GEFEN KHALEED
Khaleed kuwa k’arfe takwas ya dawo gidan, amma ya lura kamar part d’in Ameerah da duhu, alamun ba kowa. haka kawai ya samu kansa da son zuwa ya duba, ko da yaje ya tura k’ofar kuwa ya jita a rufe.
Ya koma d’akinsa ya kwanta, amma hankalinsa na gun ina Ameerah ta je yau kuma ta yi dare, shi duk da bai yi mata iyaka da fita ba, asali ma ba ruwansa da duk inda ta tafi, amma bai saba ganin ta fita ta yi dare ba. Waya ya d’auko dan ya kirata, sai kuma ya fasa yace, “idan ma na kira ta meh zan ce mata?”
Amma kuma sai zariya yake, baya d’akinsa baya waje, yana kallon gate. Ko da yaga 9.30 ta wuce bai ga Ameerah ba, ya koma d’aki ya d’auko wayarsa dan ya kirata. Ita kuma a lokacin ta shigo gate har ta yi parking.
Khaleed ya fito waje ba tare da ya lura da Ameerah ba ya danna mata call. Ko da Ameerah ta janyo wayarta a bag taga Khaleed ke kiranta, da Mamaki ta da’ga, itama ba tare da ta lura da ya fito wajen ba. Ko da ta d’auki call d’in ta waigo, karaf suka had’a ido. Murmushi ta sakar masa, sannan ta nufi gun da yake a tsaye.
Khaleed kuwa yana nan tsaye kamar wanda aka dasa, ya zuba mata ido kawai tana takunta mai d’aukar hankali, ko da ta k’araso wurinsa sai da ta hure masa ido tace, “yallab’ai kiran meh kake min?’
Basarwa khaleed yayi yace, “ohh dama ke na kira? Sorry ba ke na je kira ba kuskure ne. Amma ina kika je yau kika yi dare haka?”
Ameerah tayi murmushi tace, “gun Mom na je, ko da wani abun ne?”
girgiza mata kai Khaleed yayi yace, “ba komai.” ya wuce d’akinsa, da yake daga part d’insa akwai k’ofar da zata kai ka waje, akwai kuma k’ofar da zata sadaka da main parlour gidan, wanda daga ciki ne kuma zaka iya zuwa part d’in Ameerah da Salmah.
Ameerah Part d’inta itama ta nufa, tana shiga ta ajiye key da hijab, ta shiga toilet dan ta d’an watso ruwa, bayan ta fito ne ta goge jikinta, ta d’an shafa lotion, ta fesa turarenta mai dad’in k’amshi. Tana gamawa sai idonta ya kai ga check d’in da Khaleed ya ajiye mata d’azun, ta kuma tuna da zancen da suka yi da Aunty Fareedah, ta kuma tuna da zancen Mama.
Hakan yasa Ameerah ta mik’e tsaye, cikin kayan da Kausar ta siyo mata ta fara dubawa, duk wanda ta d’auko sai taga ba zata iya sakawa ba.
Can taga wata body hug riga da d’an bud’ad’d’en wuya, taga ita tana da d’an dama ta saka, ta janyo wani skirt 3 quarter ta had’a. Ta taje gashinta, ta d’ora wani k’aramin mayafi, ta d’auki check d’in ta kama hanyar d’akin Khaleed.
Abunda Ameerah bata lura da shi ba shine, bayan d’ameta da rigar ta yi, bayan rigar ma duk a bud’e yake gabad’aya, wanda ya ga bayan kawai zai d’auka ma kamar bakada riga gabad’aya.Khaleed na kwance a d’aki abun duniya ya isheshi, tunanin meh yasa ya fara damuwa da al'amarin Ameerah yanzu yake, kuma meh yasa duk sanda ya ganta bugun zuciyarsa ke k’aruwa? Shi dai ya san mace d’aya yake so, kuma ita ce Salmah, toh amma kuma meh yasa yake jin haka game da Ameerah?
K’wank’wasa k’ofarsa ya ji ana yi, cikin Mamaki wa yake masa nocking yace “waye?”
Ameerah cikin muryarta mai sanyi tace masa itace, shi dai Khaleed Mamaki ya kama shi, dan tin ranar da ta zo d’akinsa yace idan ta k’ara zuwa sai ta samu abunda ta zo nema bata k’ara zuwa ba. Amma dai yace mata ta shigo.
Ameerah ta shigo kanta a k’asa tana taku d’ad’d’aya. Shi ko Khaleed yana kwance, amma yana ganinta ya mik’e zaune ya zuba mata ido.
Kallon da Khaleed ke mata ne, ko meh yasa? kawai sai ga Ameerah ta yi tripping ta zube a k’asa kan tiles. Ai kuwa tasa k’ara tana fad’in, “wayyo Mamata.’ Ta shiga yarfe hannu dan ta ji ciwo a k’afa.
Cikin sauri Khaleed ya zo ya d’auketa cak ya d’ora kan gado, ya fara duba mata k’afar, ita kuma tana y’ar k’ara. Khaleed ya je ya d’auko ointment ya shafa mata a k’afar, sai wani lailayata yake, ita kuma tana kukan shagwab’a.
Khaleed duk ya rikice, sai sannu yake cemata. Sai da ya ji ta daina kukan sannan ya sauke k’afar tata, ya koma ya ajiye ointment inda ya d'auko shi .
