Ita kuma Ameerah ta taso tana ta k’ok’arin bud’e k’ofa ta ji ta gam, gajiya tayi ta koma ta zauna, a ranta tana fad’in, ‘amma Kausar kin iya wulak’anci, ita bata san tsoron yayanta nike yi ba? Duk son da nike masa shakkarsa nike, ko jiya ma dan yana asibiti ne akwai mutane a ko'ina shi yasa ban damu ba, gashi yau wai zamu kwana a daki d’aya.’
Tana nan zaune a wuri d’aya tayi wani zurum ta ji an murd’a k’ofar an shigo. A razane ta mik’e tsaye.
Khaleed ne ya shigo ya doso wurinta,yana zuwa yace, “what was the need to do all that drama outside? Meh kike tunanin zan miki dan an bar mu d’aki d’aya? Ko kin manta kan sharad’in da muka yi aure ne? Ni bana buk’atar komai a wurinki, ko an gayamiki dan wata buk’ata tawa na amince da auren ki?”
Ture baki Ameerah tayi tace, “toh shikenan kawai daga an ce na bi mijina sai na kama hanya na biyoka? Nice uwar son miji ko? Ai ko kan plan mukayi aure ai ni ba saba kwanciya d’aki d’aya nayi da namiji ba.”
Tsaki Khaleed ya ja yace, “toh ai kina iya fita ki kama d’akin kanki.” ya wuce da k’arfi ya fad’a kan gado ya kwanta abunshi, ya bar Ameerah nan a tsaye tana kyafta ido, da ta gaji da tsayuwa ta fara waige-waigen inda zata kwanta, can ta hango wata sofa a gefen d’akin ta je ta kwanta, a ranta tana fad’in, “wannan kamar ba da shi muka gama dariya ba d’azu, yanzu kuma ya rikid’e.’ tsaki ta ja, sai juye-juye take amma bacci yace shi bai san zancen ba.
Haka Ameerah ta wuni a d’akin kan sofa, iyakaci ta tashi idan taga lokacin sallah ya yi, shi kuma Khaleed ficewarsa yayi sai dare ya shigo d’akin, su Mom da Mama ko waigo su basu yi ba. Wani kebab Khaleed ya kawo wa Ameerah, ta karb’a ta ci, ta sha lemo, ta koma kan sofa ta kwanta, amma still bacci yak’i d’aukarta, ga sanyi ya addabeta duk ta duk’unk’une wuri d’aya.
Can cikin dare tana kwance ta ji motsin mutum ya doso wurinta, take tsoro ya kamata ta runtse idonta da k’arfin tsiya.
Cak ta ji an d’auketa, kad’an ya rage ta k’urma ihu. Ashe Khaleed ne ya sunkuceta, bai direta ko ina ba sai kan gado, idon nan nata gam, anan Khaleed ya lura ma ba bacci take ba, dan yanda ta runtse idon ba runtsewar bacci ba ce, dan da k’arfin tsiya ta damk’esu.
Dariya ma abun ya ba Khaleed, shi dai ya jawo bargo ya rufeta ya koma kan sofa yayi kwanciyarsa. Sai lokacin Ameerah ta fara bud’e idonta da kad’an-kad’an, da taga Khaleed ba ya kusa da ita, ta sauke ajiyar zuciya, can ta hango shi kan sofa, murmushi tayi tace a ranta, ‘Khaleed kenan, idan ya tashi kirki ya iya, idan kuma rashin mutunci ne ma ba wanda ya fi shi, kawai dan kar yacemun na kwanta a gadon shi yaje kan sofa ya rage, shine ya jira sai nayi bacci ya ciccib’oni ya kawo kan gado.’ murmishi ta k’ara yi, sannan ta shige bargo ta yi baccinta.
Da assubah ma bayan sun farka Ameerah ta yi y'an karance-karancen da ta saba ta gama, kuma ita dai ta gaji da kwanciya, tashi tayi ta kama hanyar fita, Khaleed ya bi ta da ido kawai, d’akin Kausar ta je ta rik’a buga mata k’ofa. Kausar ta taso tana tsaki ta bud’e k’ofar, tana bud’e k’ofar Ameerah ta ingejeta ta shige ciki. Mitsitstsike ido tayi tana fad’in, “au amaryar broda ya haka tin da safe?” Sai kuma ta shiga dariyar mugunta.
Harara Ameerah ta watsa mata. Kausar na dariya tace, “toh ni meh na yi miki kuma?”
Ameerah a k’ufule tace, “tambayata ma kike?”
Dariya Kausar ta saka yi tace, “toh miye laifi dan mata ta tafi gun mijinta?”
Ameerah tace, “ni dai kar ki k’aramin haka wallahi.”
Kausar tace, “oh hakane? Then tell me do u want to get close to broda or not?”
Ameerah tace, “ina so mana.”
