Page Twenty Eight

2K 104 3
                                    

Khaleed na zaune a falo dafe da kansa yana neman mafita.

Saratu ce tayi sallamah ta shigo, shi bai ma ji ba yana zaune yana neman mafita, har ta zo ta zauna daidai saitinsa ta k'ura masa ido kamar mayya.

D'ago kan da Khaleed zai yi sai ganin k'ula-k'ulan idon Saratu yayi a kansa, har ya so ya firgita, amma da yake namiji ne sai ya dake. Ko da ya lura Saratu ce ya ja tsaki sannan yace, "ke gidanku ba'a koya miki sallamah ba ne?"

Saratu ta yi mai wani fari da ido sannan tace, "ai na yi ta rafka sallamah amma kayi nisa a tinani, kyakkyawa irinka bai dace ace kana tinani haka ba, ai sai ya ja maka matsala." tana wani kashe murya, sannan ta koma cewa, "ina fatar dai ba wannan er uwar tawa ke b'ata maka rai ba, kayi hak'uri ai bagidajiya ce, bata san komai ba, ni na ma yi Mamaki da had'ad'd'en guy irinka zai zauna da Ameerah. Dama dai kowa ya sayi rariya ya san zata zub da ruwa."

A fusace Khaleed ya mik'e ya d'aga mata hannu sannan yace, "wa ya baki damar da za kiyi min katsalandan a rayuwa? Wallahi kar ki sake ki k'ara kusantata da wasu k'ananan maganganu, ke nan gani kike wayewan kenan kin zauna kina kushe er uwarki a gaban mijinta?" Tsaki ya ja ya koma cewa, "in dai haka y'an uwa suke toh wallahi basu da amfani." ya wuce d'akinsa ya bar ta nan ta sake baki tana ky'afta ido.

Sai da ya shige sannan tace "dama wannan guy d'in ya iya masifa haka? Amma wallahi ba zan hak'ura da kai ba, sai ka zama nawa very soon."

Dai dai lokacin Kausar da Sa'id suka shigo tare da sallamah. Saratu ce ta karb'a ta wani yage hak'ora.

Sa'id da Kausar suka yi mata kallon ita wannan meh take yi a nan? Sannan Sa'id yace "ina masu gidan ne? Kan Saratu ta yi magana Khaleed ya fito, ya ba Sa'id hannu suka gaisa.

Kausar tace "broda ina sister inlaw ta je ne, muka gan Saratu a nan zaune?"

Tab'e baki Khaleed yayi, sannan ya cewa Saratun "toh dama idan ba gunta kika zo ba gulmar meh ta kawo ki?"

Washe hak'ora Saratu tayi tace, "la wallahi waya na tsaya yi, ina batun tashi ne suka shigo."

Khaleed bai bi ta kanta ba yace, "friend mu je tana d'akinta." Suka wuce d'akin Ameerah.

A kwance suka tarar da ita idonta a rufe. Kausar ta je da sauri ta tab'ata, taji jikinta da zafi zau tace, "broda tana da high fever Allah."

Ameerah ta bud'e idonta da sukayi luhu-luhu suka kumbura kan kuka. Saratu na ganin haka da sauri Saratu taja baya ta dafe k'irji tace, "na shiga uku, dama dukanta ka yi?"

Cikin b'acin rai Khaleed yace "ke ki fice min daga gida, sokuwa kawai."

sumui-sumui Saratu ta kama hanyar ficewa a zuciyarta tana fad'in, 'Allah yasa ma dukanta ya yi, toh yo dama idan ba dukanta yayi ba meh zai sa tayi kuka haka, har idonta su kumbura? that means kenan har ya gaji da ita?" tana fita gate ta kira Haj. Asabe, "Mom kin san meh?"

Asabe tace "sai kin fad'a baby."

Saratu tace, "yanzu na fito gidan matsiyaciyar nan, ko da na je mijin yayi mata dukan tsiya." suka shek'e da dariya

Uwar tace, "yo dama ai bagidajiya ya aura, meh ta iya toh? Ai dole ne ta isheshi."

Saratu tace "kinga kuwa ina da hope, k'wacesa a wurinta ba zai mun wuya ba, Mom ke dai bari sai na dawo akwai magana." ta kashe wayarta.

Hajiya Asabe kuwa ta labartawa Kawu abunda Saratu ta gayamata, sai cewa yayi "toh ni dai ko kasheta zai yi ya jira sai na fanshe abunda na zuba, dan wallahi kwangilar nan da nake nema idan basu bani ita ba zasu ga rashin mutunci, dan ko spoon ba zan bari gidan Ameerah ba, sai na kwashesu tas na saida, kuma in maka su koto a ja min hakkina, dan dama na shirya hakan da lauya na, duk ban samu abunda nike nema ba, zance kawai yarjejeniya muka yi, duk abunda na kashe zasu biyani bayan biki da wata uku, dama har takardun k'arya nasa an shirya min."

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt