Page Twenty Two

1.9K 97 22
                                    

NIGERIA
suna saukowa jirgi suka hango motoci sun zo tarbar su. Ciki kuwa har da Kawu Shehu da iyalansa. suka shiga motoci direct gidansu Khaleed suka wuce.

Suna shiga su Suhailah suka shek’o da gudu suka yo kan Ameerah,  Mom tace “kunga fa kar ku illatamin y’a, bata yi k’wari ba har yanzu.” Aka yi dariya.

Siyama Ameerah ta hango ta rakub’e a baya tace, “Siyama zo mana.”  sai lokacin Siyama ta shek’o da gudu ta rungumeta, siyama har da hawayenta, Ameerah ta goge mata tana fad’in, “baby Siyama ya haka da kuka?”

Siyama tace “ba friends d’ina ne ke cewa kin mutu ba,  wai ba mai k’ara kawo min chocolates.”  dariya kowa yayi, sannan Ameerah ta cemata, “toh ai yanzu gani kin ganni da raina ban mutu ba? Kuma ko yanzu na zo miki da lots of chocolates.” 

Khairi da ke gefe ya daka tsalle yace, “ni fa?” Ameerah tayi dariya tace, “kaima Khairi na zo maka da mai yawa.”  suka fara tsalle, 

sannan Dady yace, “ku wuce ciki mana, kuka zo nan kuka tsaya.”  sannan suka yi cikin gida. 

Suna shiga Dady yace, “ga abincinku nan a kan table.”  da sauri Kausar ta mik’e tana fad’in, “Dad kamar ka san ba muyi breakfast ba.” ta wuce ta fara bud’e flask d’in abinci, tana ganin abincin ta shiga zuba, “wow Dad my favourite pepper chicken, nayi missing home wallahi,  Dad kasan tunda muka je snacks nike ci? Sister inlaw kawai ke cin abinci, wai ita abincin India ya yi mata.” 

Mom tace “hajiya Kausar ba ko gayyata? Sai kace ke kad’ai ke jin yunwa? Ku taso muje kan table.” Kowa ya tashi yayi kan dining table, da yake babbane. Saratu da hanzari tayi kusa da Khaleed ta zauna, tana masa wani kallon yaudara,  shi ko  bai ma san Allah yayi ruwanta ba.

Ameerah tsakiyar su Mom taje ta zauna, Mama tace “mu sa'aninki ne da zaki shige tsakiyarmu? Ki je ki zauna kusa da mijinki.”

Ameerah ta ture baki tana fad’in, “ni wallahi Mama kin daina so na.” 

Mom tace “ki barta kawai sai ta nemeki ta rasa.” Sannan ta juya gun Mama tace, “ai kuma ba kusa da ke kad’ai ta zauna ba, kusa da Mom d’inta ta zauna.”

Mama tace “Allah dai yasa ba ita kad’ai na haifa ba, ko yanzu ga uku  nan a gabana.”  Aka yi dariya. 

Bayan an gama cin abinci ne Mom tace, “tohfa biki nan da sati d’aya, duk mai wani shiri ya je ya fara.” su Siyama suka d’au tafi suna murna.

Haj Asabe ta tab’e baki,  Kawu yace “ai ni na d’auka d’akinta kawai zata wuce.”

Mama tace “nima dai haka nace  suka k’i yarda.”

Mom tace “ai mun riga mun gama shiri, ba za'ayi kashe kud’in banza ba,  baban Khaleed kai kasan  wannan shine bikin aure na farko da zamu fara a gidannan,  kema Maman Ameerah kuma hakane a wurinku,  bai kamata ayishi lami ba wani abu ba,  Bayan an d’aura aure ba dad’i, ai bai kamata a kai amarya ba wani farinciki ba.”

Dady yace hakane ayi bikin kawai,  su Kausar har da kid’a table da spoon dan jin dad’i. aka sa dariya.

Mama  ta mik’e tace, “Suhailah, Fatima,  Khairi, ku tashi mu tafi.”

Mom tace “tin yanzu?”

Mama tace “toh meh muke jira kuma?”

Ameerah ma ta mik’e ta d’auki bags d’inta, Mama tacemata “wai ke ina zaki?”

Ameerah tace,  “ gida mana tare da ku.”

Mama tace “ai yanzu kinga gidanku nan, ba inda zaki bimu.” 

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Donde viven las historias. Descúbrelo ahora