GEFEN KHALEED
Khaleed na fita gidansu asibiti ya nufa gun Sa'id, ko da ya je Sa'id yana theater. ya zauna nan yana jiransa, abun duniya da ya ishe shi ya shiga dukan table yana fad'in, "wai meh ma yasa nayi auren nan? Gashi yanzu zan auri wacce nike so my DREAM GIRL amma gidanmu ba mai taya ni murna, Mom da k'annena gabad'aya basa k'aunarta. Dad ma nasan ya amince nayi auren ne kawai amma ba dan ya so hakan ba, gashi Salmah tace sai na saki Ameerah zata aureni, ga kuma sharud'd'an da Mom ta gindaya min , yanzu ya za'ayi na saki yarinyar nan kuma Mom ta fahimceni? Meh yasa na amince da wannan auren k'aryar?"
A haka Sa'id ya sameshi, lokaci d'aya duk ya yamutse, har wata ramar dole ya yi. Sa'id ya shigo a razane yana fad'in "friend lafiyarka kuwa? Kaga yanda ka koma? Ni da na d'auka na ganka cikin farinciki, dan farincikinka ta dawo maka."
Khaleed a fusace yace "that's how it suppoz to be, amma yanzu komai ya lallace, kuma kaima har da laifinka."
Sa'id yace "laifina kuma?"
Khaleed yace "eh, ai duk da had'in kanka aka yi komai, kai ka k'ara convincing d'ina nayi wannan auren k'aryar, gashi yanzu ya zame min auren jaraba."
Sa'id ya baki bud'e yake kallon Khaleed, sannan yace "halan kai k'aramin yaro ne da zan tilastaka ka yi abunda baka yi niyya ba? Ai kai ka bijirewa zab'in da iyayenka suka maka, kace da ka auri Husnah gwanda ka mutu ba aure, ko ka manta? Toh dama kana da wani abun yin tun da can meh ya hana ka yi? Yanzu shine zaka zo kana blaming d'ina?"
Cikin tsawa Khaleed yace, "ai dama Husnar ka yi convincing d'ina na aurah, da yanzu sakinta ba zai mun wahala ba, amma yanzu wannan yarinyar a kanta Mom wai bazata yafemun ba idan na wulak'antata, ko na ci zarafinta. So tell me ta ya za'ayi na saketa yanzu, ba tare da Mom ta yi fushi da ni ba? Gashi Salmah tace ba zata aureni ba sai na saki Ameerah." ya cakumi wuyan Sa'id yace, "yanzu sai ka gayamin yanda zan yi?"
Sa'id dai sai kallon ikon Allah yake, Mamaki ma yamasa yawa, tureshi yayi daga cakumar da ya masa, shima a fusace yace, "wannan matsiyaciyar Salmar dai ta haukataka, ni ban san meh ka gani a tare da wannan jarababbiyar yarinyar ba, yarinya da zuwanta zata rabaka da kowa naka? Ni wallahi da zaka bi shawarata da ka hak'ura da auren wannan matsiyaciyar."
Karaf Khaleed ya wanke Sa'id da mari, sannan yace "kadda ka sake ka k'ara zagin Salmah, kuma ba zan hak'ura da ita ba."
Sa'id rik'e da kuncensa, cikin tsananin mamaki da b'acin rai yacewa Khaleed "ka fice min daga office, kuma kadda ka k'ara zuwa min office, ka je kayi abunda kaga dama, ina ga yanzu Salmah tafi uwarka daraja, shiyasa har kake neman mafita akan abunda zakayi, tsakanin umarnin mahaifiyarka da na budurwarka."
Da yaga Khaleed d'in yak'i ya d'aga ya koma cewa "ka fice min daga office." cikin tsawa.
Khaleed ya yi fuu ya yi waje yana huci.
Khaleed na zuwa mota ya fara buga kansa a sitarin mota yana fad'in, "why? Why? Meh yasa na yi haka?" Sannan ya ja motarsa ya nufi office d'insa cikin tashin hankali.
yana zuwa ya zube a kujera, ya d'ora kansa kan desk, kansa sai juya masa yake. Wayarsa ce ta fara ringing ya d'auka. Salmah ce, cikin kissa take magana, "babyna na jika shiru i'm missing you."
Khaleed wani wahalallen murmushi yayi, sannan yace "i'm missing you too my sweatheart."
tace "baby ina fatar dai parent d'inka sun amince."
yace "eh sun amince, kar ki damu, the marriage is still on."
dariya tayi wacce ta k'ara masa kasala, sannantace "i'm so very happy my baby, toh matarka fa?"
take wani gumi ya keto masa yace "bari zan zo na sameki mu yi maganar yanzu." ya kashe wayar, yana tinanin ya zai kwashe da Salmah, idan ya gayamata Ameerah ba zata saku ba.
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...