GEFEN AMEERAH
Ameerah ma haka take a wurinta, bacci gagararta yayi sam, duk da ba wai saba kwanciya ta yi tare da Khaleed ba, amma tinanin yana tare da wata macen ya hanata sukuni.
Tun suna fira ita da Kausar, har Kausar ta gaji tayi baccinta ta bar ta. Ita ma sai da aka yi kiran assubah ta tashi, ta tada Kausar suka yi sallah, suka yi azkar d’insu da karatun alk’ur'an, da gari yayi haske sannan suka koma suka kwanta, sai lokacin bacci ya d’auki Ameerah.
Sai wuraren 9.30 Kausar ta farka, Ameerah kuwa bacci take har lokacin. Kausar ta lura jiya ba bacci ta yi ba, dan idonta sun nuna hakan. Shi yasa bata tasheta ba, kitchen ta je ta fara had’a musu breakfast.
K’amshin girkin da Kausar ke yi ne ya tada Salmah. Ita fa yunwa take ji Allah, dan jiya tsabar masifa ko kazar da amare ke ci bata ci ba.
Khaleed ta lura da shi da ya manne mata a jiki, ta fara bubbugashi. Khaleed sai bud’e ido yake yana rufewa, a kan tsabar baccin da ke idonsa.
Salmah ta sauka ta fara zagaye d’akin, ta lura da ledar da aka ajiye gefen gado, cikin sauri ta janyo ledar, gasassun kaji ne manya-manya guda biyu da yourghurt a ciki. Da ta tab’a sai ta ji sun yi sanyi k’alau. Ita fa idan ba abu mai zafi ta ci ba yanzu ba zata gamsu ba.
Zuwa ta yi ta dinga bubbuga Khaleed, shi kam bacci ya masa nauyi, sai bud’e ido yake yana rufewa. Haushi ya isheta ta sauko ta fito falonta, ta bi hanya ta shigo main falo, sai Kausar da ta gani ta fara jera kayan breakfast a table. K’amshi duk ya isheta, gashi ba damar ta yiwa Kausar magana, dan sai hararta Kausar ke yi. Dole ta ja jikinta ta koma d’akinta.
Tana zuwa ta d’ebo ruwa ta kwararawa Khaleed. Ai firgigit ya tashi zaune, kansa ya shiga juya masa kamar ya tsage dan tsabar ciwon da yake masa. Dak’yar ya iya bud’e ido, a kasalance yace “ya aka yi Salmah? da za ki tada ni da ruwan sanyi, duk sanyinnan da ake.”
Salmah ta zumb’ure baki tace, “yunwa nike ji, Allah kasan tin jiya baka bani komai na ci ba.”
Khaleed a k’ufule yace “toh laifin wa? kin bari an yi maganar kirki ne jiyan, bare har na ciyar da ke? Ga kazarki nan ki d’auka ki ci. let me sleep please, jiya kinsa na kasa bacci, ki barni yanzu nayi bacci, gashi kaina ciwo yake yi sosai kamar zai tsage.”
Cikin masifa Salmah tace “toh na bar ka ka yi bacci ni yunwa ta illatani? Ni ba zan iya cin kazar can ba, dan duk ta yi sanyi, ni abu mai zafi nike so yanzu.”
Khaleed yace “toh ki d’auka ki je ki d’umama a micro wave ko a oven mana.”
Salmah tace, “ni fa ban iya shiga kitchen ba, dan ko ruwan zafi bana d’orawa a gida, kuma zamana a germany sai dai nayi order food, ko na je restaurant na ci.”
da Mamaki Khaleed ya kallota yace, “kina nufin kenan komai baki iya girkawa ba? Toh wa zai yi mana girkin kenan?”
Salmah tace, “Kaga, ni ba girki na zo nayi ba, kuma ai hakkinka ne ka ciyar da ni, dan haka ka tashi ka nemo min abun breakfast kawai, dan yunwa nike ji.”
Khaleed haka ya sauko ya fito dole, kansa kamar ya tsage. Ta main parlour ya ji k’amshi ya nufi can. Kausar ya gani tana ta faman jera abinci. Khaleed ya tsaya yana kallonta, ko da ta waigo ta ganshi duk yayi wani iri da shi tace, “good morning bro.”
Khaleed ya karb’a mata, sannan yace “Kausar ko zamu iya samun breakfast d’innan kuwa?”
A yatsine Kausar tace masa, “kai da wa kenan?”
Khaleed yace “ni da Salmah mana.”
Kausar ta tab’e baki tace, “ai itama mace ce, sai ta fito ta girka. Ni abincin mutum biyu na girka.”
ŞİMDİ OKUDUĞUN
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomantizmComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...