Page Twelve

1.7K 100 10
                                    

ASIBITI
A asibiti kuwa, Khaleed ne yabi nurse yace jininsa blood group type O+ ne, shi zai iya bawa kowa jini, a d’ibi nasa a sakawa Ameerah. Nurse d’in ta ja shi lab dan a gwada lafiyarsa. Bayan anyi test anga lafiyrsa k’alau ta wuce da shi emergency room, gado aka bashi daidai na Ameerah. Direct connection aka yi da Ameerah ba'a tsaya d’ibar jinin ba, daga jikin Khaleed direct jikin Ameerah yake shiga.

Su Aliyu ne suka iso wurin, Duk wanda ya kallesu ya san  suna cikin tashin hankali. da isowarsu direct Dady lab yace su nufa ayi test.  Nurse d’in da ta sakawa Ameerah jinin Khaleed ce ta fito tace, “ai already an fara sakawa patient d’in jini, sai dai kuma zasu iya zuwa suyi test d’in, incase idan jinin da aka samu bai isa ba.  Dady yace, “wai ina aka samu jini ne?”  Kausar tace, “ Dady gun yaya Khaleed,  kasan jininsa O+  ne zai iya ba kowa jinni.” Mom ta ji dad’i har a ranta abunda Khaleed yayi, sai Mama take ba hak’uri da take ruzgar kuka. Aliyu da Mustafa kuwa sun tafi ayi test d’in jininsu a lab.

Dad ne ya sulale yaje ya samu nurse d’in da ta saka wa Ameerah jinni, akan wai ta cire jinin yaronsa kar ta kashe masa yaro. Nurse tace ai sun san adadin jinin da zasu d’iba, yanda ba zai cutar da Khaleed d’in ba.  Dad yace shi atafau shi sai an cire jinin yaronsa ko yayi k’ararsu, tinda ga y'an uwan patient d’in nan sun zo, su sa bata jinin. Nurse tace toh ya bari taje ta duba results d’in blood test d’in su Aliyu, idan yayi match ta zo ta cire na Khaleed d’in. Dady ya dake akan shi yanzu zata je ta cire, shi samba zai yarda ba, kafin taje ta dawo jinin d’ansa zai k’are. Dole nurse d’in taje ta cire tranfusion d’in daga jikin Khaleed.

Khaleed shi dai yanata Mamaki, dan yaga ba’ dad’e da fara transfusion d’in ba. “har jinin ya isa ne? bayan kuma kumce ta rasa jini da yawa?” yake tambaya. Nurse tace masa, “ana son patient d’in ta d’an huta ne  kad’an, kan a cigaba da saka jinin.” Khaleed yace shikenan ya fita waje.

Blood test d’in da aka yiwa su Aliyu an karb’o result. Jinin Aliyu d’aya suke da na Ameerah, duk A+ ne, aka fara d’iban nashi, na yaya Musty ma O+ ne kamar na Khaleed, shi ma za'a d’ibi nashi gora d’aya a ajiye, incase idan ana buk’atar k’ari.

Ameerah ce ta fara fisge-fisge bayan an cire mata k’arin jinin da aka fara. Doctors suka yo kanta, masifa suka shiga yi akan meh ake jira ba'a fara saka mata jinin ba? Khaleed ya gaya musu abunda nurse ta gaya masa. Take wani Doctor ya kwasheta da mari, wai tana wasa da rayuwar patient, dole su d’auki mataki a kanta. Ita kuwa tasan za'a iya korarta, take ta fad’amusu abunda ya faru ita da Dad.

Mustafa ne ya daka masu tsawa cikin kuka yace, “ enof, Ameerah is fighting 4 her life, kun tsaya kuna rigima, ni muje  a fara saka nawa jinin kawai.”  Mustafa ya basu result d’in test da aka yi masa. Ko da doctr ya duba yaga lafiyrsa k’alau, take yace Mustafa ya kwanta, ya jona jinin daga jikin Musty zuwa na Ameerah.

Khaleed da Mom suka yiwa Dad kallon tuhuma, kame-kame ya shiga yi yace, “son na damu da kai ne bana son wani abun ya sameka, shi yasa nayi haka.” 

Mom tace “amma Alhaji ban tab’a sanin bakada tausayi ba sai a yau. Da Kausar ce a kwance nan zaka hana Khaleed ya bata jini ne? Ko zaka hana mijinta ya bata jini?”

Mama tace “Hajiya ki daina b’ata ranki, Ameerah ta riga ta samu jini, kuma ko jinin Mustafa bai isa ba ga na Aliyu nan, ba wani abu wallahi, tinda har yanzu ba'a d’aura auren ba, har yanzu alhakin kula da Ameerah yana kanmu, kuma Haj. Ba zan tab’a danasanin baku Ameerah ba, dan nasan son da kike mata ko ni iya abunda zan nuna mata kenan.”

Mom ta share k’walla tace, “amma ai mune sanadin faruwar hakan gun Ameerah, dan da Alhaji. bai mak’alawa Khaleed wannan jarababbiyar yarinyar ba, da duk hakan bata faru ba.”

Mama tace, “Haj k’addara ce kawai, ayi hak’uri muyi mata addu’a, shine kawai mafita.”

Kausar ce ta matso tace, “amma Mom ba zamu ky’ale Husnah ba dole muyi maganinta,”

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now