Yau ma kamar kullum Ameerah ta saka riga irin wannan da ake d'aurewa a daidai cibi, da wando 3 quarter, ta fito tana buga basket ball da ta gani a wurin.
Khaleed na fitowa ya fara abunda ya saba. Ameerah kuwa ta zo ta rik'o hannunsa. Da Mamaki ya bita da ido. kannemasa ido tayi tace, "the game is boring without a partner, can you play with me please?"
Gyad'a mata kai kawai Khaleed yayi yana kallonta. Ameerah tace "ka daina kallona fa, nima nan na iya games, dan ma ni nayi game captain a skul d'inmu."
Khaleed yace oh really? Gashi kuwa kin samu wani game captain d'in."
Ameerah tace, "oya let start, and see the best player." Suka kuwa fara buga game, Khaleed sai cheating yake yana saka ball, da yake ya fi Ameerah tsayi, kuma ya fita k'arfi, sai janyeta kawai yake yana saka ball.
Gefe Ameerah ta koma tana fushin shagwab'a, Khaleed ya zo yana mata dariya yace, "Allah you are a cheaten, ni ba zan yarda ba."
Khaleed ya janyota yace, "yayi, oya lets start a fair game, yanzu ba zan yi cheating ba, i promised." ya rik'e kunnensa alamun sorry.
Game suka koma suka cigaba da yi, suna ta k'yalk'yala dariya, wannan karon Ameerah ta nuna mai k'warewarta, dan ta sa ball da yawa. Suna cikin game Khaleed ya d'auke ball yayi sama da ita. Ameerah ta dinga tsalle tana son ta kamo k'wallon, amma Khaleed ya k'i bari ta karb'a.
Ameerah ta rasa yanda zata yi, dubara ta fad'o mata, ta shiga zare ido tana kallon gabanta kamar taga wani abun tsoro.
Ai kuwa Khaleed ya juya da sauri, dan ganin meh Ameerah ke zarewa ido. Khaleed na juyawa Ameerah ta karb'e k'wallon ta shek'a da gudu tana ce masa "looser, looser" ai kuwa Khaleed ya bita suka dinga gudu a compound suna dariya.
Hayaniyar Ameerah da Khaleed ce tasa Salmah ta fito. Su kuwa gudunsu kawai suke, sune da gudu har cikin garden, sai a cikin garden d'in ne Khaleed ya rik'o Ameerah ta baya, suka zube a kan grass carpet suna dariya, suna maida numfashi.
Ameerah ta zame daga kan jikinsa ta koma side d'insa, but still hannunsu na a sark'e. kallon juna suka dinga yi ba ko k'yaftawa, kamar masu son su karanto wani abu daga cikin idon junansu.
Tab'i suka ji ana yi a bayansu, wanda shine ya dawo da su daga duniyar da suka tafi. Waigawar da zasuyi suka ga Salmah ce, ta ci uwar kwalliya. cewa tayi "bravo, romeo and juliet zance ne ko laila majnun? Wannan scene yayi kyau fa. Ohhh ina zuwa." sai ta ciro wayarta ta dinga d'aukarsu hotuna a yanda suke.
Khaleed ya taso a fusace yace, "miye haka ? Kuma ina zaki je da kika sha kwalliya haka?"
Salmah tace "meh ya dameka da gun da zan je, tinda har ka samu mai d'ebe maka kewa?"
Khaleed yace, "matata ce, ko kinada matsala da wannan? Har yaushe kika fara kula da al'amarina da har zaki nuna kishinki? Bakyason na samu mai d'ebe min kewa, ke kike ko inkula da al'amurrana? Kuma nace ina zaki je?"
Ameerah da aka bari a zaune haushi kamar ya kasheta. ji take kamar ta shak'e Salmah, dan ta b'ata mata show. Tasowa tayi nace "Malamai ku bani hanya ni zan wuce."
Jaye mata Khaleed yayi ta wuce, tana takunta mai d'aukar hankali.
Daga Khaleed har matar tasa bin Ameerah suka yi da ido, har ta shige part d'inta. sannan suka waigo junansu, ga dukkanin alamu sun ma manta abunda suke fad'a.
Khaleed hararar Salmah kawai yayi, ya ja tsaki ya tafi ya ja motarsa.
Ameerah kuwa ta koma d'aki ta kwanta, haushi duk ya isheta. 'Wannan Salmar ni dai ta isheni Allah, oh God just help me get rid of her please." Take fad'a.
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...