WASHE GARI
Yau ta kama ranar juma'a, kuma ranar da za'a d'aura auren Khaleed da Ameerah. Shiga da fice kawai ake a gidan su Khaleed ana shirye-shiryen d'aura aure, amma Khaleed bai ma da labari, shi ya ajiye tinda Ameerah na asibiti, ba wani zancen d'aura aure, Allah dai ya bata lafiya ya warware mata wannan fake auren, shima ko zai samu nutsuwarsa.
Salim ne ya fito yaci uban ado kamar wani d'an sarki ya sauko parlour. Kausar na ganinsa ta fara shewa tana fad'in "cau-cau, wannan wankan yayi bro, dole ka bani poster." Ta zo suka d'auki hotona.
Ana haka sai ga Mom da Dad sun sauko suma sun ci uban ado. Kausar ta shek'a da gudu ta rungumosu suma, aka yi ta d'aukar pictures.
Salim yace, "Dad uban gayyarfa, shi bai fito ba ne har yanzu? Kar fa ya b'ata mana lokaci, tinda ba shine amaryar ba, bare ya tsaya wani ky'alky'ali, bari na je na fito da shi."
Mom tace, "toh uban zumud'i, kafi ango, ai sai ka je ka fito da shi kam."
Salim ya fito yana dariya ya nufi side d'in Khaleed. K'wank'wasa k'ofa yake, amma Khaleed na kwance a d'aki zazzab'i ya rufe shi yayi masa shiru. Da yaji Salim yak'i barin dukan k'ofar ya shiga masifa, yana fad'in Salimya daina k'wank'wasa masa k'ofa.
Haka yayi daidai da zuwan Sa'id wurin, da kuma fitowar su dad, Sa'id yace "Salim ka je ku tafi da su dad kawai, zan zo da Khaleed d'in." ya juya ya tafi, suka shiga motocinsu suka wuce.
K'ofa Sa'id ya fara duka yana fad'in "buddy ka zo ka bud'e k'ofar mana."
Khaleed haka dole ya taso ya bud'e k'ofar, dan yaji yanzu Sa'id ne ke kw'ank'wasar, yana bud'ewar ya koma ya kwanta.
Sa'id ya je ya tab'ashi yaji zafi zau a jikinsa, tashi yayi ya koma mota ya bud'e jakarsa ta aiki, allura ya d'auko da wasu tabs ya rufe motar ya koma d'akin Khaleed.
Khaleed na kwance ba zato ba tsammani, Allura kawai ya ji an soka masa, sai da ya rik'e gado da k'arfi yace, "aboki amma wallahi ka cika d'an iska, da ka ji min ciwo fa?"
Sa'id yayi dariya yace, "ai nasan kai jarumi ne, tashi ka sha tabs d'innan ka tashi mu tafi."
Khaleed ya karb'i k'wayoyin maganin ya sha, sannan ya ce, "amma ni fa ba inda zani, dan bakada tausayi bakaga yanayin da nike ciki ba ne?"
Sa'id ya ce, "idan ma na barka a haka ba sauk'i zaka ji ba, na san ba aikin da zakayi sai tunanin Salmah, dan haka ba wani dogon excuse, ka tashi kawai ka watsa ruwa mutafi, ka rakani d'aurin aure."
Khaleed ya ce "auren wa kuma?" Sa'id yace, "mai katin da muka raba jiya mana, ai yau ne d'aurin auren."
Khaleed ya ce, "buddy ka tafi kawai ba zan iya zuwa ba."
mik'ar da shi tsaye Sa'id yayi, ya tura shi toilet sannan yace, "na baka 15 minute ka fito, ba barin da zammaka a nan, salon naje na dawo na tarar da kayi mushe a d'aki ko?"
Khaleed yace, " ok you win." ya rufe toilet d'in ya fara wanka.
kafin khaleed ya fito Sa'id ya fito masa da kayansa da ya d'inka masa dan kawai d'aurin aurensa, bayan ya goge jikinsa ne Sa'id ya mik'amasa kayan ya fara sakawa.
Bayan ya saka Sa'id ya mik'o masa babban riga da ta sha aikin sak'i kamar ta wani sarkin musulmi.
Khaleed ya tsaya sororo yana kallon rigar sannan yace, "Sa'id are you mad? Ni ango ne da zan saka wannan kayan?"
Sa'id ya sosa k'eya sannan ya ce, "buddy ai theme d'in d'aurin auren ne haka, nima bakaga ita na saka ba?"
Khaleed ya ce, "but naka kayan are more simpler than mine, ni ai za'a d'auka ko nine angon."
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...