Page Nineteen

1.7K 95 19
                                    

Khaleed ya dad'e a nan tsaye sannan ya k'arasa shigowa d'akin, waige-waige ya shiga yi, can ya hango ledar snacks da Drinks d'in da Kausar ta bari, ya zo ya d'iba ya fara turawa baki, kamar wani mayunwaci.

Ita dai Ameerah kallonsa kawai ta ke. a ranta tace 'ita Salmar ta kasa baka abinci ne ko kuma ba abinci ne a Germany?'

Yanda Khaleed ya ke tura bread yana kora lemo, har ma abun ya ba Ameerah dariya, ta rufe bakinta dan kar Khaleed ya lura dariya take masa. Karaf tana a haka suka had'a ido, Khaleed kunya ta kama shi, ya sosa k'eya yace, "abincin Germany ba dad'i ne."

murmushi Ameerah tayi tace, "ai kuwa naga ka kwaso yunwa, na India kam da dad'i kuwa."

Khaleed sai da ya gama kwasar snacks d'insa ya ji yayi nat sannan yae, "ya jikin."

Ameerah tace, "da sauk'i." Sai kuma shiru ne ya biyo baya a d'akin. Sai can Ameerah dan ta katse zaman shirun nasu tace, "ya Salmah d'in?"

ai kuwa Khaleed ya wani washe hak'ora, irin dariyar da bai tab'a yiwa Ameerah ba yace, " lafiyanta k'alau wallahi, i missed that girl da ina da chance da nayi ko 2 weeks ne a Germany, bamu wani samu time sosai ba, idan kika ganta yanzu ta samu hutu ta k'ara kyau, kamar na d'aukota na taho da ita."

Haushi ne ya kama Ameerah, da Mamakin Khaleed a lokaci d'aya, 'wai dama wannan ya iya surutu haka? Meh yasa ma na tambiyeshi ita ne?' take fad'a a zuciryarta, a fusace ta koma cewa a zuciyarta, 'toh meh ya hana ka sakota jaka ka zo da ita?"

Ashe maganar tata ta fito fili bata sani ba, sai dariya kawai taga Khaleed na yi, ta k'ura masa ido, tana Mamakin dariyar tasa, sannan ta ji yace, "kinga kuwa ni ban yi tinanin haka ba fa, amma da na sako abata bag d'in kuwa, kinga da yanzu sai na cire abata na rik'a kallo ko?" ya sake fashewa da dariya.

Ameerah tausayin kanta ta fara yi, ta lura wato shi ko zancen Salmah aka yi masa nishad'i yake shiga. 'wayyo ni Ameerah.' Tace a zuciyarta, take k'walla ta cika mata ido, ta juya kai ta share k'wallar, dan kar Khaleed ya lura. Cikin Sauri tace masa, "yaya Sa'id fa? Dan ta kawar da zancen Salmah.

Waya Khaleed ya zaro ya kira Sa'id d'in ya mik'a mata wayar. Ameerah ta d'aga wayar tace, "hello yaya Sa'id."

cikin farinciki Sa'id yace "princess ke ce kuwa?, Allah mun gode maka, ina nan ina ta zullumi, ashe ke kin warke ko?"

Fira Ameerah ta shiga yi da Sa'id sosai, har ya bata Aunty Fareedah itama suka sha fira, daga k'arshe Fareedah tacemata, "k'awata akwai special tanadi da na yi miki fa, sai kun dawo zan kawo miki, Allah ya baki lafiya." Ameerah tace ameen, daga haka suka yi sallamah, ta bashi wayarshi.

Shiru ne ya biyo baya a d'akin daga haka, har nurse ta shigo ta ba Ameerah magani ta sha ta fita.

Khaleed fita yayi ya dad'e a waje, sai da dare ya tsala sannan ya shigo. Ice cream ya mik'awa Ameerah ta karb'a ta fara sha. Shi kuma ya koma gefe yana shan coffee.

Duk sanda Ameerah ta d'ago kai ta kalleshi sai taga yana murmushi, ta san kuwa duk a kan Salmah ne. Haushi ya ishi Ameerah kamar ta tsala ihu, amma ba dama, a haka har bacci yayi gaba da ita.

da Assubah alarm d'in Khaleed ne ya tada su, suka tashi suka yi sallah, azkar d'inta ta yi ta shafa addu'oi, sannan ta d'auko k'ur'an da Kausar ta bar mata, ta shiga karantawa, cikin y'ar k'aramar muryata da k'ira'arta mai dad'in saurare.

Khaleed shima ya kammala tashi sallar yayi kasak'e yana sauraren karatun Ameerah, har wata nutsuwa ta saukar masa. Sai da gari yayi haske, sannan Ameerah ta rufe k'ur'an ta aje. Ta tashi ta shiga toilet da kayan da Kausar ta bar mata.

wanka ta yo ta canja kaya, wata 3 quarter riga ce da pencil trouser da mayafi, samfurin kayan India ne, kayan sun mata kyau sosai. Ta fito ta kwanta a gadonta, Khaleed kuwa ya bi ta da ido yana kallonta, a ransa kuwa cewa yake, 'ita dai komai nata a nutse take yinsa.' tsaki yayi kuma yace, 'why do i even care?" Karaf suka had'a ido da shi, murmushi ta yi masa, sannan tace, "good morning."

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now