Page Three

2.9K 108 33
                                    

 Ina nan tsaye a wurin kamar wacce aka dasa, sai aikin murmushi nake kamar wata sha-sha-sha. Budurwar ce ta tunkaro wurin da nike a tsaye, ba tare da na ma san da zuwanta ba. Tsawa kawai naji ta daka min, wacce ita ce ta dawo dani hayyacina. "Malama ki jaye kin wani tare wa mutane hanya, da wani uban hijabinki kamar wata matar liman." tace dani. 

Jayewa nayi na bata hanya. Sai ta ja wani dogon tsaki taje ta zauna tana huci. 
Ni dai abun nata dariya ma ya bani, nace "bani nakar zomonba nima....." 

Bata bari ma na k'arasa abunda zan fad'a ba, ta katseni da cewa "Malama ya isheki kinji ko? Idan ba haka ba zan wulak'antaki a wurin nan.” 

Sumui-sumui na ja jikina zan bar wurin. Har na fara tafiya na hangi wani hankerchief a dai dai gun da Khaleed ya tashi. Cikin sauri naje wurin na d'auki handkerchief d'in na k'ara gaba abuna. Zuciyata wasai kamar wacce aka yi wa bushara da gidan Aljanna. Sai wane yage hak'ora nake, kamar tab’ab’b’iya.

Sunan Khaleed kawai nike nanatawa a zuciyata, ina murmushi. Khaleed Khadeejah, Khadeejah Khaleed. Wannan had'in tabbas yayi, abunda nike ta kirari kenan a zuciyata. 

 Sai gab da magrib na isa gida. Ina shiga gida ana tada sallar marib, makewayi kawai na shiga, na fito na d'ora alwala, na wuce d’akina na tada sallah. Bayan na gama sallar ne, nayi azkar d'ina tare da addu'oi, na godewa ubangiji da ya sanar dani sunan dream man d'ina, tare da kuma fatar Allah ya mallakamin shi. 

Mama naje na gaida a d’akinta. Mama dai ta lura da canjin yanayina, dan sai wane washe hak'ora nike ina jan su Fatima da fira. A ranar dai nayi fira a d’akin Mama sosai, har sai da na lura duk bacci suke ji sannan na tashi na wuce nawa d’akin. Hanky da na tsinto na Khaleed ne na d'auko na shak'i daddad'an k'amshinsa na lumshe ido, na rungume handkerchief d'in a k'irjina. A haka bacci b’arawo yayi gaba dani.
*****************************************************************************

Tun daga wannan ranar, na mayar da wannan wurin da naga Khaleed gun zuwana. Amma kamar Khalid d'in ya san dan na ganshi nike zuwa, dan na daina ganinsa sam a wurin. 

Yau ma kamar kowacce rana, na fito da yammaci zuwa gun da na mayar da zuwansa tamkar wajibi. 

Tafe nake ina ta faman sauri, kamar wacce ta makara a makaranta tana gudun duka. Saurin da nake kuwa, duk bai wuce dan ina fatar kawai na samu ganin ko giftawa d'aya ce ta abun k'aunata Khaleed ba. 

Kwatsam! Sai ji nayi kicib’is na ci karo da mutum. D’agowa nayi da niyyar bada hak'uri. Amma wa zan gani? wannan masifaffiyar yarinyar ce ta ranar, kafin ma na iya bud'e baki na bata hak'uri, kawai sai ji nayi ta d'aukeni da mari, sannan ta had'a da fad'ar "sha-sha-sha, sakarya, jaka kawai, kina tafiya amma kamar wata dabba, bloody illiterate {Jahila} I dunno y, but i just hate u {ban san meh yasa ba, kawai ni dai na tsaneki.}” sannan ta ja tsaki ta wuce, ta bar ni a nan tsaye dafe da kunce. 

A gun da nayi a nan naga ita ma ta nufa, bin ta kuwa nayi cikin hanzari, dan kuwa idona ya riga ya rufe, da mari zan ji ko da zagin da ta min? Bana ko ganin gabana, ina k’arasawa gunta na finciko kanta, kawai sai ga acuci mazanta a k'asa, ban damu da wannan ba na kwasheta da mari har guda biyu. 

Kukan kura tayi tayo cikina,tana fad'in "wallahi yau sai na kassaraki ko waye ubanki a garinnan, tinda kika mareni yau sai kin raina kanki.” 

Wani ne da ban ma san da zamansa a gun ba ya taso ya shiga tsakanin mu, yana fad'in "miye kuke yi haka Husnah? kuna abu kamar wasu jahilai." 

Wata murya na koma ji daga bayan mu ana fad'in "wai Sa’id miye haka? ka bar su mana, su kashe kansu idan zasu iya." Sannan aka ja wani dogon tsaki. 

Mai maganar ya taso ya nuna abokiyar fad'ana wacce aka kira da Husnah yace, "ke wai wacce irin mayyace? na sha gayamiki kar ki kuskura ki k'ara bibiyata, amma da yake ke jaka ce, dak'ik'iya, kin kasa fahimta." 

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now