Ita kuma Ameerah hotuna ta hango a tsakiyar gadonshi ta juya ta ja jikinta dan ta janyo hotunan, shi kuma daidai lokacin Khaleed ya waigo dan ya dawo gun da take, kicib’is idonsa sai akan bayan Ameerah da yake bud’e. take numfashinsa ya d’auke, ya bi surar jikinta da ido.
fatar Ameerah sumul ba tabo, sai shek’i take. Matsawa yay i wurinta, ya saka hannu ya shafi bayan nata. take ya runtse idonsa wasu abubuwa na masa yawo a kai.
Ita kuma Ameerah a razane ta waigo, ta ga Khaleed a durk’ushe bayanta. Ido ta k’ura masa da Mamaki, shi kuma ya bud’e idonsa da suka fara canja kala, suka shiga kallon junansu.
Da Ameerah ta ji ba zata iya jure kallonsa cikin ido ba, ta sauke idonta. Hannu Khaleed ya d’aga ya fara zagaye fuskarta. take zuciyar Ameerah ta fara bugawa da k’arfi, kamar zata b’allo k’irjinta ta fito. Ta runtse idonta gam. Khaleed kuwa ya koma kan bakinta ya fara zagayewa da d’an yatsansa, hakan yasa Ameerah ta bud’e idonta tana kallonsa, bata ankara ba sai bakin Khaleed ta ji a nata ya fara kissing d’inta.
Chak nufashinta ya tsaya. Shi kuwa Khaleed shan lips d’inta yake kamar ya samu sweet. Ringing d’in wayarsa ne ya dawo da shi hayyacinsa. Dak’yar ya iya janye bakinsa daga na Ameerah, dan ya duba wayar. Salmah ya gani, a take ya d’auka tare da cewa, “hello my love.”
jin hakan yasa Ameerah ta motsa daga sandarewar da ta yi, ta yunk’ura ta tashi , gashi jikinta duk ya mutu, amma haka ta daure ta mik’e tsaye dan ta bashi wuri. Tana taka k’afarta ta saka wata uwar k’ara, ta koma ta zauna.
A razane Khaleed ya yo kanta yana fad’in, “lafiya?” Ya ma manta da waya yake.
Ameerah ta nuna masa k’afarta tana kukan shagwab’a.
Khaleed yace “toh ina zaki je da kika tashi.”
Ameerah tace a fusace, “d’akina mana.”
Chak Khaleed ya d’auketa kamar wata baby, yayi hanyar d’akinta da ita, bai direta ko'ina ba sai kan gado. Yana sauketa ya janyo bargo ya rufeta. Har ya juya zai fita ya waigo kuma, yayi wani kicin-kicin da fuska yace, “meh ma ya kai ki d’akina?”
Check Ameerah ta nuna masa, da duk ta wani duk’unk’uneshi a hannunta. Tsaki Khaleed ya ja sannan yace, “ naki ne, Mom ce tace sai na miki kayan fad’ar kishiya, ni kuma banida lokaci, dan haka ki siye duk abunda kike so, idan kuma bakyason check d’in ki yadda.” ya juya ya ficewarsa
Ameerah ta bi Khaleed da kallon Mamaki, ‘shi wai wannan wai meh yake damunsa ne? Ko har ya manta abunda ya min ne yanzun?’ Juyawa tayi ta rufe idonta dan ta yi bacci. Amma ina, baccin yak’i zuwa, sai abunda ya faru tsakaninta da Khaleed take tariyowa tana faman murmushi, abun kamar a mafarki, wai Khaleed kissed her. Sai wuraren k’arfe 3 sannan ta samu bacci yayi gaba da ita.
A wurin Khaleed ma haka ne, tin da ya je d’aki ya kwanta, sai tinani yake, wai ya aka yi har yayi kissing Ameerah yau? Har da marin kansa yayi yana fad’in, “dole na nisanci yarinyar nan, kafin ta wargaza min duk wani shiri nawa, ga alk’awarin da na yiwa Salmah. Sai ma lokacin ya tina da Salmah ta kirashi fa d’azun, kafin Ameerah ta k’walla k’ara yayi wurgi da wayar, ba tare da ma ya kashe ba.
Da sauri ya janyo wayarsa yasa kiran Salmar, missed call 3 tak’i dauka, nan wai ita fushi ta yi, tinda ta ji k’arar Ameerah a kusa da shi, dat means suna tare. ‘namiji fa munafuk ne, yana nuna mata ba abunda ke tsakaninsa da Ameerah, amma meh yake yi a tare da ita? Har da ajiye call d’inta yana kula matarsa. wallahi tinda Khaleed yayi mata haka akan Ameerah, ranar da duk ta shigo gidan, gobe kenan, zata sanya ya yi waje da ita. ‘
Shi ko Khaleed bai san meyasa ba ma, rashin d’aukar wayar da Salmah bata yiba, bai wani dameshi ba, ajiye wayar yayi, yayi kwanciyarsa. Amma shima sai ya nemi bacci ya rasa, abunda ya faru da shi da Ameerah kawai yake tinani, duk iya k’ok’arinsa na ganin ya hana kansa tinanin ya kasa, daga bisani ya tashi ya fara salloli, a nan kan sallaya bacci yayi gaba da shi.
CITEȘTI
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
DragosteComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...