Page Thirteen

1.7K 77 11
                                    

WASHE GARI

Da safe Dad ya samu Mom tana shirye shiryen zuwa asibiti yace, "Aisha maganan na zo muyi."

Mom ta zauna, tana saurarensa.

Dad yace, "a ganina dan yarinyar na batada lafiya bai kamata a janye d'aurin auren nan ba."

Mom Mamaki tayi, dan batayi tsammanin wannan maganar ta fito daga bakinshi ba, amma tayi matuk'ar farin ciki da jin haka tace, "hakane Alhaji, a d'aura auren kawai idan yaso, daga baya ayi bikin. Bari ma na kira Son na masa bayani."

Dad yace, "niko na lura yaron nan kamar ba nutsuwa a tare da shi, ki kira wannan abokin nasa kawai ki gayamasa, shi Sa'id d'in sai ya shirya komai, mutanen da suka ji labarin accident d'in ya gayamusu still akwai zancen d'aura aure, wanda bai ji ba ma shikenan."

Haka akayi kuwa, Mom ta kira Sa'id ta masa bayanin yanda Dad yace, sannan tace shikenan idan sun je asibiti ita ta yiwa Maman Ameera bayani ta sanar a gefenta.

Sa'id d da ya tashi d'akin Khaleed ya nufa, ya sameshi yayi wani zugum duk ya wani kod'e yayi rama. S'id ya tab'ashi yace, "aboki wai meh ke faruwa ne?"

Khaleed yace "aboki kafi kowa sanin abunda ke faruwa, Salmah tak'i saurarena, yanzu kuma ga abunda ya faru ga Ameerah, kuma duk ni na ja mata. Amma ko yanzu is not too late, da Allah ya tashi kafad'unta zan warware wannan auren da muka shirya."

Sa'id yace, "lallai kuwa, ni zan tafi, zan je asibiti na duba Ameerah."

Khaleed yace "ka jirani mu tafi a tare." Ya fito suka wuce.

A mota kuwa shiru suka yi kowa da bikin zuciyarsa. Sa'id na fad'i a zuciyarsa, ba sai ya gayawa Khaleed zancen d'aurin aure gobe ba. Dan yaji yana yunk'urin janye auren, idan Ameerah ta warke. Kuma ya tabbata idan Khaleed ya gayawa su Mom gaskia, abun ba zai yi dad'i ba, gwanda ya bar shi kawai har a d'aura auren. Beside ma Salmar da yake yiwa fighting, ya lura ba wani damuwa tayi da shi ba, tun farko da tana sonshi ta ke, ba za ta ce yayi keeping r.Ship d'insu secret ba, duk da yake iyayenta da na Khaleed d'in aminaine, akan wani uzurin karatu. Gwanda Khaleed ya auri Ameerah kawai, dan shi yana zargin Ameerah son Khaleed take, dan idan ba so ba, ba dalilin da zaisa ta iya yi masa haka ba. Duk da yake bai tabbatar da zarginsa ba, amma yana fatar haka ta kasance, gwanda Khaleed kawai ya auri Ameerah.

Sa'id ya katse shirun ya ce, "Khaleed meh yasa ba'a nemeni ba jiya da aka kawo Ameerah asibiti? Duk da kasan ina asibitin.

Khaleed yace, "aboki ni kaina ban sani ba, Mom da dad kawai suka jani asibiti, daz where i found out everything. Beside ma kaida kake likitan mata, meh zaka iyayi, idan an kirakan?"

Sa'id yayi dariya yace, "wa ya gayamaka Gynocologists basu iya komai ba sai aikin mata?" Dariya sukayi da haka suka isa asibitin.

Ko da suka shiga gun da Ameerah take, Mamace da Aliyu da su Suhailah zaune shiru, kowa yayi zugum ba mai magana. Suka duk'a suka gaida Mama. Mama ta karb'a da d'an sakin fuska, suka tambiyi mai jiki? Mama tace, "to alhamdulillah za'ace, amma ba wani canji har yanzu."

Sa'id ya ce, "Doctor ya zo ya dubata?"

Mama tace, "eh yace k'alau take, kuma ana sa ran ta farka a kowanne lokaci."

Mama ta kalli Khaleed taga duk ya zabge, yayi wani zurum da shi ta ce, "Khaleed da fatar ba wannan abun kasa a ranka ba, naga duk yanda ka yamutse jiya kawai?"

Shi dai Khaleed ya sadda kai a k'asa kawai, a ransa kuwa cewa yake, dama damuwar da ke damuna akan hatsarin Ameerah ne kawai.'

Sa'id kuwa sai kallonsa yake, sai yanzu ya k'ara ganin yanda abokin nasa yayi rama yayi duhu, girgiza kai kawai yayi, a ransa yace, d'ole na fito da kai daga wannan jarababbiyar soyayyar, bari ma na tashi na k'arasa rabon katin aure.'

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now