar shi ta same shi yana jiran fitowar ta,tana fitowa kuwa ya sakar mata murmushi,ita kuwa d'aure fuska tayi kafin ta qarasa. Ce mishi tayi "wai lafiya mallam kake ta bina neh?",yace "lafiya klou". Tace "to fad'i abinda ke tafe da kai inada abinyi". Yadda take masifa qara burgeshi yakeyi,smiling yayi tareda fad'in "idan kin so ma yanzu zan barki ki tafi,matuqar zaki bani abinda nazo nema".

    Da sauri da juyo dan ta matsu ya barta ta shiga gida tace "fad'i menene?",yace "tun d'azu dana ganki naji kin kwanta mun a rai,kinyi daidai da irin macen dana ke son ta zama matata,sannan...",bai qarasa ba ta katse shi "dakata mallam,waye yace maka nayi daidai da irin Matar da kke so? To karka yadda idanunka su rud'i zuciyarka a kaina,ban dace da kai ba",tana kaiwa nan ta tafi ta barshi a gurin cikin kuka dan ya sosa mata inda yake mata qaiqayi ne.

    www.hghausanovelseries.blogspot.com

LAIFIN WAYE?? Where stories live. Discover now