Page Fourty Six

4.7K 203 85
                                    

Ko da Ameerah ta shiga gidan  Kausar na zaune a falo, tana ganin Ameerah ta taso da gudunta tana fad’in, “oyoyo sister inlaw.”  ta rungumeta.

Ameerah tace, “ba wani nan, bayan kin manta da ni? yanzu sai Yaya Sa’id kike yayi.”

Kausar  ta marairaice  tace, “Allah ba haka ba ne, ki yi hak’uri. Wallahi na tsani ganin wannan kishiyar taki ne,  i hate naga broda yana kulata, shiyasa kika ga na rage zuwa gidan.”  Suka je suka zauna Kausar ta koma cewa “ya kishiyar taki?”

Take taga Ameerah ta sha  jinin jikinta, sannan tace “Mom fa?”

Kausar tace “Mom batanan, ni kad’ai ce a gidan yau, Siyama ma na skul. Ya naga kinyi wani zuru-zuru haka?  Har da wani kod’ewa kika yi.” 

Ameerah tace, “Kausar ni ban san ma ta ina zan fara ba.”

Kausar tace, “fara ma ko daga ina ma, I'm getting restless.”

Ameerah tace, “Kausar Salmah is lesbian.” 

K’ulalo ido kausar tayi a tsorace tace, “meh kika ce? Ta ya aka yi kika sani?”

Ameerah ta kwashe duk abunda ya faru jiya tsakaninta da Salmah ta gayawa Kausar.

Mik’ewa Kausar tayi tsaye ta fara yawo a tsakiyar falo ta je ta dawo. Ta sake duban Ameerah tace, “are you sure Ameerah?”

murmushin takaici  Ameerah tayi tace, “toh da k’arya zan miki ne Kausar?”

Kausar tace, “perfect, that’s just great.”

Ameerah tace, “miye wani perfect kuma, kin ji abunda na gayamiki kuwa? That girl is after me.”

Kausar ta ja hannunta tana fad’in, “tashi mu je gidan,  yau k’arshen zamanta da broda ya zo. Yau sai ta bar gidannan i swear.”

dakatar da ita  Ameerah tayi tace, “meh kike tunani Kausar? Kina ga idan kin gayawa Khaleed gaskiya zai yarda ne?”

Kausar tace, “a'ah, ai na san ba zai yarda ba,  zai yarda ne kawai idan ya kamata red handed. Just  trust Ameerah, get the hell up and lets go to that house now. I have a perfect plan. Ki tashi mu tafi for God sake.”

Kausar ta je da gudu d’akinta ta d’auko hiijabinta ta saka, ta ja hannun Ameerah  suka kama hanyar waje, mai makon ta ja motarta  sai kawai ta ja Ameerah suka fita gate.

Ameerah tace “ba ga motarki can ba?”

Kausar tace “no, ba zamu tafi a motata ba,  a adaidaita sahu zamu tafi.”

Ameerah binta kawai dai tayi ba tare da ta san meh Kausar take shiryawa ba. haka aka yi kuwa, adaidaita sahu suka shiga, ya saukesu har a k’ofar gida.

Bayan su sauka Kausar ta lek’a gate taga ba kowa, sannan ta ja Ameerah suna lab’ab’e kamar wasu b’arayi suka shiga ciki. Ameerah ta cemata , “ke dalla sakeni, tinda dai ba sata muka zo ba.”

Kausar  tace, “bana son Salmah ta ganni ne, bare ma ta san ina gidan.”

Ameerah tace, “toh miye, ai  ma batanan ta fita, duba kiga ba motarta a nan.”

Sai lokacin  Kausar ta saketa suka taka suka shige part d’in Ameerah.

suna zaune a d’aki suka ji mota ta shigo gate, suka tashi suka  lek’a .

Salmah ce kuwa,  ta dawo ita kada’i .

Kausar tace “perfect. Ina kayan da na siyo miki ranar?” 

Ameerah tace, “suna wardrop.”

Kausar  ta je ta kwaso kayan ta zube akan gado. Wata  ficiciyar riga ta zab’o shara-shara da mini trouser ta mik’awa Ameerah tace, “ki saka wannan yanzu.”

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now