GEFEN KHALEED
Khaleed kuwa ko da ya isa ma an d’aura aure, dan dangin amarya tsorata suka yi, kar dai ace Khaleed ya fasa auren Salma ne. Shi yasa dad yace a d’aura auren kawai, Khaleed d’in baya jin dad’i ne ya je asibiti, amma yana zuwa. Shi yasa ko da ya isa an d’aura auren, sai gaisawa da jama'a kawai ya shiga yi, ana d’aukar hotuna.
Ana tashi daga d’aurin auren kuma aka nufi wurin reception. Khaleed duk a takure yake ga rashin sabo, ga kuma rashin wankan da bai yi ba. Ana cikin taro ya silale ya shiga motar wani abokinsa yace ya kaishi gida please.
Shi dai Abokin yana ta Mamaki wannan angon, bayan yazo late gashi yana neman guduwa kuma. Haka dole ya ja ya wuce da shi gida, sai neman ango ake amma ba d’uriyarsa, haka wasu suka gaji suka fara watsewa, ba tare da ganin ango ba, bare ayi zancen d’aukar hotuna.
Direct gida aka wuce da Khaleed, ya ba wani friend d’insa key d’in motarsa, dan ya taimaka ya dawo masa da ita gida, kan cewa shi baya jin dad’i ne, sai sun had’u wurin dinner. Abokin yace masa shikenan, Allah ya sauwak’a, ya ja motarsa ya fice.
Su Ameerah na a d’aki suna ta shan fira, Aunty Fareedah na complain wai Kausar tak’i sakewa da ita suyi fira tin d’azu, sai yanzu da Khadeejah Nasir ta zo ta saki jiki tana fira.
Ameerah dai ta kalli Kausar kawai ta sadda kai k’asa, dan ita tasan dalin rashin sakewar Kausar da ita, a zuciyarta tace, ‘toh dama tana son mijinki ta ya za'ayi ta iya sakewa da ke, toh ranar da kika san gaskia ya zaki kalleta?’
Kausar d’in ce ta mik’e tace, “ni kunga bacci ma nike ji, dan ina bacci Dad ya tasoni, zan je d’ayan d’akin na kwanta.”
kai kawai Ameerah ta gyad’a mata, ta fice.
Bayan Kausar ta fita ne Aunty Fareedah tace, “wai meh yake damun Kausar ne?”Ameerah tace, “ina ga bata jin dad’ine.” Ana haka suka ji shigowan mota. Ameerah ta d’aga labule ta lek’a. Khaleed ta gani an sauke ya wuce part d’insa.
Da Mamaki tace “Aunty Fareedah angon ne fa.”
Aunty Fareedah tace “haka da sauri?”
Ameerah tace, “eh, may be ya yi mantuwa ne, bari na tashi na d’ora mana girki, rana ta fara yi.”
Haka suka tashi suka tayata har suka gama. Bayan sun gama Suka koma d’aki, Ameerah ta je dan ta tada Kausar, amma ta tarar da ita ma chat kawai take, ga alama baccin bai zo ba, kuma ba zata iya sakewa da su ba, tinda Aunty Fareedah wurin.
Ameerah ta zauna bakin gadon da kausar take kai tace, “Kausar ki zo mu yi lunch.”
Kausar tace, “ki bari kawai, idan na tashi zan d’ebi nawa.”
Ameerah tace “Kausar na san matsalarki, amma dole ki daure, idan har ba so kike su zargi wani abun ba, kinga tama fara complain bakya sakewa da ita, yanzu idan suka lura kuma kin ci lunch d’inki daban meh zasu d’auka?” haka dole Kausar ta tashi suka yi lunch d’in a tare gabad’aya.
Har azahar ta yi Ameerah bata ji fitowar Khaleed ba. Haka ta silale tayi d’akinsa dan ta duba ko lafiya. Tana zuwa ta tura k’ofa ta shiga. Khaleed na kwance a gado yana bacci, da Mamaki ta je kusa da shi ta zauna a gefen gado, tana kallon fuskarsa. A zuciyarta take cewa, ‘shi dai ba abunda Allah ya yi masa rowa na kyau, komai nasa masha Allah.
Juyawa Khaleed yayi ya gyara kwanciyarsa. Ameerah ta kai hannunta ta shiga zagaye fuskarsa, haka yasa Khaleed ya bud’e idonsa.
Da sauri ta janye hannunta daga kan fuskarsa. khaleed kur’a mata ido yayi k’ur yana kallonta. Ameerah duk ta rikice, ta shiga kame-kame, “dama……dama….. na….. ga…… naga…. Shigo….. shigowarka ne, kuma naga lokacin sallah ya yi baka fito ba, shine na zo dan na tada kai.”
ESTÁS LEYENDO
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...