Page Twenty Five

1.7K 85 4
                                    

Ameerah na fita Khaleed ya ky'alky'ale da dariya yace, "wai meh yasa nake son tsorata yarinyar nan ne?" Wata zuciyar tacemasa 'dan kaga tana tsoronka ne.' wata zuciyar kuma tace 'birgeka take yi.' Khaleed ya girgiza kansa yace, "No kai no that can't be, but kawai i know its fun to watch her getting scared." Dariya ya sake yi sannan ya fita d'akin.

Ameerah na fita tayi falo, ta samu Kausar zaune ta afka mata, tana fad'in, "wallahi ke muguwa ce, meh yasa kika bar ni ni kad'ai?

Kausar tace "toh mutum zai gana da matarsa sai na tsareku da ido? Toh kuma ai naga kun dad'e ne, watsup?" ta d'aga mata gira.

Ameerah tace "kud'i muka tsaya k'irga."

Kausar ta fashe da dariya tace, "toh kud'in nawa ne?"

Ameerah tace bamu gama ba, "amma ba zasu fi dubu d'ari biyar ba."

Kausar fara dariya, sai da tayi son ranta sannan tace, "ke fa 7million ne da y'an canji."

Ameerah ta gwale ido tace, "7million? You are kidding right?"

Daidai lokacin Khaleed ya fito ya haye dining ya fara cin abincinsa. Satar kallonsa Ameerah ta shiga yi, a ranta tace, "shi dai baya wasa da cikinsa.'

Had'a ido suka yi yace "ke ba yunwa kikace min kina ji ba? Idan kika biyewa wannar uwar sanaben, sai yunwa ta illataki."

Kausar tace "ni broda? dama ka zo ka bata a baki, da zaka fi birgeni."

Wata harara Khaleed ya banko mata, sannan yace, "ke ki taso kici abinci kinji."

Ameerah ta mik'e tayi kan table. Har Ameerah ta zuba abinci zata fara ci aka yi sallamah, Saudah ce da Khadeejah Nasir . Ta tashi ta shek'a da gudu ta rungumosu suka zube a kujera. Ameerah tace, "ku kuma kun kyauta." Ba su bi tata ba, suka shiga gaisawa da Khaleed, yana karb'a musu da sakin fuska. Ameerah tace, "ku tashi mu tafi d'aki."

Khaleed yace "abincin da kika zuba fa, wa zai ci miki shi?.

Saudah tace "kai dai ango kace ta barka kai kad'ai a kan table, ki je ki tayashi." ta turata su kuma suka koma suka zauna.

Ameerah ta koma kan dining ta fara cin abincin kenan, aka koma sallamah. Fareedah ce da Sa'id suka shigo, ta yunk'ura ta mik'e kenan ta rungumo Aunty Fareedah Khaleed ya take mata k'afa. Ba shiri ta koma ta zauna tana yarfe k'afa.

Aunty Fareedah ta lura ashe tace "ango idan har baka son amaryar taka ta mik'e ta barka, shine sai ka wani take mata k'afa?" Suka yi dariya.

Khaleed yace "Aunty Fareedah ai ba haka ba ne, tin d'azu ta d'ebi abinci amma tak'i zaunawa ta ci, kuma yunwa take ji.

Fareedah tayi dariya tace, "wato Khaleed yau na zama antinka ko? Tinda matarka na kirana Anty."

Sa'id yace "idan ta kasa cin abincin ba sai kai ka bata da kanka ba?" Wata harara Khaleed ya watso masa, ya basar.

Su Khadeejah kuwa suka shiga yi masa ihu, akan ya ba Ameerah abincin a baki su gani. Dole tasa Khaleed ya d'auki spoon ya fara ba Ameerah abincin, su kuma suka shiga tafi. Ameerah dai duk kunya ta kamata, sai wani nok'ewa take. Da ta k'oshi ta shiga nunawa Khaleed ta k'oshi, amma dan mugunta yak'i barin bata abincin, sai zunguramata yake, da taji cikinta na batun fashewa tana yunk'urin amai, ta mik'e tsaye.

Shima mik'ewar yayi yana dariyar mugunta. winking yayi mata ya sauka abinshi.

Ameerah kuwa kamar tayi kuka. ciki yayi mata fam nishi ma daky'ar take. Haka dole ta janyo su Saudah suka yi d'aki. Suna shiga ta fad'a kan gado ta kwanta kan k'oshin da tayi.

Aunty Fareedah tace "k'anwata ga alama Khaleed ya wahalar min da ke ko? gashin da yayi inaga bai yi ba, sai mun sake wani." suka shek'e da dariya.

KAI NE MAFARKINA {DREAM GIRL }full Story Is On Okadabooks.com Where stories live. Discover now