Page Ten

2.5K 84 44
                                    

GEFEN KHALEED
Khaleed kuwa direct office ya wuce, amma still ya kasa tab’uka komai.  Wayarsa ya d’auko ya kira Salmah, sai da ya kira kusan sau uku, a na hud’un sannan ta d’auka yace,  “hello babyna, haba baby, tin yaushe nake ta kiranki amma kika k’i d’agawa?  Har text messages d’ina ba wanda kika yi reply.”

Salmah tace,  “I’m really sorry my baby, aiki ne ya mini yawa, kasan aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, daz why kwata-kwata banida sukuni, amma nima kewarka tana damuna.”

Khaleed yace, “to atleast baby ki rik’a replying messages d’ina mana.”

Salma tace, “ok zan yi k’ok’ari, duk ma meh ya rage na dawo gabad’aya na zama taka?” 

wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar Khaleed, sai wani washe hak’ora yake, kai ba kace Khaleed d’in Ameerah ba ne, da baya ko murmushi.

Salma tace masa, “ok i have to go baby, ina da lectures now, talk to you later.”  Bata ma jira abunda zaice ba, ta kashe wayar. Ta bar shi rik’e da waya yana kallo yana murmushi.

Abunda Khaleed bai saniba shine, Salmah ta k’are karatu tin last year, tayi zamanta ne kawai tana aiki. Iyayenta sunyi-sunyi ta dawo tak’i, dan ita Salmah kwata-kwata aure baya gabanta, rayuwar duniya ta sawa gaba kawai.

{Toh nidai Deejah ina biye dasu inga ya wannan Drama zata k’are, shin Khaleed ke wahalar banza ko Ameerah?}

GEFEN AMEERAH
Ameerah basu suka dawo daga rabon i.v  ba, sai da yamma lik’is. Tana shiga gida ana kiran sallah. D’akin Mama ta shiga ta zube kwance.

Mama tace, “ke ya haka? Baki ji ana ta kiraye-kirayen sallah ba ne, kika zo nan kika kwanta?”

Nace “wallahi Mama a gajiye nake, yau mun sha yawo. Kusan duk k’awayenmu na primary da secondry da muka san gidajensu sai da muka tafi.”

Mama tace, “ai  gwanda da kuka je, idan kin tashi rabon naki katin, ba sai kin sha wahalar nemansu ba.”

nace “Allah ni Mama ba zan iya wannan wahalar ba.”

Mama  tace, “ashe kuwa ko tsuntsu ba zaki gani a bikinki ba.” 

Tashi nayi zaune nace, “ni dai Mama ina abincina? yunwa nake ji Allah.” 

tace “yana d’akinki a kula.” 

Tashi nayi har zan fita na juyo nace,  “yauwa, Mama an cire chargen wayoyin kuwa?”

Tace “eh gasu nan a Drawer” nace yauwa bari na gama cin abinci nayi sallah na zo na koya miki yanda ake amfani da wayarki.”

Mama tace “toh.” na fice.

D’aki naje na farma abinci da ci kamar ba gobe, na loda na loda, naci kaji ,nasha zob’o, sai da nayi k’at naji ba space d’in saka wani. Ai kuwa sallah sai a zaune na yi ta, ga gajiya ga k’oshi. Kwantawa nayi har bacci ya kwasheni, kiran sallar isha ya tadani, alwala na sake nayi sallah sannan naje d’akin Mama.

Ina shiganace, “Mama ina wayoyin suke?”

Tace “aje zancen wayoyinnan, ki tashi muje wurin Kawunki.”

nace “wane Kawun Mama?”

Mama tace “ubanki Shehu mana, ko kina da wani Kawun ne bayan shi?”

Nace “Mama wallahi Allah kin san na tsani zuwa gidansa, da wannan tsinanniyar matar tashi, bare ma wannan Saratun mai jin kan tsiya.” 

Mama tace, “Ai kuma ya zama dole ki zo mu tafi, dan duk yanda na so ki, ba zan d’aura miki aure ba, dole dangin ubanki zasu aurar da ke. Dan ke ba shegiya bace.  Gashi iyayen Khaleed mu suke jira su turo magabatansu ayi tambaya.”

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now