Page Thirty Three

1.9K 84 22
                                    

GEFEN SU KAWU

Kawu na falo yana kumfan baki da masifa,  “ashe yaron nan baya da mutunci? Suna nufin nayi asarar banza kenan?”

Haj. Asabe tace “ai dama ni sai da na gayamaka,  amma kai mai wayo kace ka san abunda kake.”  

Kawu  yace “wallahi tallahi basu isa suce sun ci bulus ba,  nerar da na kashe ba zan yi asararta ba, sai an biyani.  Ina wayata na kira lawyer na?” Ya janyo wayar zaisa kira,  sai ga maigadi da driver sun rik’o Saratu sun shigo da ita,   baki jini hanci jini, kai duk ya fashe. Kuka take sosai.

Hajiya Asabe ta daka tsalle ta k’urma ihu, “na shiga uku na lalace,  wa ya yi miki wannan aikin Baby?”

Cikin kuka Saratu tace “Khaleed  ne.”  

Kawu na jin haka ya shiga tafa hannu, yana fad’in, “lallai wannan yaro baya da mutunci,  wato duk rashin mutuncin da yayi min  bai isa ba? Sai da ya bi min yarinya ya illata?”

Asabe kuka take tana fad’in, “wallahi Alhaji ba zata sab’u ba, wannan wanne irin bala'i ne? Y’ar tawa guda d’aya zasu kashe min ita? Y’a d’aya tilo Alhaji? Wallahi  ba zan yarda ba."

Alhaji yace “yaron dai muka tab’ashi zamu janyowa kanmu ne,  akan matarsa zamu rama dukan y’ar mu.  Ki zo muje gidan matsiyaciyar.”

Asabe ta  d’auko tab’arya,  ta kwashi Saratu ta zuba mota, suka nufi gidan Ameerah.

Kausar ta sauke Ameerah  ta shiga gida,  ta juya ta wuce gida kenan ta hango su Kawu, sai masifa suke a mota.

Kausar tace “meh ke faruwa kuma?” Ta juya kan motarta ta dawo ta bi bayansu.

 Ameerah na shiga gida ta  zube a kujera, dan duk ta gaji. mutane kawai ta gani a falonta suna dirowa ba ko sallamah.

Ko da ta lura taga hajiya Asabe rik’e da tab’arya . take ta ji gabanta ya fad’i,  jikinta ya d’au b’ari. Cikin rawar murya tace, “kawu lafiya meh ya faru?”

Saratu Kawu ya nuna mata.

Ameerah ta kalleta taga  ta yi jina jina. Take ta k’ara tsorata, cikin rawar murya ta koma cewa, “kawu meh ya  sameta?”

Haj. Asabe ta zo ta kwashe ta da mari sai da ta duk’e. K’arar marin ce ta farkar da Siyama da take bacci  a tsorace , ta taso  ta k’ank’ame Ameerah itama jikinta ya hau rawa.

Kawu yace “d’an iskan mijinki ne yayi mata wannan aikin,  da yake shi tsinanne ne, bayan ya gama ci min mutunci, shine ya zaga ya dakar min y’a. Toh wallahi a kanki zamu rama mata.”   

Asabe tace “Alhaji har sai ka wani tsaya yi mata bayani, ka barni na ci uban tsinanniya kawai.”  

Cikin Ameerah ta yi ta sake kwasheta da mari,  ta d’aga tab’arya za ta rafka mata kenan daidai lokacin Kausar ta shigo, ta k’urma ihu. Suka  waiga dan ganin mai ihu.

Kausar ta zo da gudu ta ja hannun Ameerah, ita ko ta ja Siyama suka yi d’aki, Kausar ta saka mukulli a k’ofar. 

Hajiya Asabe ta shiga  dukan k’ofa tana fad’in,  “wallahi ki fito ma Ameerah,  dan yau sai na fitar da jini a jikinki, yanda Baby ta rasa nata jinin, yau kema sai kin rasa naki."  

Jikin Ameerah kuwa sai b’ari yake, ita da Siyama sai faman kuka suke, Kausar ta d’aga waya ta kira Khaleed tace, “broda ka zo za'ayi kisan kai a gidanka.” Daga haka ta kashe wayar.

Da su Asabe Suka gaji da dukan k’ofa suka wuce. Su Ameerah ma sun d’auka sun hak’ura sun wuce ne, sai can suka fara jin k’arar fashewar glass. Kayan  parlour da na kitchen suka dinga fashewa ,ji kake tamas.

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now