Page Thirty

2K 99 3
                                    

Kai tsaye Khaleed gidansu ya nufa, dan  tunaninsa gwanda ya gayawa iyayensa da wuri kawai.

Yana  shiga kuwa yayi sa'a duk suna a falo zaune. Siyama ta taso da gudu ta rungumeshi tana fad’in, “broda ka kaini inda sister Ameerah”

yace “toh, yanzu zamu tafi kuwa.”  ya duk’a ya gaida iyayensa, suka karb’a.

Shiru ya yi kuma yana sosa k’eya.

Dad ya kalleshi yace “Son fad’i meh kake so, dan na san da magana a bakinka.”

Khaleed yace “dama Dad ba wani abu ba ne, alk’awarin da ka yi min ne, da kace duk abunda nake so kayi alk’awarin zaka bani.”

Dad yayi dariya yace “Son ko rayuwatace zan iya baka, bare wani abun duniya, fadi buk’atarka kawai.”

Khaleed yace “Dad ka san Salmah?”

Dad yace “wacce Salmar?”

Khaleed yace “y’ar gidan abokinka Alhaji Usman Nasir.”

Dad yace “eh na gane, uban ma yana yi min complain kwanan baya,  a kan tinda ta je Germany tak’i dawowa, sun yi iya k’ok’arinsu tak’i  ta dawo,  meh ya faru da ita?” 

Khaleed yace “Dad ta dawo yau, kuma aurenta nike son yi.”

zumbur Mom ta mik’e tsaye a fusace tace, “kana da hankali kuwa Khaleed? Auren naka duk bai yi wata d’aya ba, zaka wani fito da zancen aure? Toh baka isa ba, ni  ban yarda ba sam. Idan akwai abunda Ameerah take yi maka da baka so ka gayamin kawai, ni zan yi mata magana.”

Khaleed yace “Mom ni  ba abunda ta yi min.”

Mom tace “toh wace gulmar ce tasa zaka k’ara aure yanzu?” 

Yace “Mom tun kafin na had’u da Ameerah akwai alk’awarin aure tsakanina da Salmah, dawowar da batayi ba ne, da kuma matsa min da kuka yi da zancen aure, shi yasa na fara neman Ameerah. Toh  yanzu ta dawo, kuma Dadynta ya min maganar auren,  kuma ni ina son na cika alk’awarin da  na d’auka.”

Mom tace “kace Ameerah ta sani?”

Khaleed ya gyad’a mata kai. Mom waya ta d’aga ta sa kiran Ameerah, tana d’agawa Mom tace, “maza-maza ki zo ki same mu gida yanzu.” 

a razane Ameerah ta mik’e  ta cewa Kausar da suke tare, “Kausar Mom nemana take yanzu, ko ta san gaskiya ne? na ji kamar ranta a b’ace yake.” Ta  d’ora hannu a ka,  ta fara kuka ta shiga uku, “yanzu da wanne idon zan kalli Mom? Ta san k’arya muka yi mata Kausar.” 

Kausar ta kwantar mata da hankali kan  ba abunda zai faru sai alkhairi,  tace “Mom tana sonki Ameerah, duk fushin da zata yi na d’an lokaci ne,  ki kwantar da hankalinki.” ta d’auko mata hijabinta ta saka mata, suka nufi gidansu Khaleed da motarta.

Suna  isa k’ofar falo Ameerah ta tsinci muryar Mom tana masifa, “Alhaji kama daina wannan zancen, yarinyar da ta je cikin arna ta zauna? Iyayenta su kansu tafi k’arfinsu, shine shi zai ce ya aura?  Kwata-kwata ni ban amince ba wallahi.” 

jiki a sab’ule Ameerah da Kausar suka yi sallamah suka shiga. Mom na ganin Ameerah  ta janyota ta d’aga kanta tace mata, “wai da amincewarki Khaleed zai auri Salmah?”

cikin sauri Ameerah ta sauke kanta k’asa.

Dad yace “wai wanne irin zance kike ne Aisha? Dan miji yana buk’atar k’ara aure dole sai da amincewar matarsa zai yi?”

Mom tace “ai cewa yayi ta san da zancen,  sannan saboda Allah Alhaji auren nashi duk kwana nawa ne?  Yanzu meh mutane zasu kira mu? Ita ma wannan yarinyar ai sai a yi zargin wani mugun abu take masa, da har ya buk’aci k’ara aure yanzu. Sannan  ni gabad’aya ban nutsu da yarinyar ba.”

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now