GIDAN SU AMEERAH
Ameerah bayan ta tashi, zazzab’in da ke tare da ita ya d'an sauka, amma still jikinta ba k'wari. Wanka tayi taje d’akin Mama ta gaida ita. Mama tayi mata ya jiki, Ameerah tace "da sauk'i."Aliyu ne yayi sallama ya shigo, bayan ya gaida Mama ya zauna yace,"Sweet Sis ya jikinki? Jiya yaya Musty da na gani a waje yake gayamin baki da lafiya, ko da na shigo cikin gida kuma kinyi bacci. Kuma bana son na tada ke shiyasa na barki har da safe. Gashi yanzu ma naga kamar kin samu sauk'i."
Mama tace, "toh uban surutu, je kitchen ka d'auko mata breakfast."
Aliyu ya tashi yaje ya d'auko ya kawo min. Bayan na gama Breakfast d'inne nace, "Mama zan shiga school, ina so na dubo sauran results d'ina ne da akace min sun fito, kin san monday zamu fara registration."
Mama ta d'auko d'ari biyu ta mik'omin tace, "ga wannan kiyi maleji, nima kinga su kad'ai ne suka ragemin."
Nace "la Mama wallahi ki barshi ma kawai, ina da sauran kud'in da Yaya Musty ya bani ranar."
Mama tace, "yauwa, dama ina son in tambiyeki, anya Mustafa ba sonki yake ba
kuwa?"Mik'ewa nayi ina murmushi nace, "hmmm Mama, ni dai bai cemin komai ba, shak'uwa ce kawai."
Mama tace, "toh Allah ya zab’a muku abunda yafi zama alkhairi,"
nace "ameen."Zan fita kenan Aliyu ya shigo yace, "Sister ana kiranki a waje."
Hannu na dafe a k'irji nace, "ni kuma wa yake kirana yanzu?"
Aliyu yace, "oho, nima ban sansu ba,"
Mama tace, "toh koma waye kije ki gani mana, sauran idan kin je ki wulak'antasu."
Ni dai nace, "toh na tafi, kuma ni dai daga can zan wuce sai na dawo." Na fita ina tunanin su waye ke nemana yanzu da safe haka.
Ina fitowa idona tar sai kan kyakkyawar fuskarsa. Tsaye nayi na kasa k'arasawa.
Sa’id ne ya nufo ni da fara'arsa, zai yi magana na zagaye shi na wuce abuna.
Cikin sauri Sa’id ya shige gabana yace, "haba Gimbiya, laifin abokina ne ya shafeni? Dan Allah ki tsaya ki saurareni mana."Tsayawa nayi na juyo nace, "toh gani, ka k'ara zuwa da shi ne ya gayamun abunda ya manta?"
Sa’id yace, "ba haka bane Ameerah, hak'uri muka zo mu bayar."
Khaleed ne ya matso yace,"Ameerah i'm sorry." daga fad'ar haka sai yayi shiru kuma. Ko da ganin yanayinsa ma kasan bai saba bada hak'urin ba.
Dariya nayi a zuciyata, amma a zahiri na sha mur nace, "Sa’id ba komai, ni zan wuce, Allah ya kyauta gaba."
Sa’id yayi sauri yace,"tsaya mana ki ji princess, ai ba iya zancen kenan ba."
Na gyara tsayuwa nace," toh meh yayi saura kuma?"
Cewa yayi, "da fatar har yanzu taimakon da zaki yiwa abokina baki canja ra'ayi ba."
Har a raina naji dad'i, amma ai gwanda na nunawa Khaleed nima fa macece ina da aji.
Murmushi nayi nace,"Sa’id ai abunda ya faru jiya yasa na dawo hankalina, na gane shirmen da nayi, so ni na janye wannan zancen kawai."Sa’id yace, "kina nufin kin hak'ura da masoyin naki kenan?"
Nace, "Sa’id i still love him, amma kuma ba zan rugurguza rayuwata saboda shi ba, tinda shi ya kasa yin komai a kai, gwanda na hak'ura kawai na bi umarnin mahaifiyata, dama banida wanda ya fita a duniya.”
Sa’id yace, "wato kin zab’i zama na har abada da wanda ba kyaso kenan?"
Nace, "well atleast ai mutuncina yana nan, kuma shi wanda za’a baiwa ni, tinda yana k'aunata, ai na san zai kula da ni. Kaga nima a sannu zan iya fara son koma waye aka aura min."
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...