Kausar ta koma cewa, “toh kina nisanta kanki da shi taya za’ayi ki samu kusanci da shi?”
Ameerah tace, “sis ni fa Allah tsoronsa nike sometimes.”
Kausar tace, “gwanda ma ki daina kuwa, dan ni yanzu ma na fara, duk wata hanya da zata sa ku samu kusanci sai na ingizaki kin bi ta. Yanzu ki ma tashi ki koma d’akinku dan ni bacci zan koma.”
Gado ma Ameerah ta je ta haye na kwanta, ta baiwa Kausar baya. Kausar murmushi tayi dole ta rufe d’akin, ta dawo itama ta kwanta.
Da safe bayan kowa ya tashi sun fito, suka gaida su Mom, restsurant d’in da ke had’e da hotel d’in da suka sauka, suka yi breakfast, sannan suka fita yawon bud’a ido.
Sun je amusement parks kala-kala, da ordinary parks ma irinsu, cross maiden, horniman circle gardens, joseph baptista garden da sauransu.
Su na wani park zaune can Mom ta tuna da zuwa asibiti, tace Khaleed da Ameerah su tashi su tafi. bayan an yi wa Ameerah allura ne suka fice, Horniman garden d’in Khaleed yace a maida su. zuwa yayi ya samu wuri yayi zamansa, itama Ameerah dole ta zauna haka sai kallon mutane da ta ke.
Khaleed har da beach sai da yasa aka kaisu, shiga ruwa yayi yana ta wasa, ita kam Ameerah tana nesa tana kallonsa, dan akwaita da tsoron ruwa.
Ba su suka koma ba sai yamma. Kausar na ganinsu ta fara musu tsiya, wai dama neman hanyar guduwa suke yi, shine daga zuwa asibiti suka je shak’atawa. Mom tace, “Kausar kada ki sa musu ido, mutum da matarsa? Idan an gama biki ma ai dole su je honeymoon.”Ameerah a ranta tace, ‘honey wahala dai, wannan idan na yarda muka je honeymoon guduwa Germany zai yi ya bar ni, ina kwance bana motsi ma ya tafi, bare ina k’alau.’
Mama tace ai dama dai an bar zancen bikinnan tinda abun ya zo haka, suna komawa ta wuce gidanta kawai, tinda angama gyara komai dama.”
Mom tace, “wai hakan yayi Ameerah?”
Ameerah Gyad’a kai kawai ta yi. Khaleed kuwa yace, “ai Mom a ma daina zancen wani biki….”
Kafin ya k’ark’are maganarsa Kausar tayi sauri tace, “broda meh kake yiwa sauri ne? Ko munyi bikin ai dole a kai maka matarka.”
Harara Khaleed ya watsa mata ta basar ta koma cewa, “Mom ni fa Allah gwanda a yi bikin nan, komai fa mun shirya dama, kuma kin san kowa cemasa muke biki sai sister inlaw ta warke.”
Mom tace “nima dai haka na gani, gobe ma shopping zamu, dan har Indian night sai an yi.” Kausar ta fara ihun murna.
Mama tace ita dai ta gaji zata shige, Mom ma ta mik’e, Kausar ma ta tashi, janyo hannunta Ameerah kan ta wuce ta zaunar da ita, bayan su Mama sun gama wucewa tace mata, “miye naki na wani dagewa sai an yi biki?”
Kausar ta janye Ameerah gefe dan kar Khaleed ya ji abunda zata fad’a tace, “sis we need this, k’awayen Salmah nake so na turawa hotunan biki, na san dole su tura mata ta gani, kinga idan ta ji haushi may be ma tace ta hak’ura.” Suka saka dariya suka tafe.
Khaleed tsaki ya ja shima ya wuce d’aki. Ameerah kuwa ta bi Kausar, sai da suka kai bakin k’ofar d’akinta, Kausar tayi sauri ta shige da sauri ta turo k’ofa, ta bar Ameerah waje turus.
Dole Ameerah ta mik’e ta wuce d’akin Khaleed. Tana isa ta tura k’ofar ta ji ta a rufe, dole ta shiga k’wank’wasawa. Khaleed da ke ciki yace “waye?”
Haushi Ameerah ta ji dan tasan rainin hankali ne kawai ya san ita ce, har da za ta ce masa ubanka ne, saidai ta daure tacemasa “ni ce.”
Khaleed ya taso ya bud’e k’ofar yana fad’in, “ai na d’auka a d’akin Kausar zaki kwana, dan naga ko d’azun ma can kika je.
Ameerah bata ce masa komai ba ta wuce ciki, amma fuskarta d’auke da murmushi, a zuciyarta take cewa, ‘ashe ya damu da ni, wato d’azun da na fito sai da ya biyoni yaga inda na je kenan.’
Yau ma Khaleed gado ya barwa Ameerah, shi kuma ya kwana kan sofa.
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...