Page Sixteen

1.5K 79 9
                                    

INDIA

Kai tsaye babban birnin Mumbai aka sauke su, aka saka Ameerah ambulance sai CITY HOSPITAL, direct ana isa suka karb'eta dama anyi process d'in komai kan su zo, operation room suka kaita, aka turata cikin wata na'ura, domin ayi checking idan bata tare da ko wacce matsala, luckly ba wani brain damage, sai targad'e da aka samu a hannunta, sauran ciwukan kuma dama anyi treating d'insu tin a 9ja.

Doctors suka yi mata abunda ya dace sukayi shifting d'inta zuwa ICU.

Khaleed da Kausar na ganin likitoci sun fito, suka taso suka yi wurinsu, domin jin abunda za su ce kan binciken da suka yi wa Ameerah. Wani Doctor ya gayamusu, patient d'insu bata da wata matsala, wasu k'ananun raunuka ne kawai da ba'ayi treating ba tun a Nigeria, shi yasa har ta shiga comma. Amma yanzu komai zaiyi daidai, zata farfad'o within the next 24 hours, yanzu sunyi shifting d'inta zuwa ICU, nan za'a ajiyeta for observation, amma zasu iya su ganta a yanzu.

Khaleed da Kausar suka wuce d'akin da Ameerah take ciki, Kausar ta zauna kusa da ita, shi kuwa Khaleed bayan ya ganta juyawa kawai yayi zai fita, Kausar tace cikin hanzari, "Yaya Khaleed ina zaka je kuma?"

sai da yayi kamar ba zai tankata ba, sannan dai ya waigota, harara ya fara watso mata sannan yace, "inda kika aikeni mana." Ya juya ya ficewarsa, ya barta da Mamakin inda zai tafi, bayan kuma an sanar da shi matarsa zata iya farkawa kowanne lokaci.

Kai tsaye Khaleed na fita asibiti airport kawai ya wuce, ya fara neman ticket na jirgi zuwa Germany, Cikin sa'a ya samu kuwa, ana kammala komai Khaleed ya keta hazo sai Germany ba tare da wani danasani ba.

A asibiti kuwa, Khaleed bai dad'e da fita ba Kausar ta d'ora kanta a gado bacci yayi gaba da ita, can cikin bacci taji kamar ana tab'a hannunta, cikin hanzari ta bud'e idonta, Ameerah taga tana motsa hannunta, tashi tayi taje kusa da kanta, ta fara girgizata tana fad'in, "Sister inlaw, Sister inlaw....."

Ameerah ta bud'e idonta, amma kuma sai ta fara ihu tana fizge-fizge, tana fad'in, "Husnah please kar ki kasheni, Husnah don't kill me please......."

Kausar ta fita da gudu taje ta kira Doctor, suka shigo cikin gaugawa, nurses suka rik'eta tanata fizge-fizge, wani Doctor take ya d'auko wata allura yayi mata, cikin second da baifi 20 ba ta langab'e, ta koma bacci.

Kausar cikin kuka take tambayar Doctor "Doctor please what is wrong with my sister?"

Doctor yace mata kar ta damu, shock da tsoron da ta ji ne kawai lokacin da ta had'u da accident, amma bata samu damar expressing d'insa ba, toh shi yasa yanzu ta tashi da shi, amma komai zai zama normal da ta farka bacci.

Kausar ta musu godiya suka fice. Kausar ta so ta kira Khaleed ko su Mom amma sim card d'inta baya aiki, kuma ba zata iya fita ta bar Ameerah ba, dan kar ta sake farkawa bata ga kowa ba, da ta fita ta siyo sabon sim card. Zaunawa tayi ta k'urawa Ameerah ido, daga bisani ta fara tofa mata addu'oin da ta iya.

GERMANY

Khaleed kuwa yana sauka k'asar Germany cab ya tara, yace a kai shi near by hotel. Bayan an kai shi ya sauka ya nufi reception, ya je ya kama single room na tsawon kwana biyu. Bayan ya shiga d'akin da aka bashi sauke y'ar k'aramar jakarsa kawai yayi, ya fito da wani k'aramin diary yana duba adreess d'in makarantar Salmah da ta tab'a bashi. Bayan yaga address d'in fitowa ya sake yi ya d'auki cab ya ba mai cab d'in address domin ya kaishi gun. Ba'a sauke Khaleed ko'ina ba sai LUDWIG MAXIMILIAN UNIVERSITY OF MUNICH.

Bayan ya shiga school d'in direct admin block ya wuce ya fara binciken Salmah Usman Nasir, final year student of psychology department. Bayan anyi checking aka ce masa babu meh wannan sunan a final year students.

Khaleed yace a sake dubawa dai, still aka bashi same answer. Ya rok'e matar da take wurin da taimaka ta bashi details na sauran Salmas da ke school d'in. Matar da taga kamar yana cikin damuwa ta taimaka ta bashi details d'in.

