Ko da ta koma Khaleed da Sa’id suna fira, Khaleed na cewa, “friend baka san damuwa da kad’aici da na shiga ba da baka tare da ni.”
Sa’id yayi dariya yace, “ai na san baka iya yi sai da ni.”
Khaleed yace “oh, yanzu da nayi ba kai d’in fa?”
Sa’id yace “ai shiyasa naga ka yamutse kamar ba ango ba.”
Ameerah ta yi murmushi tace, “lallai, abu yayi kyau, yau k’ara'in abota a ke.”
Sa’id ya kalleta yace “wai ina ciwon k’afar ne?”
Ameerah tace “ni banida wani ciwon k’afa, inaga dai shi da k’anwarsa ke son ganinka, shi yasa suka had’a plan, wai k’afata ke ciwo dan kawai ka zo su ganka.”
Sa’id yayi dariya yace, “oh really?”
Ameerah tace “eh.”
Khaleed baki bud’e yake kallon Ameerah, ta d’aga masa gira tana dariya. Khaleed yace, “wato mu zaki yi wa sharri ko?”
tace “ba wani sharri, ba gashi kana fad’a masa ka yi kewarsa ba, ka shiga kad’aici da ba shi?”
Sa’id yace “toh ni dai kira min amaryar tawa ma mu zanta mana.”
Ameerah tace, “iye, lallai namiji ba kunya? Wato Yaya Sa’id haka zaka yi wa Antina ko?”
Dariya Sa’id yayi yace, “toh wa zai k’i k’ari ne? Kuma antin taki batada matsala, na san zata amince.”
Khaleed yace “toh shine ni kake fushi da ni d’in, dan na nemi k’arin?”
Sa’id yace “ni ba k’arin aurenka ya dameni ba, yarinyar da ka zama obsessed a kanta ne, its turns out ma batada kunya.”
Khaleed yace “toh ya isheka dai, ai laifi aka yi mata.”
Sa’id yace “laifin meh kuma?”
Khaleed yace “kishiya mana, ai na san ba macen da take son kishiya, sannan kuma honeymoon d’in da muke so mu je mu sake, shi ma cancel , ai dole ta shiga damuwa ko?”
Sa’id yace “ai ita ta yi wasa da damarta. Da lokacin da kake single ta karb’i kayanta, all these will not happened, yanzu kuma dole ta bi layi, dan an rigata.”
Ameerah a k’ufule tacewa Khaleed, “excuse me Mr. Man, waye kishiyarta a nan wurin? Ni ba kishiyarta ba ce, ya kamata ta gane, idan kuma ma haka ne, ai ni aka yi wa kishiyar ba ita ba, dan a bayana ta zo.”
Khaleed ya kalleta yace “lallai yarinyar nan, dama kina da baki ashe?”
Ameerah ta yi murmushi tace, “ai kai ya kamata na tambaya, dan na ga kana k’ok’arin kare matarka, alhalin ita ce mai laifi.”
Khaleed yace “ku dai kuka sani, ni da ba dan wannan k’awayen nata da suka dami mutane ba, da na je na lallab’a abata.”
Ameerah tace, “Malam if you are that romantic, ai k’awayenta ba zasu dameka ba, sai ka je ko a gabansu ka lallashe abar taka.”
Khaleed yace “Madam are you jelous?”
Ameerah tace “jealous of who? Dama ka fad’i hakan ne just to make me jelous?”
Yace “toh na ga kin wani b’ata fuska ne, dan nace zan lallab’a abata.”
Ameerah ta yi dariyar da ta bayyana fararen hak’oranta tace, “kaga Malam, it obvious matarka bata so na, so ni kuma banga dalilin da zai sa na yi farinciki dan ka ambaci sunanta ba. Ni da kai da ita ku je ku yi duk abunda ku ka ga dama, i really don't care. Amma dai a daina min zancenta a falona ehe.”
VOUS LISEZ
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
Roman d'amourComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...