Wayar Khaleed ta yi ringing ya d’auka, har ya kama hanyar d’akinsa. Kausar ce ta gayamasa Ameerah bata ci komai ba tin safe.
Khaleed ya kashe wayar yana tsaki yana fad’in, “ ita ba jaririya ba sai an lallab’ata zata ci abinci?” ya koma jan tsaki. Mota ya koma ya d’auko ledojin kaji da lemo da ya manta da su ya nufi d’akin Ameerah.
Khaleed na tura k’ofar d’akin ya shiga, Ameerah ta tashi tsaye da sauri, ta je ta rungumeshi, ba tare da ta lura da wanda ya shigo ba, dan kanta na a mayafi duk’e. Magana ta fara yi, “shine kika wani shanyani? na d’auka ai kin gudu kin bar ni.” Tana ta faman kuka. Shi ai Khaleed duk ta kashe masa jiki.
Sun dad’e a tsaye a haka, sannan yayi k’arfin hali yace “kukan meh kike yi ne?”
A razane Ameerah ta sakeshi ta yi baya da sauri ta bud’e fuskarta. Sun dad’e suna kallon juna da idonta da suka kad’e suka yi jajir.
Ledojin ya ajiyemata, sannan yace “Kausar ta gayamin baki ci komai ba tin safe, gashinan ki daure kici ko yunwa ta illataki, kuma ni ban san kukan meh kike yi ba. Ni na sha gayamiki ba abunda zammiki, ke da Kausar duk d’aya kuke a wurina."
Ameerah ta zunb’ure baki tace, “ai ba kai aka rabo daga gidanku da iyayenka ba, aka kawoka ka zauna da wani ba.”
tab’e baki Khaleed yayi, sannan yace, “da kin san baki shirya rabuwa da gidan naku ba kika wani shirya plan d’in aure? Shi wancan saurayin naki, da idan ya aureki gidan naku zai barki?”
Ameerah tace “ ai dai kaima dai plan d’in nawa ya taimakeka, dan da yanzu Husnah aka kawo maka.”
tsaki ya ja sannan yace, “ki ci abinci idan zaki ci, idan kuma kukan zakiyi sai kiyita yi.” ya fita ya ja mata k’ofa.
Khaleed na fita Ameerah ta fad’a kan gado ta cigaba da kukanata tana fad’in, “wayyo ni Ameerah , wannan wane irin aure na saka kaina? A wurina aure nayi, amma a wurin mijina kuma is just like a game, which will be over soon. Yunwa ta taso mata har jikinta ya fara rawa kan yunwa. Dole ta janyo ledojin da ya ajiye mata. Kaji ne da lemo, taci ta sha tayi k’at, sannan ta samu nutsuwa. Bayan ta gama ta shiga toilet ta had’o alwala, tayi nafila raka'a biyu ta godiya ga Allah, da addu'an Allah ya d’orata a kan mijinta, kuma ya saka musu albarka. Ta shafa sannan ta je ta rufe d’akinta, ta dawo tayi addu'oin kwanciya ta kwanta.
GEFEN KHALEED
Khaleed ne kwance a d’akinsa yana tunani, wai yau shi aka d’aurawa aure, amma kuma ba da DREAM GIRL d’inshi ba. Waya ya d’auka ya kira Salmah, tana d’agawa tace, “shine zaka ce mun yarinyar da zaka aura ba sonta kake ba?”Khaleed yace “toh meh kika gani ne?”
Salmah tace “Wannan pictures da aka turo min duk wanda ya kallesu ya san happy marriage ka yi, k’awayena sai dariya suke min, wai an kasa ni, ni kuwa ka san ba macen da ta isa tayi takara da ni ko? Bare ma kai da nake ganin na mallaka tintini.” Duk cikin masifa take masa wannan maganganun.
Khaleed yace “haba sweatheart, just calm down mana, ni naki ne tintini har yau har gobe.”
Tsawa Salmah ta daka masa tana fad’in, “kar ka isheni da wannan dad’in bakin naka.”
Shi ma cikin masifa yace, “ Salmah ya kike min tsawa kamar wani yaronki? Yau fa aka kawo min amarya, amma yanzu gashi ina waya dake, idan amaryar tawa ta wani dameni yanda kike tinani, a daren yau har zan iya kiranki?”
Shiru tayi na d’an lokaci sannan tace, “toh shikenan, ina nan dawowa nan bada dad’ewa ba, and that is sooner than you think, kuma idan na dawo take nake so ka saki yarinyar nan, that’s the only way da zaka tabbatar min da cewa da gaske ni kake so, kuma ba wani damuwa da ita kayi ba.”
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...