Page Fourty Five

2.6K 120 25
                                    

GEFEN KHALEED

Khaleed kuwa yau da farinciki ya wuni,  tunanin game d’in da suka yi da Ameerah kawai yake through out the day yana murmushi,  aikin da ya tara office for months bai yi ba, yau shi yake ta yi. sallah kawai ke tada shi.  Idan kuma ya ji yunwa, snacks ne abincinshi. Khaleed ba shi ya gama aiki ba sai 9.00 pm. sannan ya kamo hanyar gida.

Ko da ya shigo gidan part d’in Ameerah ya nufa, dan kawai ji yayi yana son ganinta. ko da ya je ya tura k’ofar d’akinta  ya ji gam. Har zai wuce ya ji kamar sautin kuka a cikin d’akin. Ai kuwa  ya dawo ya fara buga k’ofar. 

Ameerah na jin haka ta daka tsalle ta mik’e tsaye, ta koma k’arshen gado. magiya ta fara “dan Allah ku yi hak’uri ku k’yaleni, wallahi Allah ba zan iya ba. Ni zan bar muku gidan ma gabad’aya. Wallahi Allah ni zan k’yale miki mijinki,  ki yi hak’uri ki k’yaleni."

Khaleed  cikin rashin fahimta ya fara magana, “Ameerah zo ki bud’e k’ofar nan.”

kunnenta ya jiyo mata kamar muryar Khaleed, amma kuma gani take yaudararta suke,  sai k’ara takurewa take a bango, tana magiya.

Cikin tashin hankali Khaleed yayi part d’insa da gudu ya nemo spare keys. Dariya ya ji a falon Salmah,  ita da k’awayenta. Take yayi recalling abunda ya ji Ameerah na fad’a,  na cewa su yi hak’uri zata bar gidan, zata bar mata mijinta.  Does that mean su Salmah ne suka tsoratata a kan sai ta bar gidan? Ya tambayi kansa. 

Falon Salmah d’in ya nufa yana huci kamar wani zaki. Su Salmah na ikin firarsu  da dariya, tsaye kawai suka ga mutum a kansu yana huci. Cikin fushi Khaleed yace, “ku dan iyayenku meh kuka yi wa matata?”

A tsorace suka waigoshi, ganin yanayinshi yasa cikin su ya d’uri ruwa. Salmah tunaninta kar dai ace Ameerah ta gayamasa, kuma har ya yarda. Wata tsawar Khaleed ya daka musu yace, “ba magana nike muku ba?”

Wata figaggiyar ta fara magana, “haba angon Salmah, mu meh zamu yiwa matsiyaciyar matarka? Komai ta gaya maka k’arya take.”

Take Khaleed ya kifa mata wani wawan mari, sai da taga stars.  d’ayar ma ta bud’e baki zatayi magana, “haba Khaleed......... “ Bata k’arasa ba ta ji saukar nata marin. tuni Salmah ta fara tsorata.

A fusace Khaleed ya koma cewa, “duk y’ar iskar da ta k’ara shigo min gida, kuma har tayi tinanin tab’a Ameerah, wallahi sai ta raina kanta.” Nuna Salmah yayi da yatsa yace, “wato dan kin ce na saki Ameerah nak’i,  mahaifiyata ta gaya miki ba zata saku ba,  shi yasa kika fito da wata hanyar, dan ki tsoratata ta bar gidan? Toh bari ki ji in gayamiki ba zan saketa ba,  yanzu ma na fara zama da ita, ni aurenki bai k’ara ni da komai ba sai bak’inciki. Baki damu da ni ba, y’an iskan k’awayenki ma sun fini daraja, toh miye naki na kishi? So i' m giving you a last warning, kar ki sake ki k’ara zuwa inda matata take.” Ya juya gun k’awayenta yace, “ku kuma ku fice min daga gida,  kar y’ar iskar da ta k’ara shigo min gida, duk na sake ganin d’ayar ku a gidannan sai na b’allata wallahi.” cikin tsawa ya koma cemusu, “ku fice nace.” da gudu suka fita gidan. Sannan ya ja jikinsa fuu yayi part d’in Ameerah. 

Yana wucewa Salmah ta sauke ajiyar zuciya tace, “ohh, dama  abunda ta gaya mishi kenan?” murmushin mugunta tayi tace, “Khaleed i'm so sorry, ni fushinka bai dameni ba, dan na fi buk’atar matarka a kanka yanzu,  zuwa kusa da ita ma yanzu na fara. sannan ta wuce d’akinta.

Khaleed kuwa zuwa yayi ya fara trying keys d’in d’akinsa yana k’ok’arin bud’e k’ofar d’akin Ameerah. Jin haka ya k’ara firgita Ameerah, kukanta ya tsananta. Ameerah na jin an bud’e k’ofar d’akin ta k’urma wani uban ihu, ta dafe kanta.

Khaleed ma ya firgita, ya rasa meh suka yi mata, ko suka gayamata da ya tsoratata haka. Zuwa yayi ya tab’ata yace, “Khadeejah”.

Ameerah  jin an kirata da sunan Khadeejah yasa ta daure ta bud’e idonta, da suka yi jajir, kan kuka da tashin hankali. Tana ganin Khaleed ne da gudu ta afka jikinsa,  shi ko ya rungumeta. Da tsayuwa ta gagaresu ya zauna da ita kan gado, yana bubbuga bayanta.

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now