GIDAN SU KHALEED
Khaleed ne kwance a d’akinsa, abun duniya duk ya ishe shi, kiran sallar da yaji ne yasa ya mik'e ya shiga toilet d'in da yake d’akinsa yayi alwala, bayan ya fito ya wuce masallacin da ke k'ofar gidan su yayi sallah, bai dawo ba sai da aka yi sallar isha.Yana dawo d’akinsa ya kwanta. Kwanciyar sa ke da wuya, sai ga k'anensa Salim ya shigo yace, "Yaya Khaleed wai ka zo inji Dady da mummy."
Gaban Khaleed ne ya shiga dukan uku-uku, a ransa yace, yau fa ake yin ta. Amma a zahiri yacewa k' anen nasa "ka je kace ina zuwa." Sannan ya tashi ya fice.
Khaleed d'an gidan Alhaji muhammad Khalifa ne, wani shahararren mai kud'i kuma babban d'an siyasa a nan garin Sokoto.
Alhaji M. Khalifa mutum ne mai son nuna isa da girma, shi talaka bai da wani muhimmanci a rayuwar shi, kuma mai tsatstsauran ra'ayi ne a kan duk wani abu da yasa a gaba zai aiwatar.
Hajiya Aisha ita ce mahaifiyar Khaleed. mata d'aya tilo a wurin Alhaji muhammad Khaleefah. Hajiya Aisha macece mai son jama'a, abun hannunta bai tsone mata ido ba, kuma talaka a duk inda yake bata rainashi. y’ay’ansu hud'u ne, Khaleed ne babba sai, Kausar mai binsa, sai Salim da kuma autarsu Siyama.
Zaune suke a fakeken falonsu mai kama da palace, da y’ay’ansu da suke Zaune kewaye da su suna fira cikin nishad'i. sallamar da Khaleed yayi ne ta katsesu, aka karb’a masa a cikin fara'a ya shigo.
Khaleed ya duk'a ya gaida iyayensa.
Alhaji M. Khaleefah ne ya fara magana, "ba sai mun gayamaka dalilin kiranka ba, ka riga da kasan dalilin, dan haka muna jinka ka gaya mana miye decision d'inka?"Khaleed ya d'ago kai yacewa su Salim "ku tashi ku bawa mutane wuri, kun kafe mutane da ido kamar wasu sa'aninku."
Hajiya Aisha tayi dariya tace, "kada ko korarmun yara, ai suma suna so suji amsar yayansu, dan sun matsu su sha biki, kayi magana Malam kai muke saurare."
Khaleed ne harda wani sunkuyar da kai k'asa, cikin wata kasalalliyar muryar sa mai dad'in sauraro ya fara magana, "dama Dady so nike dan Allah dan darajar iyeyenku ku k'aramin lokaci ko zuwa next year ne dan........."
Alhaji Khalifa ne ya dakatar da shi da cewa, "Khaleed wai kai yaushe zaka girma ne? ka duba kaga duk sa'aninka sunyi aure, har kake fad'ar a wani k'ara maka time, ko Sa’id da kuke tare y’ay’ansa nawa?"
Hajiya Aisha tace, "biyu Alhaji, shi wannan inaga baya ko damunsa, ko wai bakada lafiya ne Son?"
Alhaji yace, "lafiyarsa k'alau, shashanci ne kawai. Amma idan ma rashin lafiyar ce ai zamu sani nan bada dad'ewa ba. Mik'o min wayata a d’aki Kausar, na kira Deputy Governor na gaya masa ya shirya zuwa next week a d'aura masa aure da Husnah.”
Ai zumbur Khaleed ya mik'e kamar wanda kunama ta harba, yayi wurin Dady ya rik'e masa hannu, "Dady dan Allah kayi hak'uri, wallahi na samu wacce nike so, dama karatu ne bata kammala ba, shi yasa na so na k'ara mata lokaci, amma yanzu na amince zanyi auren."
Cikin fara'a Hajiya Aisha ta taso tace, "Khaleed dama in banda shirmeh, wa ya gayamaka aure na hana karatu ne?"
Dady yace, "to a ina yarinyar take?"
Khaleed yace, "a nan garin take Dady."
Kai tsaye Dady yace," y’ar gidan waye? Waye ubanta a garinnan?"
Khaleed yayi wani jim bai ce komai ba, saida Dady ya maimaita masa, "nace y’ar gidan waye? kayi shiru."
Khaleed yace, "Dady ba y’ar gidan kowa ba ce."
Dady yace, "kana nufin y’ar talakawa ka d'auko kenan?"
Hajiya Aisha tayi sauri ta matso tace, "haba Alhaji, ita y’ar talakawa ba mutum ba ce?"
YOU ARE READING
KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com
RomanceComplete novel is on okadabooks.com Highest ranking #1st in romance lots of times. This is a journey of a Hausa Girl Love Story. A girl fall in love with a man Who never notice her, who she doesn't even know his name, talkless of anything about him...