Page Thirty Five

1.9K 101 19
                                    

Tun lokacin da Khaleed ya bar d’akin Ameerah kuwa bai k’ara shigowa ba, sai dai ta ji shigarsa da fitarsa . ga shi gobe d’aurin aure.

Khaleed ya zama wani busy, tinda a da komai da Sa’id yake, amma gashi yanzu shi kad’ai yake komai. Idan ka ganshi duk yayi rama,  kai baka ce ango ba ne.

Ameerah kuwa kullum tana a d’aki zaune.  Sai dai ta ji hayaniya part d’in Salmah ana gyaran d’aki.

Yau ma kamar kullum  zaune a d’aki ta yi wani zugum,  Kausar ce ta turo k’ofa ta shigo,  ga wasu uban ledojin shopping da ta rik’o. Tana zuwa ta zube kayan a kan Ameerah.

Ameerah tace, “ke kuma daga ina haka? Kuma duk wannan kayan mene?”

Kausar tace, “ki duba ki gani mana.” 

ko da Ameerah ta bud’e kaya ne english wears na fitar arziki ,ta kwaso kala-kala,  ga nightys  ma kala kala.

Ameerah ta dubeta tace, “Hajiya kayan aurenki kika fara siye ne ba ko gayyata?”

Wani kallon Kausar ta watsa mata tace, “aurena kuma? Wane mijin kika tanadar min da zan yi aure?”

Ameerah tace “toh ai kece kika k’i, ba wai dan kin rasa masoyan ba.’

Tab’e  baki Kausar  tayi tace, “toh ni dai a bar zancen, kayanki ne.”

Ameerah tace “nawa kuma? Are you kidding me?  Ni zaki kwasowa wannan fitsararrun kayan?”

Kausar  tace “ai mace bata fitsara a gidan mijinta.”

Ameerah tace “haka Aunty Fareedah tace, amma ni dai Allah kunya nike ji.”

Kausar tace “gwanda ki aje kunyar a gefe kuwa, idan har kina son ki samo soyayyar mijinki.”

Ameerah ta girgiza kai ta zauna tana fad’in,  “toh wai ke yaushe zaki fito da mijin mu sha biki?”

Kausar tace “ni dake ai duk kanwar ja ce,  amma ke gwandake kin auri wanda kike son.”

Ameerah ta juyo da Mamaki ta kallota tace,  “meh kike nufi Kausar?”

Kausar tace “abunda kika ji mana.”

Ameerah  tace “wani kike so da baya sonki?”

Kausar ta girgiza kai tace, “No bai ce baya so na ba,  na dai kasa gathering courage ne na gaya masa.”

Ameerah tace “haba Kausar, meh kike tsoro ne? Ai ba namijin da zai k’i mace irin ki.”

Kausar tace “hmmmm, ke dai mu bar zancen kawai.’

Ameerah  tace ‘ba zamu  bar zancen ba,  kawai ki gaya min waye? Kar fa kiyi irin nawa Kausar.”

Kausar  tayi murmushi tace, “ai ni bani da hanyar da zan yi irin taki k’aryar,  dan wanda nike so yana da aurensa, har da y’a y'ansa biyu ma.”

Ameerah dai  duk kanta ya d’aure, tace “Kausar ni fa ban fahimceki ba, please tell me waye. Idan  ina da taimakon da zammiki wallahi zan yi miki.” 

Girgiza mata kai Kausar ta yi tace, “ki tashi ki fara gwada kayan nan kawai.”

Ameerah tace, “toh ni dai ki gaya min mana.”

Kausar tace “ki tashi ki fara gwada kayan, zan gaya miki only after that.” 

Jikin Ameerah na mazari ta tashi tayi toilet dan ta fara canja kayan.

Haka ta yi ta shiga tana gwada kayan Kausar na tafa mata. Inda ta saka ba daidai ba, ta yi mata dariya sannan ta gyara mata. 

Wata  riga ta saka mai bud’ad’d’en wuya, kusan half brest all out. Kuma rigar iya cibi ta tsaya, wandon had’inta kuma short ne iya cinya. Ameerah  na fitowa ta janyo bed sheet ta nad’e jikinta.

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now