Page Twenty One

2K 98 16
                                    

cikin y’ankwanakinnan biyu da suka rage musu India, sun zagaya ko'ina  sun bud’a ido,  sun je cinema kala-kala sunyi kallon sababbin films da suka fito.  Biggest  shopping mall da ke Mumbai kusan duk sai da suka zaga su, shopping malls irinsu:  high street phoenix dake lower parel mumbai,  Inorbit mall dake malad,  infinity mall dake new link road mumbai,  Oberoi mall dake goregan east,  Artria mall dake worli.  Sun jibgo kaya kamar zasu bud’a shop,  su Suhailah da ke gida  kansu an  zab’a musu kaya kala-kala.

Yau ma ta kasance ita ce last day d’insu a India,  wasu shagon jewelries suka je da designer saries,  India akwai designer jewelries both passion jewelries and gold.

Mom duk da sark’ok’in da ta zuba wa Ameerah a lefe, bai hana ta  kwasar mata wasu designer gold ba,  wai wa y’annan na biki ne,  tana so Ameerah ta yi looking like a princess lokacin bikinta. Mama ta yi ta hanata, amma Mom tace ita da ' yarta?  Mama dole ta ja bakinta tayi shiru, tana Mamakin irin wannan soyayya da Mom ke yi wa Ameerah. ita ma Kausar ko kishi batayi sai  zab’a wa Ameerah wasu kalolin sark’ok’i take.

Kausar ce ta jawo hannun Ameerah ta had’e da na Khaleed, wani shock  da Ameerah ta ji har tsakiyar kanta ya sa ta janye hannunta ba shiri.

Kausar ta shige tsakiyarsu ta  ta jasu suka nufi gefen saries. Saries suke ta kallo, masu tsananin  kyau.

Kausar ta dage sai sun zab’i saries d’in, wai su zab’a irin  na celebrities  ne.  can ta janyo Ameerah tana mik’a mata wani sarie tana fad’in, “sis Allah wannan zai yi masifar yi miki kyau,  kinga wannan? Irin shi ne naga Priyanka Chopra ta saka a wani award night da aka yi last year.”

Dariya Ameerah tayi tace, “toh Priyanka kika ce y’ar uwa, ni miye had’ina da ita?”

Kausar  tace “ai sis kin fita kyau da diri, sai dai ta gwada miki hasken fata kawai.” 

Ameerah na dariya tace, “Allah Kausar idan mutum ya d’auki zugarki sai ya fara girman kai.” Ta karb’i sarie d’in tace, “toh  ai sai ki zo ki gwada min yanda zan saka saree d’in.”

wata mata Kausar ta gani y’ar India, itama tana duba saree, ta je ta taho da ita,  wai dan Allah ta nuna musu yanda ake saka saree.  Ita ko matar da murnarta ta amince zata nuna musu.

Wani d’aki da ake canja kaya ta shiga da su,  suka cire kayan da ke jikinsu,  suka saka er k’aramar rigar saree d’in,  amma dama sun bar dogon wandon da suke sanye da shi. Matar ta nuna musu yanda za su laulayi saree d’in, haka akayi kuwa suka laulaya suka lik’e. Kausar ta je ta  warware gashin Ameerah da yake nad’e,  gashin ya zubo,  ta fita ta d’auko bindiya (wannan da ake mak’alawa a goshi) ta d’ora mata. Sannan ta jata suka je gaban madubi.

Ameerah kasa gane kanta tayi, sai gani take kamar ba ita ba ce, dan saree d’in ba k’aramin kyau ya yi musu ba,  idan ka gansu kamar indiyawan, barin ma Kausar da take fara  ce tas, sai ta sade da su. Ita ma Ameerar  ta ma fi wasu indiyawan haske,  dan suma da bak’ar fata a cikin su.

Bayan sun gama ne Kausar ta janyo hannun  su ka fito. Duk wanda ya kallesu sai kaji yace, wow u ar looking very beautiful, su kuma  su ce thanks.

Khaleed Kausar ta hango ta je ta janyo shi. Khaleed  sai k’are mata kallo yake dan ganin irin shigar da tayi. Khaleed bai gama mamakin Kausar ba ya ji ta ce masa,  “broda look there.”

Khaleed ya d’aga kai suka yi ido hud’u da Ameerah, k’ura mata ido yayi k’ur for  quite sometimes, ya kasa d’auke idonsa kanta.

Kausar sai kallo take tana dariya,  shi gogan bai ma san tana yi ba,  sai da ta kirashi “broda,  broda,  ya ka ga matar taka?” 

Basarwa  Khaleed yayi, ya shiga banbami, “wannan wane irin hauka ne? maza ku je ku canja kayan.” 

Kausar bata bi ta tashi ba ta ja ta ja hannun Ameerah tace, “zo mu je wurinsu Mom.” 

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang