Page Thirty Four

1.9K 96 2
                                    

Su kuma su Ameerah haka suka isa gidan suka zube a falo. Mom da Dad sai tsinewa Kawu da matarsa suke.

Mom ke cewa, “Da Allah ya baka uba irin wannan ai gwanda rashinsa.”

Ameerah  ta duk’a k’asa tana kuka tana bawa Dad da Mom hak’uri.

Dad  yace “ba laifinki ba ne Ameerah, kema kiyi hak’uri.”

Mom kuwa tace “ai mai laifi duk bai wuce wannan ba.”  ta nuna Khaleed “Duk abunda yarinyar nan ta maka  bai ci ka ma ta wannan dukan ba,  yanzu da ba dan Allah yasa Kausar na gidan ba,  da sai dai mu tarar anyi aika-aika, dan na tabbata ko kasheta zasu iya yi.  Toh wallahi tun wuri ka canja hali,  ka iya controling zuciyarka, idan ka yi fushi. Yanzu da sun kashe maka matar  murna zaka yi ko? Lallai hakane, dan dama wata sabuwa zaka auro, shi yasa baka damu da wannan d’in ba.” 

Khaleed yace “Mom ya zaki ce haka? Dan zan yi aure ba shi zai sa na so a kashe Ameerah ba. Kawai dai ni ban san zasu yi haka ba ne.”

Dad yace “yanzu dai wannan surutun bayada wata fa'idah,  ku gode Allah abun ya tsaya iya nan,  ku kwashe kayanku kuje d’akin bak’i, dama a gyare yake.”

Ameerah tace ita a barta kawai ta zauna d’akin Kausar.

Kausar ta yi maza tace, “caf, ai ni na gaya miki bana sharing room.”  

Siyama tace “toh ni su zauna a nawa mana.” 

Mom tace “Siyama ki bari kawai zasu zauna a guest room, kafin a gama gyara gidansu. Ku tashi ku kai kayan.” Ta cewa Khaleed “kaima ka bi su ka tayasu.”

Haka suka tashi suka nufi d’akin, suna sauke kayan Kausar ta fita ta bar su.

Ameerah  ta fara gyara kayan, shi kuma Khaleed yana a tsaye, haushi duk ya ishe shi, a kan Saratu yanzu ya zo zai yi confining d’aki d’aya da Ameerah,  gashi ba damar ya koma d’akinsa da yake kafin yayi aure Mom zata sa mishi ido. Ya ja tsaki, Ameerah ta waigo ta kalleshi, ya sosa k’eya yace, “hope dai ba su ji miki ciwo ba?”

Ameerah ta gyad’a mishi kai kawai. Ya koma cewa, “kiyi hak’uri ban san haka zata faru ba.”

Ameerah tace “ba komai, haka Allah ya so.”

Khaleed  ya fara tayata gyaran kayan kenan wayarsa ta yi ringing. ya d’auka yana fad’in, “hello my love,  I'm sorry wallahi na fito zan kai bugun katin, wata y’ar rigima ta taso a gida,  shine na dawo,  amma yanzu zan je wurin. No kar ki damu ba wata babbar matsala ba ce,  everything is normal now.  Zan miki bayani idan na zo anjima.  Bye missed u." Ya  kashe wayar,  sannan ya fita.

Wasu zafafan hawayene suka zubo wa Ameerah tana fad’in, “ni dai wannan Saratu ta ja min masifa, zama d’aki d’aya da Khaleed ai jinina ne zai hau,  dan waya zai rik’a yi da budurwarsa ko a gabana,  ba zai damu ba, ni abun zai dama. Gaskiya skul zan koma, daga can na wuce gidan Aunty Fareedah. Amma kuma Mom zata saka mana ido fa,  ya zan yi? Toh ai shima na san ba wuni zai rik’a yi a gidan ba,  zai je shirye-shiryen bikin sa ne.”

GEFEN KHALEED

Khaleed bayan ya fito Mom ta tareshi tace, “ina zuwa Son? Ai baku isa gama gyara kayan ba ko?” 

Khaleed yace “Mom na manto wasu kayan a d’akina ne,  zan je na d’auko."

Mom tace masa a dawo lafiya,  ita kuma ta je d’akin Ameerah tana tayata gyara kayan.

Khaleed kuwa yana fita wurin kai bugun invitation ya wuce. Duk ya yi missing Sa’id, dan da yanzu tare suke harkokinsu. Ya san  idan ma ya je bashi hak’uri yanzu ba saurarensa zai yi ba,  zai dai hak’ura har ya k’ara hucewa, sai yaje ya bashi hak’urin.

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Donde viven las historias. Descúbrelo ahora