Bayan Khaleed ya fito daga admin building, ya shiga yawo different departments yana neman masu suna Salmah, amma duk Salmar da ya gani ba Salmarsa ba ce.

Khaleed yaci uwar wahala, ya gaji ga yunwa ga k'ishi, ya samu wani seat k'ark'ashin wata bishiya ya zauna yana hutawa. Wata budurwa itama y'ar Nigeria da tabi wurin kusan sau 3 tana ganin shi, ta nufi wurinshi. "Excuse me handsome," tace masa.

Khaleed ya d'ago idonsa da suka fara ja ya kalleta. Robar ruwa mai sanyi ta mik'o masa, ba gardama ya karb'a ya kwankwad'e rowan sannan yace mata, "thanks."

tace "tin d'azu nike wucewa tanan ina ganinka, ko akwai taimakon da zan iya yi maka?"

Khaleed ya gaya mata Salmah Usman Nasir yake nema. Yarinyar tace, " toh meh yasa ba zaka kira ta a waya ba?" Yace " I called her several times already, but the number is not going."

tace masa "okay let me see her photo if u have one."

Cikin hanzari Khaleed ya zaro wayarsa don duba photon, yana ta jin haushin kansa, 'shi meh yasa tin d'azu bai yi tunanin nuna picture ba? ai da bai sha wannan wahalar ba.'

Ya miak'awa budurwar photon dan ta gani, tana gani tace masa "ohh u mean (SUN)?"

"SUN?" Khaleed ya k'ara tambaya. Yarinyar tace, "that's what we call her here, ai tayi graduating tin last year, har ma ta fara aiki yanzu. Tin d'azu da ka nuna picture d'inta da ma baka sha wahala ba, saboda kusan kowa ya santa, she is very popular."

Wata figigiyar yarinya ce tazo gunsu ta katse musu zancen da cewa, "ke virus who are u currupting there?"

wacce aka kira da virus tace, " SNACKS this handsome guy here is looking for your SUN."

wacce aka kira da snacks ta yiwa Khaleed kallon sama da k'asa sannan ta ce masa, "Malam lafiya kake neman SUN?"

Virus tace, "Just shutup snacks and help him out, tin d'azu yake nemanta."

tab'e baki snacks tayi sannan tace, "ai ke kin san SUN bata komai da d'a namiji, ba namijin da ya isheta kallo ma." Sannan ta kalli Khaleed tace, "Malam ko ma ka je zaka b'ata lokacin ka ne, dan SUN ba zata saurareka ba."

Khaleed yace, "ni brother d'inta ne, ki taimakeni please." Tace, "shikenan." Ta d'auko biro da takarda ta rubuta masa, adress d'in hotel d'in da Salmah take zama ta bashi." cikin jin dad'i Khaleed yayi musu godiya ya wuce da sauri. A ransa ko yana gode Allah da yasa Salmarsa ta rik'e masa alk'awari, tinda gashi ance bata kula ko wanne namiji.

Cab kawai ya shiga ya nufi hotel d'in da aka bashi address d'insa.
Kai tsaye THE CHARLES HOTEL MUNICH a ka kai Khaleed. Ya sauka ya nufi reception, ya gayawa matar ha zo ne dan ziyarar Salmah Usman Nasir.

Receptionist ta fara bincike, sannan tace masa, su ba su da customer mai wannan sunan. Take ya ciro wayarsa ya nuna mata photo, itama tace "oh you mean SUN? Is she especting your visit now?" Khaleed yace a'ah, matar tace yayi hak'uri domin ta yi musu gargad'i, idan ba ita ta gayamusu tana especting bak'o ba, kada ma su saurareshi.

Khaleed ya shiga magiya, "just help me plz, i came from Nigeria just to meet her." matar taga ya damu ta d'aga waya ta kira d'akin Salmah, tana cemata tanada bak'o kafin ma ta k'arasa zancenta, Salmar tace mata bata son ganin kowa yau, ta kashe wayar.

Khaleed yayi ta magiya akan matar ta taimaka ta bashi number d'akinta, amma matar tace Salmah already gave her orders, su hotel d'insu baya violeting order na customers d'insu. Khaleed da ya gaji da tsayuwa, ya juya zai wuce, matar tace masa ya dawo gobe. Ya rubuta details d'insa yace taba Salmah d'in. ta masa alk'awarin zata bata, sannan ya fice jiki ba k'wari. Khaleed ga yunwa ga gajiya, dan ya k'arar da yini d'aya gun neman Salmah, amma duk da haka bai samu ganinta ba. Cab ya tara yace a kai shi near by restsurant, CHOPAN SCHWABING RESTSURANT aka kai shi, mafi yawancin abincin da suke wurin italian cuisine ne, haka yayi order abincin dole ya ci, dan dad'i ba sai dai dan kar yunwa ta illatashi. Bayan ya gama ya koma hotel d'insa HOTEL METROPOL, ramuwar salloli yayi, ya watsa ruwa sannan ya kwanta yana jiran call daga Salmah, shiru-shiru har baccin wahala ya kwasheshi.

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now